Chapter 7
Chapter 7
yace, “yanzu haka yana ina?”. “general hospital ”. Nuren yay hanzarin fad'ama sarkin mota “muje general hospital na garinnan”. “to ranka ya dad'e”. ‘sarkin mota yafad'a a ladabce. Hannun Galadima dake d'igar jini har yanzu Nuren ya kamo, ya kalli Galadima da alamar tambayar miya damesa? amma shi galadiman sai yamak'i kallonsa, Nuren ya girgiza kai kawai Dan yasan hakan dayayi bazai fad'aba ne, handkerchief d'insa ya Ciro ya d'aure hannun Na Galadima Dan jinin a samu ya tsaya daga zubar, dukya d'an 6ata seat d'in mortar kad'an, da yake a nan ya ajiye hannun daga gefe. ran Nuren a 6ace yace “brother dolene muyi bincike akan Surukinka, dan duk ta yanda zamu fassara a yanzu, zukatanmu bazasu d'aukaba. zamu iya zargin akwaima hannunsa a ciki, zamu iya zargin sunnemi wani Abu daga garesa yak'i basu had'in kai, zamu iya zargin abubuwa da dama”. Iska Galadima ya furzar daga bakinsa, yasaka hannu ya tura hularsa baya, kansa ya jingina da kujerar tareda lumshe idanu. zuciyarsa tana tunani yaushene zai kawo k'arshen mak'iyan mahaifinsa? Sai yaushene za'ayi walk'iya yagansu? yana buk'atar sanin dalilinsu Na za6ar maida masa mahaifi haka, miyayi musu?. Wannan tambayoyin yakema kansa kullu yaumin ta kowacce rana. Hannunsa Nuren yakamo yad'an matsa, Galadima yabud'e idonsa dasuka fara komawa kalar jaa. “brother a wannan karon bana buk'atar 6acin ranka, dan duk sanda ranka ya6aci baka iya Controlling d'in fushinka, fushinka Na saka aikinmu tafiyar wahainiya, lokaci yayi dazaka saba da irin wad'annan abubuwan fa, karinga saka nutsuwa a zuciyarka aduk lokacin da irin haka tafaru, kamarfa yanda takawa (papi) yake fad'a mana ne a kullum, sufa sunayin wad'annan abubuwanne dan kawai su fusata ka, a haukansu zasu iya samun nasara a kankan saboda ciwon da ALLAH ya jarabceka dashi, waynote kaikuma ka karya wannan kwarin guywar tasu OK?”. Ajiyar zuciya Galadima ya sauke, shima ya dafa hannun Nuren d'in yana lumshe idanu, a hankali yace “Okey it's better”. Daga nan motar ta d'auki shiru, ahaka suka isa asibitin. Zuwa lokacin jama'ar gidanmu sun kuma cika asibitin, harsu Munubiya duk sunzo suma. Tunda motocin Galadima uku suka shigo asibitin kallo ya koma Kansu, kowa son ganin mai fitowa yakeyi. Dogaraine suka fara fitowa, kafin abud'ema su Galadima. 'Yan gidanmu sun fahimci daga masarautane, amma babu Wanda yay tunanin ganin Galadima d'in. Tunda yafito kwarjininsa da cikar haibarsa ta kasancewarsa jinin sarauta ta cika idanun jama'ar wajen, dogarensa sun tsare ko ina babu mai damar ra6arsa, Nuren na gefen hannun damarsa. Wayyo, nanfa ido yaymasa caa, baya son kallo ko kad'an, amma yaya zaiyi, tunda jama'a sunga abin kallon.🤦🏻♀ Tunkan ya k'araso su yaa Hameed suka mik'e suka nufoshi. Munubiya kam bayansa kawai take lek'awa, azatonta harda 'Yar uwarta. amma ganin babu alamar mace ma acikinsu sai jikinta yay sanyi. Hannu Galadima ya d'agama dogaransa alamar su dakata, baya suka ja, yayinda shikuma yamik'ama yaa Shafi'u daya fara k'arasowa hannu, sun gaisa da yayuna cikin girmama juna, kafin sumasa jagora zuwa ciki inda Abba yake. Dayake su Munubiya suna daga gefene, shiyyasa basu gaisa da Galadima ba, sai k'amshin turarensa daya cika hancinansu. Dukda halin da ake ciki, saida 'yan gidanmu sukaji Hassada, kowa jitake inama mijin 'yartane🤕🥴. Humm doctor daya hana kowa ganin Abba saigashi jikinsa Na rawa ya tarbi Galadima, daddy da baba k'arami sunje gida suyo wanka, bayan dawowar su yaa Naseer sai sukuma suka tafi. Doctor yama Galadima jagora har d'akin da Abba yake kwance. “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un” kawa Galadima ke iya fad'a a la66ansa, maganar gaskiya jikin Abba babu k'yawun gani, yaa Shafi'u ma mai ragguwar zuciya kasa daurewa yayi yafice da sauri yana hawaye, yaa Hameed kam runshe ido yayi zuciyarsa Na suya kamar zata fad'o k'asa. Galadima ya dafe bango tareda rik'e kansa dayaji ya sara masa, halin da Abba yake ciki exactly dana Alhaji Abdus'salam Abba. Da sauri Nuren yaruk'o hannunsa, a hankali yake fad'in “Control yourself please”. Doctor yajawo kujera biyu yabama Galadima da Nuren dansu zauna. Ina kasa zaman sukayi, dole suka fito. Galadima yabuk'aci ganin doctor d'in. 'Yan gidanmu kuwa fitowar yaa Shafi'u yana share hawaye yasaka zukatansu kuma tashi, caa sukayo kansa da tambayar lafiya. Kasa magana yayi, ahaka su Dady suka samesu, sukansu jiki a sanyaye suka k'araso wajen, kardai ace d'an uwansu yatafi ya barsune. muryoyinsu har rawa sukeyi wajen tambayar lafiya?. Sai alokacin yaa shafi'u yasamu bakin maganar cemusu bafa rasuwa yayiba, jikinnasane sai babu dad'in kallo. Baba k'arami yace, “sun bari kun gansane?”. “Eh baba, Galadima ne mijin Munaya yazo”. Dady da baba k'arami ciki suka shiga, sukabar 'yan gidanmu dake kuka abin gwanin tausayi. Doctor bai 6oyema Galadima komaiba, yafad'a masa gaskiya jikin Abban yayi tsanani, dan yaji raunuka Na tashin hankali, ga karaya a jikinsa takai hud'u. Galadima ya cije lips d'insa, kafin yace, “ina police d'in dasuka kawoshi nan?”. “ai wlhy yalla6ai basu kwana ba, tun jiya around 11pm suka tafi abinsu, kuma har yau basu dawoba”. Amatuk'ar fusace Galadima yace “Why!!?”. Doctor yagama rikicewa, jiki Na rawa yace “ban saniba wlhy ranka ya dad'e”. Harara Galadima ya watsa masa, yace “saboda kaima bakasan aikinka ba? wai......”. Nuren yay sarin fad'i “Cool down Sameer!”. “haba Nuren, kajifa wani zancen banza, saboda jami'an tsaron k'asarnan basu san aikinsuba, su kawo mutum cikin irin wannan mawuyacin halin amma bazasu dakata suji wani issues akansaba su tafi, bazama su iya zama zuwa washe gariba ko za'a iya buk'atarsu”. “sorry ranka ya dad'e”. ‘cewar doctor a tsorace’. Dady da baba k'arami dake tsaye abakin k'ofa tun d'azun suka k'arasa shigowa, sune suka kwantarma Galadima hankali da nuna masa yayi hak'uri. A girmame ya risina ya gaidasu da tambayar mai jiki. Suka amsa masa da Alhmdllh. Cikin mintuna 30 Galadima yasa aka canjama Abba d'aki Na musamman, sannan aka kawo police 5 suka zagaye d'akin. Hakan yama familyna dad'i sosai, dansu baba k'arami tun a daren jiya sukaga wasu sunata zagaye-zagaye a k'ofar d'akin da Abban ke kwance, ba k'aramin tsoro abin yabasuba, amma basuda mai taimakonsu, sai addu'a dasukai tayi da Neman tsarin ALLAH akan mutanen. Amma gashi yanzu ALLAH ya kawo musu Galadima. Galadima yasaka doctor yayi shirye-shirye daduk tattara bayanan Abba. Da k'yar Nuren ya lalla6a Galadima ya amince aka masa treatment d'in hannunsa shima, sai da Dady yasa baki ma, amma da ya dage akan abarsa shifa baya masa ciwo, saigashi hardasu d'inki akayi masa a wajen. Daga nan suka fito daga office d'in doctor d'in, sunason zuwa inda Accident d'in yafarune. Harsun kusa fita Galadima yatuna, ya buk'aci abashi wayar Abba idan babu damuwa. Baba k'arami yace, “ai bama azo da wayarsa asibitin ba gaskiya, maybe ma tana can inda abun yafarune”. Galadima ya jinjina kai kawai suka tafi. Su innarmu sunji dad'in abinda Galadima yayi, innaro sai kwararo masa addu'oi takeyi tana kuka. ____(((★)))____ Zuwa yanzu hankalina yakai k'ololuwar tashi, saboda mafarkin Abba na danayi da daddare, abin mamaki a barcin safema dana koma hakance ta faru, nakuma mafarkin Abba yana cikin mawuyacin hali, a firgice na farka jikina sharkaf da zufa, wayata na lalubo nashiga neman wayar Abbana, amma Switch up, nakira Innarmu network yahanata wucewa, hakama Munubiya, hankalina fa ya tashi, haka naitabin Number's d'in 'yan gidanmu ina kira. Amma daga Wanda zaik'i amsamin sai wadda zan kira switch up,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92