Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Murmushin takaici yayi, ya kalleni ido cikin ido, kasa jurewa nayi nai k'asa da nawa. shima lumshe nasa yayi yana fad'in “zaki gani”. daga haka ya janye laptop d'in gefe ya zame ya kwanta. Binsa nayi da kallo tamkar wata sokuwa, gaba d'aya ya kulle magudanar tunanina da wadda ke kaima kwakwalwata sakonni. Medical glasses d'in idonsa ya cire ya ajiye, sai kuma ya juyo gareni, hannunsa d'aya ya mik'amin yanamin alamar nazo gareshi. Idanu na d'an zaro, sai kuma na nok'e kafad'a alamar nak'i din. Wani murmushin da bako yaushe yakeyinsaba ya sakarmin, ya juyamin baya yay kwanciyarsa. bai sake juyowa gareniba har kusan 6minutes. nagaji da kallonsa da nazarin murmushinsa da tambayoyinsa na janye idanuna, waishi guy d'innan mike damunsa ne? gaba d'aya ya canjamin daga saukarmu zuwa yanzun, dubana nakai ga agogon d'akin. 3:27am, “ya salam” na fad'a a hankali, muna Neman kwana a zaune. can k'arshen gadon na koma na kwanta, zuciyata cike da tsoron ALLAH yasa bawani Abu ya shiryaminba, babu dad'ewa barci 6arawo ya saceni. Numfashina dake sauka a hankali yasaka Galadima gane nayi barci, juyowa yay yana kallona, yayinda zuciyarsa keta cud'a amsoshin dana basa yanzun, tabbas mahaifin yarinyarnan akwai abinda yasani, kwarai da gaske zaiyi amfani da ita wajen gano ko wanene mahaifinta?, minene alak'arsa da case d'ina?, sannan minene alak'ar Muftahu da ita?, Dan tabbas akwai manufar sako yarinyar acikin wannan tak'addamar, kuma Muftahu dashi aka shirya komai. yasaki wani murmushin mugunta tareda nuna kansa, a fili yace _MAK'IYAN MAHAIFINA SAINA ZAME MUKU_ *RAINA KAMA KAGA GAYYA* tabbas lokaci yayi dazakuga wannan *Gayyar*. Tofa masu karatu, ana zaton wuta a mak'era🤔, mikuna yasako Abban munaya a rikicin masarauta? Kodai ba masarautar kawai bace keda alhakin ciwon tsohon Sarki Saifudden Abubakar🤔?, shin tsakanin Galadima da Munaya & munubiya, innarsu Munaya. Wanene RAINA KAMA...... d'in🤗?. Kumuje zuwa kudai my Guy's😁, duk nisan jifa👆🏻, k'asa zai fad'o👇🏻🤗 ★___________________________★ Bayan shigewar su Galadima Muftahu ya fito daga mota shima yana murmushin dashi kad'aine yasan fassararsa, jiyay kawai handkerchief ya rufe masa fuska, yay saurin cirewa yana waige-waige dan dunba wanene ya jeho masa, wayam babu alamar mutum a wajen, bai gama dube-duben ba yay luuu zai fad'i, saigashi a hannun mutum, idanunsa sunriga sunyi nauyi, dishi-dishi yake kallon Wanda ya tareshi d'in, dama gashi ya rufe rabin fuskarsa ba'a gani, wasu samarine su biyu sukazo suka kama Muftahu tareda wancan suka danna a mota, tun yanajinsu sama-sama har idonsa da jinsa suka rufe baki d'aya. 🙆🏻tofa suwaye?. ★__________★_________★ Tun kusan around 8pm Nuren yake k'ofar wajen, a dukkan bayanan daya samu daga majiya mai k'arfi yarinyar Minister ta shigo gari yau, kuma zatazo shan ice-cream wajen, wayarsa ya d'auka yay wasu 'yan danne-danne, murmushi yayi ya maida wayar ya ajiye tareda dasama k'ofar wajen idanu, dolene kafin tashiga ciki zai saceta, dan bincikrnsa ya nuna masa cctv camera d'aya ce a cikin wajen kawai, a waje babu, dan haka bama ya buk'atar ta Shiga, murmushi yayi saboda ganin motar da driver d'inta yamasa kwatancen zasuzo aciki, saida driver n yaga motar Nuren sannan yazo kusada ita yay parking, bud'e murfin gefen mai zaman banza Nuren yayi, hakan kuma yay dai-dai da fitowar zankad'ed'iyar budurwa daga motar datai parking kusada ta Nuren d'in, murfin ne ya daki gefen hannunta kad'an. A fusace ta kalli motar Nuren, shikuma yay mata murmushi, wani haushine ya kamata, banda rainin wayo ya bigeta amma yamata murmushi saboda wulak'anci, yau saitaga wanene ubansa a garinnan?. da k'arfi tabuga saman motar tana lek'a kanta ciki, “kai wawa bakaga abinda kayi bane?”. Maimakon ya bata amsa saiya jefa mata handkerchief d'insa saman fuskarta, janyewa tayi da sauri zatayi magana kanta ya sara mata, da lalube ta dafa kujerar motar ta shiga ta zauna, sai faman lumshe idanu takeyi. murmushi Nuren yayi, ya taimaka mata ta ida shigowa Sannan ya rufe motar, komai akan idon driver n ta ya faru, bashida damar hanawa, dan Nuren yasashi a tsaka mai wuyane. Agaban idonsa Nuren yaja motarsa yabar wajen yana murmushin samun nasarar tafiyar plan d'insa yanda ya tsara. a wannan daren yanufi gidan Galadima dake can bayan gari inda aka ta6a kai Munaya. 😱humm yau 'yar kidnapping akeyi kawai😂🤪. ------------(((★)))-------------- Galadima yariga Munaya farkawa, dama bawani isashshen barci yayiba, tunani da damuwa suka taru suka hana idonsa rintsawa sai gabannin Asuba. Ana kiran sallar farko kuma yana farkawa, tashi yay zaune dafe da kansa, kusan mintuna biyu ya juya yana kallon munaya data juyo tana fuskantar inda yake yanzun, da gani kasan barcin bamai dad'i takeyiba, dan sai yamutse fuska takeyi a cikin barci. matsawa yayi kad'an ya d'ora yatsunsa biyu gefen fuskarta, sai yaji zafi jikinta, ya janye yana mamakin wai mike damun yarinyar nan kwana biyu haka? dolene yau yasata taga doctor idan sunje ganin Abba. gabansa yad'an fad'i daya tuna har yanzu itafa batasan komai ba, shi baima San ta yadda zai sanar mata abbanta yana cikin mawuyacin hali ba, ya dafe kansa yana ambatar sunayen ALLAH kozaiji sassauci a ransa. Da k'yar ya samu ya mik'e domin yin rakata ainul'fijir kafin akira assalatu. Bayan ya idar ya tadani, da k'yar na iya tashi dafe da kai, dan barcin bai isheniba, muryarsa da alamun shima rashin isashshen barcin yace, “time d'in salla yayi”. Idona dake bud'ewa da lumshewa Na kad'a masa alamar amsawa, yay saurin janye nasa saboda wata fad'uwar gaba da tsirgawar wani Abu dayaji lokaci guda tun daga Kansa zuwa yatsan k'afarsa, bai sake magana ba yafice. nikuma nakoma Na sake kwanciyata. 'Dakinsa ya shiga ya tada Sauban dansu tafi massalaci. Babu dad'ewa Sauban ya kammala alwala yafito ya iskeshi a falo yana jiransa, harara ya antayama Sauban, shikuma ya kauda kai gefe yana had'iye dariya (yo daga taimako saiya zama laifi?). Sarki yayi mamakin ganin Sauban, dan yaron bawani zuwa k'asar yakeba saida dalili mai k'arfi, bayan yagama k'ar6ar gaisuwa wajen jama'arsa Galadima da Sauban sukabishi zuwa sashensa. Kasa 6oye mamakinsa yayi, ya kamo hannun Sauban d'in dake d'ayan 6arinsa zaune kamar yanda Galadima yake, “yarona ne yau ak'asarsa ba biki ba ba bikin salla ba?”. Dariya Sauban yayi, yace “Abba nazo gaidakune kawai”. Sarki ya Murmusa yana kallon Galadima, “Galadima kodai akwai abinda ke faruwane kuke 6oyemin?”. Galadima ya d'ago kansa cikin damuwa yace “babu abinda muke 6oyewa ranka ya dad'e. Mahaifin Munaaya ne yay Accident shine suka taho da Sauban d'in”. “mu bamuda muhimmancin da zamu Sani kenan ko?”. “ALLAH ya huci zuciyarka ba haka nake nufiba, bayan barina wajenka jiya nima aka sanarmin, lokacin dana shigo kuma dare yayi”. Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke, yace “ALLAH yabashi lafiya, zuwa anjima sai su waziri suje dubashi ai, tana ina ne ita d'iyar tawa?”. “tana nan cikin masarauta”. Jin jina kai kawai Sarki yay bai kuma cewa komaiba, sai zuwa can yacigaba dayima Sauban tanbaya akan jikin Abie, shikuma yana bashi amsa. Galadima dai Na jinsu bai saka bakiba. ************* Saida gari yafara haske ALLAH yabani ikon tashi, dan zazza6in kuma ya sauka, yanzu kuma haka yakemin, da dare yayi zan fara zazza6i, lokacin da gari zai waye saikiji ya sauka. Sai dai ciwon jiki. Saida nayi wanka da ruwa mai zafi sannan nayo alwala, sallar asubahi data kwacemin nayi, Na jawo handbag d'ina danazo da ita

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});