Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya juya kwanciyar sa yana murmushi, zuciyarsa tace “to matar contract fa?”. ya d'age kafad'a da ta6e bakinsa kad'an, saikuma yasaki k'aramar dariya, daren jiyane kawai ya fad'o masa a rai, yau kuma koyaya ta yini ta kwana? (danba time d'inmu d'aya da India ba), a fili yace, “ALLAH yasa yau dai babu zazza6in, my Friend kin cika taurin kai, dakin yarda nakaiki asibiti zanfi samun nutsuwa, oh god🤦🏼‍♂”. ‘ya k'are maganar da dafe kai’. Shima yajima baiyi barciba, sai can dare yaja da nisa sannan ya saceshi. Da asubahi da k'yar ya iya tashi, alwala yay yafita massalaci, bayan an idar da salla yafito suka had'u da Sarki da jama'a keta zubewa suna kwasar gaisuwa. Sarki yayi mamakin ganinsa, dan har saida fuskarsa ta nuna hakan, murmushi kawai Galadima yayi yana rissinar da kansa k'asa. Sarki baice masa komaiba yanufi sashensa, sai Galadima yabi bayansa, dogarai kuma suka take musu baya, bayan sun gaida Galadima d'in. A hamshak'in falon mai martaba na farko suka yada zango, Sarki na zaune bisa kujera mai zaman mutum biyu, Galadima na k'asa kusada k'afafunsa. Kukun Sarki ne suka shigo shida jakadiyya bayan sunyi sallama.. K'aramin tire suka ajiye dake d'auke da butar shayi, sai mug da wani k'aramin bowl mai k'yau anzuba sukari, sai jug k'arami shima an zuba tataccen lemon tsami, saikuma Zuma shima a k'aramin bowl. Kuku da jakadiyya suka zube gaban mai martaba suna kwasar gaisuwa, sannan suka gaida Galadima shima da masa barka da zuwa. Cikeda kulawa ya masa musu, har kuku ya durk'usa zai had'ama mai martaba shayin Galadima ya dakatar dashi, tareda masa nuni dayaje abinsa. Kuku ya rissinar da kai alamar girmamawa sannan suka fice shida jakadiyya suka basu waje. Galadima ya had'ama Mai martaba shayi da ruwan lemon tsami kamar yanda yasan yana sha a kowacce Safiya, (ada mahaifinsa yasani da wannan al'adar, dan awajensa Sarki jalaludden ya koya). cikeda girmamawa ya mik'ama mai martaba mug d'in, kar6a yayi yana masa murmushi, sannan yace “kaifa?”. Girgiza kai Galadima yayi, yace “a'a Abba, wannan sai ku”. Mai martaba yay murmushinsu na manya sannan yace “Saukar yaushe Sameer?”. Galadima yad'an shafa wuyansa, cikin tsantseni yace, “da daddare Abbah, wani business ne ya kawoni, inaga insha ALLAH zamu bud'e company anan Nigeria saboda muma matasanmu su Mora daga guminmu”. Murmushi mai martaba yayi, ya kur6i shayinsa sannan yace “tunani mai k'yau yarona, ALLAH yasaka hannu a lamarin. ya jikin d'an uwana dasu auntyna Zeenah?”. “jikin Abie Alhmdllh Abba, dan bayan tahowarku sauk'i yakuma samuwa gaskiya, Momma kam suma lafiyarsu lau”. “to Masha ALLAH, tareda iyalin naka kazo kenan?”. “a'a Abba, ni kad'ai nazo, saina kammala abinda nazoyi itama idan zan dawo zamu dawo tare”. “to ALLAH ya tabbatar”. “Amin Abba, bara naje nad'an kimtsa mu gaisa da jama'a, dan zan d'an fita”. “ok, ALLAH yayi Albarka”. “amin Abba, a huta lafiya”. Hannu kawai mai martaba ya d'aga masa, Galadima kuma yafita. Babu inda ya Shiga, ya koma sashensa domin yayi shiri. saida ya had'a coffee da kansa kamar yanda ya saba idan yazo k'asar, ya zauna yasha danba abincin kowa yakeci a masarautarba, ko Ummu hasheem bayacin abincinta kota kawo, duk da kuma kulawa datake nuna masa fiye da kowa a gidan, gimbiya zulfah uwargidan sarkima tanada k'ok'arin aika masa abincin inhar yazo, amma ko kallon kulolin ma bayayi, saidai bayinsa su cinye. Yafito wanka yana tsane jikinsa wayarsa tayi k'ara alamar shigowar sak'o, wayar ya d'auka danya duba ko company ne, dan yana fatan ace komai ya daidaita ne, yanason kiran su Momma yaji Yaya jikin mahaifinsa. Ganin number ce sai abin yabashi mamaki, bud'e sak'on yayi kawai azatonsa ko Nuren ne. _Gargad'i!! tabbas sirikinka ya tsira a wanan karon, amma ka tabbatar masa next time bazamu barsaba, saimun raba ruhinsa da gangar jikinsa!!!!.................._✍🏼 *_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_* [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 ~Book 2~ 👉🏻5⃣ ..............Bayan an idar da salla Galadima yace wanne office yakamata su fara zuwa?, mtn ko glo?. Shiru Nuren yay yana tunani, zuwa can ya kalli Galadima “Sameer mizai hana mubari sai zuwa gobe, kasamu kaje kad'an kwanta ka huta, kaga yanda idonka yay jazur kuwa, ga jijiyan dukta tashi”. Lumshe idanu Galadima yayi yana furzar da huci mai zafi a bakinsa, “Nuren muje kawai, kona kwanta bazan samu nutsuwa ba, kaga fa yanda suka jigata bawan ALLAHn nan”. “hakane, amma karka damu muje kai dai kawai”. Galadima bai musaba, suka jera shida Nuren zuwa wajen mota, bayan anbud'e musu sun shiga sai Nuren yacema Sarkin mota suje hotel d'in daya sauka. Galadima yanajinsu amma baice uffanba, yayi shiru kawai yana kallon jama'a ta glass. Koda suka isa hotel d'in sai Nuren yace su sarkin mota suje abinsu, zuwa anjima zai kirasu su maida Galadima d'in gida. Cikin girmamawa sarkin mota ya amsa da to, yamusu sallama suka tafi. Koda suka isa d'akin da Nuren ya sauka Galadima cire rigar shaddar yayi ya kwanta dagashi sai dogon wandon da vest, kwanciyar mintuna 5 kacal barci yay gaba dashi. Sosai tausayinsa yakama Nuren, yanason d'an 'yar uwar mahaifinsa sosai, (Nuriddeen d'ane ga Abubakar yayan Momma, babban d'an Sarki Abdul'fatah daya gaji sunan Sarki Abubakar kakansu Galadima, mahaifin Nuren ayanzu haka shine mai jiran gado a masarautar su momma, Nuren d'ansane na biyu, akwai yayansa Ballo, shid'in sa'an Galadima ne, kusanma tare akayi goyonsu, amma Galadima ya girmesa da watanni 7 a duniya, kunga d'an uwansane na jini kenan, ta 6angaren mahaifiya👌🏻). Galadima ya jima yana barci, dan kiran sallar la'asarne ya tadashi ma, wanka yasake yi, ya kar6i kayan Nuren ya sanya, k'ananun kayane amma sun masa k'yau sosai, Nuren nata tsokanarsa, wai kayan sun masa k'yau, inhar Munaya ta gansa bazata ganeshi ba. Harara ya zubama Nuren, sannan yanemi hanyar fita, “malam idan kagama surutun saika taho muje”. “sorry sarkin gagara badau mai jiran gado”. tsaki Galadima yayi kawai yafice abinsa, shifa haushin mai jiran gado d'innan yakeji idan aka ambata masa, sadai nemi mai jiran gadonsu amma bashiba, mtsoww!!. Wata mota dake fake a harabar hotel d'in suka nufa, Nuren ya zauna a mazaunin driver, yayinda Galadima ya zauna gefensa. A hankali Nuren ke tuk'in suna 'yar hirarsu jefi-jefi, dayake kowanne akwai nutsuwa basuda yawan hayaniya, dan shima Nuren d'in bashida surutu. Tafiya mai d'an nisa ta kaisu wani k'auye, bawani babban gari baneba can. Galadima ya kalli Nuren yana hararsa, “wai Nuren bazaka saida gidannan ba dai ko?”. Murmushi Nuren yayi, yad'an gyara zamansa yana kallon Galadima, saikuma ya maida ga hanya. “brother kenan, ai yanzu ba abinda kuke tunanin nake aikatawa ba a gidan, wlhy babu ruwana da 'yar kowa yanzun”. “Humm Nuridden! nasan inhar kana tareda Muzaffar bazaka ta6a daina neman mataba, nidai bazan gaji da gaya maka gaskiya ba, inhar aure kakeso kawai kayi aure, bazaka gane llar zina ba saika auri yarinyar da wani yagama Sani, saika haifi yara kuma, Nuren! Ba cika baki nakeba, bakuma nafi k'arfin ALLAH ya jarabceniba, amma dana aikata zina ka ganni nan gamma a d'auramin aure da mata hud'u a rana d'aya, please and please d'an uwana, ka canja tun Kannada damar hakan, dukkanin ahalinmu basa son wannan d'abi'ar taka wlhy”. Nuren ya jinjina masa kai yana cije la66a,

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});