Chapter 72
Chapter 72
ya bata izinin shiga. Tun da ta shigo taga yanayin da yake sai gabanta ya dad'i, tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki ta mik'a masa ledar data zubo kayan sannan ta zauna a kunyace saboda yanayin da yake babu kaya. Ba tare da ya kalleta ba ya hau Fiddo kayan, ya zubesu saman gado yana d'aukar hotonsu a waya, yay latse-latse nawasu mintuna kafin yasaka wayar a kunne. “Saleem ka dubamin kalar kayannan, koda basu kaisu tsadaba, yanzunan kataho ka kawominsu”. Bataji mi Saleem yafad'a daga canba. Muryarta a raunane tace, “yalla6ai mike faruwa wai?”. Jajayen idanunsa ya d'ago ya kalleta, k'ala baice mataba ya mik'e ya d'akko wani k'aramin box ya dawo ya zauna, ita duk saima kunya takuma kamata, saboda dagashi sai boxer, amma taga ko a kwalar rigarsa bai damuba, hidimar gabansa kawai yakeyi. Kwantar da Amaturrahman tayi kusa dashi ta tashi zuwa wardrobe d'insa, k'aramar t-shirt ta d'akko, tazo ta mik'a masa. Ya d'ago ido yana zuba mata harara, dukda ta tsorata saita daure tace, “please mana yalla6ai”. tayi maganar muryarta a raunane. Saida yayi k'aramin tsaki kafin ya amsa ya saka, wani abu da batasan minene ba taga yana mak'alawa jikin kayan yaran, saida yagama tsaf sannan ya maidasu a ledar, kallon Amaturrahman dake k'yalla y'an idanu zata fara k'aramin kuka yayi, ya shafa kumatunta batare da ya d'auketa ba. Laptop d'in sa ya jawo ya saka eye glasses d'insa, ya kalli Munaya yamata alama da ido akan tazo. Babu musu ta taso zuwa kusa dashi ta zauna. Laptop d'in ya d'ora mata akan cinya yace, “wanene SD a cikin su?”. Nutsuwa Munaya tayi tana kallon hotunan, cikin waro ido tace, “kai ga Fu'ad ai”. Da mamaki Galadima yace, “Fu'ad!?”. “eh wlhy yalla6ai, Wanda ya kaimu birnin gayu plaza ranar da abunnan ya faru”. Kar6a laptop d'in Galadima yayi yakuma kallon hoton da k'yau yana taunar lips, kuma mik'a mata yayi batare da yace komaiba. itama batace dashiba tacigaba da bin hotunan da kallo sannu a hankali. Harta kai k'arshensu babu SD. ta kalleshi cikin damuwa, “yalla6ai babushi fa anan gaskiya”. Kansa ya jinjina mata yana kar6ar laptop d'in, cigaba yay da danne danne, itadai Munaya tana kallonsa. Kuma d'agowa yay ya kalli Munaya, “duba annan kuma fa”. Kallon hotunan ta shigayi, canko saiga hoton SD, tace, “Alhmdllh gashi anan”. Kallon hoton Galadima yayi, da mamaki yace, “kinsan wanene wannan kuwa?”. “Ah! yalla6ai SD ne mana”. “Munaya kin tabbata wannan ne kika gani a wajen Abba?”. “Wlhy shine yalla6ai, bazan ta6a manta fuskarsa ba ai komai dad'ewa. balle acikin abinda bai rufa 2years ba, amma kasanshi ne?”. Bai iya cemata komaiba, sai zuciyarsa dake wani irin bugawa da sauri-sauri kamar zata fad'o, mamaki ya hanashi motsin kirkirma, Alhaji Shehu Darma shine SD kenan, babban Amini kuma d'an uwa ga Mahaifin su Samha, innalillahi, ya abubuwa keneman koma masa rikid'ar hawainiya haka?, wannan fa Fu'ad d'in d'ane ga yayar Uwargidan Sarki mahaifiyarsu Matawalle, cikin cije lips ya buga hannunsa akan gadon yana fad'in “Kai!!!! miyasa hakane? miyasa duk Wanda Na yarda dashi shike fara bayyana a maicin dunduniyata?!! miyasa rayuwa tazomin da irin wannan rikicin ne?, oh God!!”. ‘ya k'are maganar cikin matsanancin k'araji, tareda runtse hannayensa waje d'aya. Tsoro ya kama Munaya, ganin yanda duk ya rikice kamanninsa suka canja, idonsa yayi matuk'a jajur, jijiyoyinsa da gashin jikinsa duk sun mimmmik'e, ga Amaturrahman data tsorata lokacin daya buga gadon, d'aukarta tayi tahau jijjigawa. Sauban ma a firgice ya tashi, ya hau waige-waige, ganin babu kowa a falon saiya nufo hanyar bedroom d'in Galadima, tabbas muryarsa yaji a yanayin da ba'aso. harzai murd'a k'ofar saiya fasa saboda jin kamar muryar Munaya tana magana. Tunda tasamu Amaturrahman tayi shiru sai ta d'auki towel d'insa ta goyata, ta matsa kusadashi a tsorace, hannunta ta d'ora akan nasa daya dafe mirror, ko motsi baiyiba balle ya kalleta. Murya a d'arare kuma a sanyaye tace, “please yalla6ai, fushi baisa a samu sauk'i saidai ya k'ara zafi, kaine kasha gayamin wani karatun baya buk'atar fassara ko dogon nazari, akan barsane kawai a yanda yazo, dukda bansan tushen matsalarba zan iya bada gudunmawa wajen kama bakin zarenta, kayi hak'uri ka kwantar da hankalinka, ita fahimta fuskace, ba fushinka ko tsantsar damuwa ne abin buk'atarba yanzu, d'ana tarkon dazai fara kamo maka hannun mak'iya shine jarumta, ka danne kuma ka daure, ni dama Dan banida ikon hana walimar nanne kawai, amma inaji a jikina akwai lauje cikin nad'i, saidai wad'anda suka nad'a d'inne bamuda ilimin saninsu sai ALLAH yaso Samar damu, amma ai duniya makarantace, idan su a can suka yini kaikuma saika nuna musu kwana kayi, lokuta da dama fushinka ke lalata maka aiki, dan inhar kana cikin fushi dukkan aikinka tafiyar hawainiya yake, wannan lagon naka suka samu suke wasa da hankalinka, koda ace wani ya salwanta cikin yarannan karka d'aga hankalinka, ALLAH n daya baka yafika sanin hikimar k'addara hakan, duk lokacinda kaga Matsaloli sun raunana, buk'atu kan kuma kan yalwata ne, kasa a ranka wannan wata damace tazo gareka, ai duk lokacin da aka rasa kwallo a cikin wasa, ba wasan ake dainawa ba, wata kwallon ake jehowa a cikin fili”. Duk maganar da takeyi ko motsawa baiyiba, baikuma juyo ya kalleta ba, saidai alamu sun nuna yana saurarenta, ta janye hannunta ta juya zata fita tana hawaye. Cak ta tsaya saboda rik'o hannunta da yayi, kusan minti 1 suna a haka, ta waigo ta kallesa, har yanzu yana a yanda yake, kallon hannunsa daya ruk'o nata tayi. Bai kalletan ba kuma bai saki hannunba yace, “Lallai ina shaidama dukkan Wanda ya maida rayuwata data ahalina magijin kallonsa, zan tsiyayar masa da idanun, sannan zan kacaccala rayuwarsa Na binnesa da ransa”. ya mik'e tsaye sosai tareda juyowa ya jawo hannunta ta fad'o jikinsa, saurin dafe Amaturrahman dake bayanta tayi da d'ayan hannun. Ya saka idonsa dasuka firgitata cikin nata, fuskarsa dab da tata yace, “kedai kibama yaranki kariya kawai, dan sune fitilar zuciyar mijinki”.. sakin hannunta yay ya zagayeta yabar wajen. Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo, yayinda zuciyarta keta kuma maimaita maganar tasa, _yaranta, kuma mijinta?_ mi yake nufi to?, amsar itace bata saniba. Jitai kawai ya saka mata ledar kayansu Abdurraheem a cikin hannu, baice k'alaba yabar wajen zuwa gaban wardrobe d'insa yafara fiddo had'add'iyar Shadda gizna ash colour, sai maik'o take da d'aukar idonu. Ganin ya shareta yana cigaba da hidimarsa itama saita juya ta fice. Tunda Sauban yaji motsin kama handle d'in k'ofar yabar wajen da sauri. Fitarta babu dad'ewa Saleem ya kawo kayanda Galadima ya umarcesa. __________________________ Munaya Na komawa Aunty Salamah tahau shiryata, dukda taga a yanayin data dawo bata tambayeta daliliba, saida tagama gyara mata fuska tana gyara mata gashi Munaya tafara fad'a mata iya abinda taga ya dace kawai Aunty Salamahr ta iya Sani, sauran kuma sirrinta ne ita da mijinta. Murmushi Aunty Salamah tayi, tace, “dukda banida tabbacin faruwar wani Abu dagani har Munubiya dama mun shirya hanyoyin d'aukar matakai saboda tsaro, kowa baisan dalilin Munubiya na dagewa akan ki dawo gida ki haihuba, amma ita tasan dalilinta, ba son zuciya ya sakata yin hakanba, Ubangiji Na kallon kowa kuma zaiyi maganin komai, tun a shekaran jiya Saleem yazo mungama tsara komai dama, kuma ya tabbatar min
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92