Chapter 40
Chapter 40
ya lullu6a mata, harya mik'e ya koma ya zauna, risinowa yay kanta a hankali ya mannama goshinta kiss, sannan yamik'e ya fice. Koda ya dawo saiya wuce d'akinsa, yabar su Aiyaan suna kallonsu. Kayan jikinsa ya cire ya kwanta shima, dan yana buk'atar hutawa kona 2hours ne, kwanciyarsa kuwa babu dad'ewa barci ya saceshi. Kiran sallar la'asarne ya tashesu kusan lokaci d'aya, Galadima yatashi da k'yar, a mamakinsa sai yaga Aiyaan da Aryaan kwance a gefensa suma suna barci, murmushi kawai yayi yasako, saida ya watsa ruwa sannan yay shirin tafiya massalaci cikin k'ananun kaya. Harzai fita saiya dawo yashiga wajen Munaya. tana tsaye gaban wardrobe tana neman kaya, da alama wanka tayi, dan daga ita sai towel. Banji sallamarsa ba, saboda shi idan zaiyi magana bayason bud'e baki, ganin batajishiba saiyayi gyaran murya, a tsorace na waigoshi, ganin shine nai saurin saka kayan dana d'akko ina kare k'irjinna da tura baki, bakinsa ya d'an ta6e, sai kuma ya shiga takowa inda nake, duk takun da yayi sai gabanna ya fad'i, na waiga kozan samu nabar wajen ko abinda zan suturta jikinta sosai, amma sainaga babu a kusa, kuma ina jikin wardrobe d'inne sosai ai. ban gama yanke shawara ba ya k'araso daf da ni, kuma matsawa nayi na matse jikinna sosai a drowa d'in, shikuma yawani had'e gabas da yamma, wannan ne yakuma sakamin tsoronsa a raina, na zata kowata tsiyarce ta kawoshi. Hannu yasaka ya d'ago da ha6arta muka kalli juna, ya tsareni da idanu yanda nakasa janye nawa cikin nashin, munkai kusan 2minutes a haka, kafin yakumamatsoni sosai, ya kai fuskarsa gab da tawa tamkar zai had'e bakinmu, dan haka saina lumshe idanu, murmushi yayi ya hura mata iska akan idanun, ta rumtse idon sosai, ya d'an ja baya yana ta6e baki, kafin yasaka hannu ya cire nata dataketa faman kare k'irji da kayanta, still ya kuma matsawar saitin kunnenta yana fad'in “wane darene jemage bai ganiba yalla6iya”. ‘ya k'are maganar da shafa kirjina ya fice abinsa. Kad'an yarage namasa ihu wlhy, aiko yana fita na durk'ushe a wajen ina sauke numfashi, sometimes nakan rasa yazan fassara Galadima da ayyukansa. Da k'yar Na iya tashi nayi sallar nakoma kan gado Na kwanta. Galadima kam daya fita dariya ce taita cinsa, ya kula Munaya akwai tsoro, kuma haryanzu a tsorace take dashi, cikinnan ne kawai kanci galaba akanta yake samunta cikin sauk'i, ya girgiza kansa kawai yana murmushi. Bayan ya dawo massalaci d'akin nata ya dawo, dan yanason suje su gaida jama'ar gidan, maybe gobe suje masarautar papi ma. A kwance ya iskeni, nak'i kallonsa, jingina yay da mirror yana fad'in “yaya jikin naki?”. Ban kalleshinba nace, “da sauk'i”. “ALLAH ya k'ara sauki, idan zaki iya tashi ki shirya muje cikin gida, kafin waccan tsohuwar tafarama mutane surutu”. “to” nafad'a ina mik'ewa, Na sakko a gadon, harna nufi wardrobe zan d'auki alk'yabba saina tsaya, batareda Na kalleshi ba nace, “toka fita Na shirya”. Hard'e hannayensa yayi a k'irji yana fad'in “ashe bazaki shirya d'inba, dan bazanje ko inaba”. “karkaje d'in, ai akwai bayi” nayi maganar a zuciyata. Kayan Na d'auka na shiga toilet, shikuma ya ta6e baki. Babu dad'ewa na fito tsaf, nayi k'yau, nazo ta gefensa na d'auki turare nasaka kad'an sannan na kallesa nace, “na shirya”. Baice komaiba ya nunamin hanya, gaba nayi yana bina a baya muka fice. Kasancewar tazarar dake d'an tsakaninmu da sassan nasu muka shiga mota, dan banajin dad'in jikinna, bama zan iya tafiyarba. 6angaren Abba hayatudden muka fara zuwa, daga nan sai sashen matan mai martaba, soyayyar da uwargidansa ke nunamin yasani k'ara k'aunarta, sai addu'a take zabgamin akan ALLAH ya saukeni lafiya. Galadima kad'ai ke amsawa, amma ni saidai a zuciya kawai. daga nan muka d'an shishshiga wasu sassa, 6angaren mama fulani shine k'arshen zuwanmu. Kunsan dai mutuniyar taku akan mulki, tana kishingid'e kuyanginta nata bauta, mai matsa kafa daban mai firfita daban, ga masu bata labarai, tufa takeci cikeda k'asaita da izza. Amintacciyar baiwarta data mana iso tana gaba muna biye, mama Fulani ta d'agama kuyanginta hannu alamar subata waje. Rige-rigen ficewa suka, yayinda mukuma muka k'arasa gareta, idonta a kammu ko k'yaftawa batayi, nidai tsarin ALLAH na nema daga sharrinta, ina dalili wannan kallon k'urilla haka?. Galadima yace, “barka da yammaci”. nima saurin fad'a nayi. A yatsine ta amsa mana, ta d'ora da fad'in “Saraki kayi wuyar gani?”. Galadima ya murmusa yana kallona, “Ranki ya dad'e kinsan mai amarya ai yafi dubu wahalar gani dama”. “Humm” kawai tace batareda ta amsaba. Sai zuwa can tace “nafa manta, ina tayaku murnar samun k'aruwa”. “mun gode ranki ya dad'e, amma taki murnar itace tazo a latti, gashi kuma idonkine yafara hango abin cikin kwan tun a india”. Mama Fulani ta tsatstsare Galadima da idanu, shikuma yay salute nata yana murmushi. Jitai kamar zata makesa dan haushi. Ya lura da haushin da taji, dan haka ya kama hannuna muka mik'e tsaye yana fad'in, “bara mukoma inda muka fito ranki ya dad'e, a huta lafiya”. Bai jira amsartaba mukayi fitowarmu. Da kallo kawai ta bimu, takasa koda motsawa, tarasa miyyasa yau Galadima da matarsa suka mata wani mugun kwarjini? batada mai bata amsar tambayar tata... Yini guda yau Galadima a gida yayishi, baije ko inaba, sai da daddare Nuren yazo sukayi magana, daga nan yace ya nema mana tickets d'in zuwa masarautarsu. Washe gari muka tashi da shirin tafiya masarautar su papi, mukad'ai muka tafi, babu kuyangi babu dogarai, dagani sai shi dasu Aiyaan, sai Nuren..................✍🏼 *_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*😭🙏🏻 [7/3, 9:59 AM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS. ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻1⃣5⃣ ...................Abin yabani mamaki ganin yanda akazo tarbarmu, yo saikace wani Sarki, hakan yakuma tabbatarmin da Galadima d'an gatane a wannan masarautar. A masarautar ma gungun mutane muka iske wai masu tarbarmu, ni dukma sai kunya ta kamani wlhy, musamman da Mom ta rungumeni tana fad'in “ga maman twins d'inmu ga Maman twins d'inmu”. Galadima dai murmushi yayi, Nuren kam dariya ya kemin. Lallai naga tsantsar soyayya a wannan masarauta, sai nan nan ake dani kamar wata sarauniya, duk wani Motsina Inno tace minakeso? hakama mom. Aiyaan da Aryaan kam ai suna tare da Galadima, duk inda yasaka k'afa suna biye. Nikam dai a kwana biyun da mukayi babu abinda zance da wad'annan bayin ALLAH sai godiya, naga karamci naga hallaci sosai, hakama k'annena. Sosai Galadima yasamu tattaunawa da papi a tsakaninnan, sunyi maganganu masu muhimmancin gaske. Musamman akan ciwon Abie da cikin jikin Munaya, harma da Abbanta. sosai kuma Galadima yakuma samun haske akan lamuran. Kwannamu biyu muka dawo cikeda kewarsu, tare da tarin alkairi ga wad'annan mutane masu tsayawa a rai. Mun dawo da kwana 1 yaran gidanmu na ma'auri suka kawomin ziyara. Aunty khaleesa, aunty Hauwa'u, aunty Ramlah, aunty Raheenat, matansu ya hameed, Fiddausi, Siyama, Zarah, Safara'u, Fauziyya, Haleematu,Munubiya, Ayusher, Feena. Wayyo dad'i wlhy saika d'auka biki akeyi, rasa inda zansaka kaina nayi saboda dad'i, shi kansa Galadima ya fahimci ina tare da tsantsar farinciki, nima dagewa nayi namusu hidima iya hidima, dan hardani aka shiga kitchen. Sukam duksun rikice da mamaki, dama haka gidan sarautar yake, dan saidama Galadima yaje da kansa ya shigo dasu. Su Aiyaan anata murna anga 'yan gida. Ranar dai anan suka yini zir, dazasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92