Chapter 19
Chapter 19
cikin cije lips da lumshe idanu ya d'ora hannunsa bisa sumar kanta da d'ankwalinta ya zame ta fito, saikuma yasaka d'ayan hannunsa ya shafi kumatunta, a kan la66ansa ya furta “sorry my friend, ALLAH yana tare da masu hak'uri kinji”. Daga haka bai sake cewa komaiba, ya janye hannunsa daga kanta ya mik'e ya fito. A k'ofar d'akin ya iske Doctor Farida tsaye, kallonta yayi cikin maganarnar tasa mai kama da an masa tilas yace “zata iya kaiwa wane lokaci bata farkaba?”. “Ranka ya dad'e inaga daganan zuwa kamar awa d'aya”. Kansa ya jinjina mata, bai sake magana ba yanufi d'akin da Abba ke kwance. ya Tatar da doctor d'in dake kula da Abban a d'akin. Da sauri doctor yabashi kujera ya zauna, k'afa d'aya kan d'aya ya d'ora ya Ciro waya a aljihu yana danne-danne. batare da ya kalli doctor ba yace, “kunyi gyaran karayar?”. Doctor yace, “eh ranka ya dad'e duk an gyara, saidai na hak'ark'arinsa yaso kawo matsala, amma Alhmdllh komai ya dai-daita”. “humyim, maganar bayanan danace a tattara minfa?”. “shima komai ready ranka ya dad'e ”. “o right, insha ALLAH zuwa jibi nakeson mu tafi, amma wai har yanzu bai ta6a farfad'owa bane?”. “ai ba'a sume yakeba, allurar damuke masace kawai takesakasa yawan barci”. d'ago ido Galadima yayi yana kallon doctor d'in, yace “amma danme ake masa?”. “ itace ke taimaka masa wajen rage masa rad'ad'in ciwukan, dan maganar gaskiya yana cikin matsanancin ciwo”. Cije lips Galadima yayi kawai, yace “ALLAH ya bashi lafiya”. “amin ya rabbi”. ‘cewar doctor. Daga haka suka fito shida doctor d'in. Inda Harun yake Galadima ya nufa, “brother yau ba zakaje aikiba kenan?”. Kallon agogon hannunsa Harun yayi, sannan ya kalli Galadima, “ka rikitamu ne ranka ya dad'e shiyyasa ban kula time ya tafi hakaba”. Murmushi kawai Galadima yayi amma baice komaiba. Harun yay musu sallama ya fita da nufin zuwa anjima idan yatashi aiki zai dawo. Su yaa Hameed sukai masa godiya da fatan alkairi sannan yatafi. Daddy ya kalli su yaa Hameed d'in yace ai kuma da tafiyar kukayi, karku makara wajen aiki”. A ladabce suka amsa masa da to, suna shirin barin wajenne saiga motocin su waziri sun shigo, dole su yaa hameed suka dakata. Waziri ne da matawalle, sai Garkuwa da baraya, sai kuma wasu manya-manyan 'yan majisar Sarki. dogarai duksun kasa sun tsare, wasuma zato suke sarkinne yazo da kansa. Su daddy ne suka musu iso har d'akin da Abba yake kwance, sosoi suka nuna tausayawarsu gareshi, sunja doguwar addu'ar samun lafiya da fatan alkairi ga Abba. Sannan suka Isar da sak'on Sarki. Sun d'an jima a d'akin suka fito da nufin tafiya, a dai-dai time d'inne kuma doctor Farida ta iso gaban Galadima cikeda sassarfa. Bakinta a washe tamkar gonar auduga. Wani dogari Na k'ok'arin dakatar da ita Galadima ya d'aga masa hannu alamar ya barta tazo. Cikin girmamawa doctor Farida tace “wannan asibiti da dukkan jama'ar cikinsa suna taya masarautar gagara badau murnar samun k'aruwa daga jikin gimbiya Munaya, insha ALLAH nanda watanni 7 dawasu satittika zata zama uwa, ma'ana tana d'auke da cikin wata 1 da sati uku”. Atare dogarai suka d'auki kabbara, Galadima dake tsaye baki bud'e cikin tsantsar mamaki ya kafe doctor Farida da idanu, sai kawai yashiga zame agogon hannunsa mai masifar tsada da k'yau ya mik'ama doctor Farida. Sauban yazo ya rungumesa, hakama matawalle. 'Yan gidansu Munaya sai suka koma 'yan kallo kawai, amma bakin kowa yakasa rufuwa. Doctor Farida ta kalli Galadima cikin mamaki da al'ajabi, “ranka ya dad'e ni Na cancanci wannan agogon mai d'unbin tsada kuwa?”. Wani murmushin Daba a cika gani Galadima yayiba ya saki, ya gyara tsayuwarsa yana fad'in “idan duk abinda na mallaka a duniya kike buk'ata zan baki shi, saboda wannan shine albishir Na farko da aka ta6amin Na farinciki a rayuwata, kifad'i dukkan abinda kike buk'ata inhar baifi k'arfina ba kafin nabar asibitinnan za'a kawo miki shi”. Kanta ta shiga girgizawa, kafin ta d'aga agogon ga mutane su gani. Mamaki ya cika kashe matan gidansu Munaya hassada da al'ajabi ya cika zukatansu, tunma ba'a haifi cikinba Galadima yake wannan rawar kan inaga an haifoshi?, Kansu bai kuma kwanceba saida sukaji waziri da baraya Na sanarda tasu k'yautar ga doctor Farida, hakama matawalle da Nuren. Doctor Farida fa ta rikice, itakam yau taga farar rana, (🙄idan ta ALLAH ake niya kamata abama wad'annan k'yaututtuka ma😏). Nuren da matawalle suka hau rabon kud'i a asibitin, tamkar basu San ciwonsu ba. Waziri kam d'akin da Munaya take kwance aka musu rakkiya, sun mata addu'a kafin su fito, kowa bakinsa a washe, wasukam ta cikin Na ciki kawai😳🤭. Kafin kace mi labari yagama zagaye asibitin, gidan Sarki kam kafin su waziri su Isa labarin cikin Munaya yaje. hakama Sauban ya kira su Momma ya guntsa musu, Momma saida tayi sujudar shukur. Abie bakinsa yakasa rufuwa, kamar daga sama sukaji yace “ALLAH ya inganta”. Dukda a hankali yayi maganar hakan bai hanasu ganin motsawar la66ansa ba, Khaleel dake kusa dashi yace “Lah Abie yayi magana Momma!!”. ba momma ba hatta da jakadiya sakin kwanon hannunta tayi ta waigo tana kallon Abie. Aunty Mimi ta tura laptop d'in gabanta tafad'o, hakama Samha wuntsilowa tayi daga kujerar datake zaune tayo inda gadon Abie yake. Gaba d'aya suka rufu akan abie, kowa yanason sanin gaskiyar batun Khaleel, murmushi Abie yamusu yana jinjina kai alamar gaskiyane, sannan a hankali yakuma furta “da gaske Khaleel yake”. Ai yau babu kunya Momma ta rungume Abie a gabansu aunty Mimi ta fashe da kuka mai ban tausayi. Aunty Mimi ta had'a momma da Abie d'in ta rungume itama. Jikin Samha har 6ari yakeyi takira Number Galadima ta Nigeria. Ya rako su waziri da zasu tafi kiran Samha ya shigo, bai d'auka ba, itakuma bata gaji da kira ba. Saida su waziri suka wuce sannan yaciro wayar a aljihunsa cikeda haushin wanene mai nacinnan. yana dubawa yaga Samha Ce. Murmushi yayi kawai sannan ya kirata da kansa, bugu d'aya Samha ta d'aga, kuka kawai ta fashe masa da shi, zuciyar Galadima tashiga tsitstsinkewa. tsawa ya daka mata yana tambayar lafiya?. Share hawayenta tayi, murya Na rawa tace, “Uncle Sam wlhy Abie yayi magana, yanzun nan da Uncle Sauban ya kira yace aunty gimbiya nada ciki sai Abie yace ALLAH ya inganta”.. Galadima ya ciro wayar a kunnensa ya kuma kallon number, tunaninsa wasune kawai keson masa yawo da hankali, ganin dai da gaske number Samha d'in ce saiya maida a kunnen, cikin sanyi murya ya kira ainahin sunan Samha, “Zeenah! banason wasan banza kema kin sani”. “wlhy Uncle ba wasa nakeba, ga Momma ma kaji awajenta”. Kafin yace wani Abu yaji muryar Momma namasa sallama, yanayin muryarta yasakashi lumshe idanunsa. Momma tace, “Muh'd! Yau ranace dabazamu manta da itaba a tarihinmu, k'yautar abinda kud'i baya saya, ALLAH kuma yabama takawa damar magana, narasa yanda zan musalta farin cikina Muh'd”. Wasu hawayene suka gangaro a kumatun Galadima, ga murmushi yak'i barin fuskarsa, cikin nutsatstsiyar muryarsa yace “Momma ko yanzu Ubangiji ya d'auki raina yagama min komai, Momma mizanyi duniya tasan ina cikin tsantsar farincikin da tunda nazo duniya ban ta6a riska ba?”. Dariya momma tayi, tace “godiyar ALLAH ta wadatar da komai Muh'd, lallai yarona zai zama baba”. Galadima yayi dariya yana goge hawayen fuskarsa,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92