Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bai gama sakiba, ki Ce masa sai dare zaku sallameni kawai”. 'Yar dariya tayi, ta nunamin Galadima dake bakin k'ofa tsaye ya hard'e hannaye a k'irji. Baki na tunzuro gaba saboda borin kunya. Shikuma ya janye idanunsa yana ta6e baki. Doctor Farida ta bamu sallama, na d'auki alk'yabbata na saka, tareda d'aukar handbag d'ita, sai wani ciccin Magani nakeyi, shi da nakeyi danshi yawani share tamkar bai gane da shi nakeyi ba. Jinai ya sak'alo hannunsa cikin nawa, na kalleshi da sauri, saiya kannemin ido d'aya. Ja nayi na tsaya, shima saiya tsaya, ga mutane duk sun zubo mana idanu, kuma har 'yan gidanmu. tamkar zan fasa ihu nace, “yalla6ai ni dai wlhy ka sakeni, kai bakajin kunyar su innarmu ma?”. Yace “kai ALLAH dai ya shiryeka Sameer, yalla6iya Sameer najin kunyar su Innarmu fa, sai dai kuma yana gudun amasa gangancin abin cikin kwan ne”. Kallonsa nayi, “ wai minene wannan abin cikin kwan daka ishi mutane da fad'a”. Ya d'an d'ora hannunsa saman bakinsa alamar mamaki, “yamzu nan bakisan abin cikin kwan ba friend? Lallai news ya wuce dake, ina tayaki jaje kam”. Kuma kullemin kai yayi a duhu. Ita dai doctor Farida dake bayanmu sai kuma birgeta muke da bata dariyar salon namu. Mutane kam dake kallonmu tunaninsu koda doctor Farida muke magana, Dan bazaka ta6a d'auka Galadima ya iya zaro magana hakaba. nikaina mamakin dama yana magana mai tsayi irin haka nakeyi, narasa miya d'abbak'a wannan farin cikin nasa na yau?, duk da bawai yanata dariya baneba, fuskarsa nanan yanda take babu walwala, sai dai yau akwai sakewa tattare dashi, kuma yakan yawaita murmushi bakamar ko yausheba. Nidai nace, “dan ALLAH yalla6ai kayi hak'uri, wlhy bazan iya zuwa gabansu baba k'arami ahakaba”. Baice komaiba ya saki hannuna, amma munci gaba da tafiya kafad'a da kafad'a dashi. Wata kuyanga cikin kuyangin da uwargidan Sarki ta had'omu tai saurin tasowa ta kar6i bag d'in hannuna, ban musaba na mik'a mata, mutane sai gaishini sukeyi, nidai kunyama ta isheni, Dan wasu sun girmemin. Mun Isa gaban 'yan gidanmu, kowa ya taso yana k'ara min sannu da jiki, nidai sai ce musu make na samu sauk'i. d'akin da Abba yake muka shiga, hawaye suka cikamin idanu, Galadima ya ruk'o min hannu, kallonsa nayi saiya girgiza min kai alamar kar nayi. Bance komaiba na janye idanuna, sannan na k'arasa gaban gadon nafara tofa masa addu'oi, shima Galadima ya matso ya tayani, daganan fitowa mukayi, Galadima yakuma gargad'ar police d'in akan su kula sosai, inhar wata matsala ta biyo baya to suyi kuka da Kansu. Cikin girmamawa suka amsa masa da insha ALLAH hakan bazata faruba ma. Ni dai ina wajen 'yan gidanmu, jinake kamar karna tafi wlhy, amma innaro tace kartaji karta gani, nabi mijina naje gida na huta, suma sauran 'yan uwana duk gida zasu tafi hakanan, tunda dai iya k'ok'ari galadima tsaye yake akan komai na abban, dukkan kulawa yasaka ana bashi gwargwadon iko. Nidai sai tunzura baki nake su Fiddausi namin dariya. Muna haka Galadima ya k'araso wajen, cikin girmamawa yace yakamata suma 'yan gidanmu suje gida hakanan su huta, insha ALLAH Abba zai samu kulawa tamkar suna nan. Godiya suka shiga yimasa, innaro nata kwararamasa addu'oin gamawa da rayuwa lafiya, da samun afuwa shima ga mahaifinsa, ta k'are maganar da f'adin “ALLAH ya kawo mana kishiyata ko angona duniya lafiya”. K'asaitaccen murmushi Galadima yayi, a kan la66ansa ya amsa da ammin Granny ”. Daga nan wajen Munubiya muka nufa, suma 'yan gidanmu suka shiga dansu k'ara ganin Abba su tafi. Munubiya na kwance tana barci har yanzu ana k'ara mata ruwa, rungumeta nayi ina hawaye, yayinda Galadima da yaa Marwan suke gaisawa cikin mutunta juna, inajinsu sunama juna Congrat, amma ban fahimci na mineneba. Nace “yaa marwan wai mike damun sweetheart ne haka ta rame?”. Dariya yaa marwan yayi, yace “babynku ne”. “lah yaa marwan kana nufin tanada cikine?”. Kansa ya jinjina min. Cikeda murna na kuma rungume munubiya ina fad'in “ashe na kusa zama mummy”. Galadima ya kauda kai gefe yana murmushi kawai, shina yaa marwan sai k'aramar dariya yakeyi. Da k'yar dai na hak'ura na baro asibitin nan badan nasoba, suma 'yan gidanmu duk sun wuce gida. ***************** A mota sai zun6ire-zun6iren baki nakeyi, saboda haushin banso rabuwa da 'yan uwana ba yanzu, Galadima ya wani shareni. shikam dukya gajine, bai cika wahalar zirga-zirga irin hakaba, gashi dama bawani isashshen barci yasamuba jiya. Batare dana kalleshi ba nace “wai ina yaa Sauban ne?”. Bai d'ago daga latsa wayar dayakeyiba ya bani amsa da “suna tare da Nuren”. Da sauri na kalleshi danjin ya ambaci sunan Wanda nake son Sanin wanene shi?, cikin kwantar da murya nace “yalla6ai wai wanene Nuren? ”. Tambayar tabashi mamaki, amma saiya share ya d'ago muka had'a ido, kowa ya janye cikin basarwa. bai bani amsarba har muka shiga cikin masarautar...................✍🏼 Kuyi manage da wannan sister's🤗. *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻 [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 ~Book 2~ 👉🏻8⃣ .........Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima. Casuke ALLAH dai ya infanta mana, ranki ya dad'e ALLAH ya saukeki lafiya. Cikin tsantsar farinciki yake amsa musu, murmushi yak'i barin fuskarsa. Nikam zuciyata Ce ta shiga tsitstsinkewa, idan har Na fahimci inda zancensu ya nufa cikine dani kokuma wani keda cikin? Galadima Na kalla, amma saiyamin wani miskilin murmushi yana kauda idonsa, alk'yabbar jikinace kawai taima mutane katanga da ganin zufar data gama jik'emin jiki. Tun a falon farko Na dakatar da kuyangin da damuke tare, handbag d'ita Na kar6a nace suje nagode. cikeda girmamawa suka amsamin suka fita suna min addu'ar k'ara samun lafiya. suna fita na juyo ga Galadima, amma tuni ya shige d'akinsa. handbag d'in Na dungurar saman kujera nabi bayansa, hankalina bazai ta6a kwanciya ba sainaji gaskiyar lamarinnan. Na iske babu kowa a falonsa, Dan haka nashiga bedroom d'insa, ranar farko kenan dazan fara shiga bedroom d'in. babu kowa nanma, sai motsin ruwa dana jiyo a bathroom. Waige-waige nafarayi ina k'arema d'akin kallo, komai ya birgeni a d'akin, sai k'amshin mayen turarensa da ya mannema d'akin. karaf idona ya sauka ga takarda kusada kayan daya cire, mik'ewa nayi Na d'akkota, Na dawo Na zauna. cikin nutsuwata nafara karantawa, nai mugun waro idanu ina fad'in “wlhy impossible, abindama bazai ta6a yuwuwaba kenan” sai kuma Na fashe da kuka. Dai-dai lokacin Galadima ya fito daga bathroom, sanye yake da rigar wanka fara, ahankali ya ringa takowa idonsa a kaina, sai dai fuskarsa a d'aure take tamkar bashine cikin walwala ba a asibiti. Bai k'araso inda nakeba ya tsaya a tsakkiyar d'akin ya cigaba da goge ruwan kansa zuwa fuska hankalinsa kwance. a harzuk'e nayo Kansa ina cigaba da kukana, naja birki a gabansa, da d'anyatsa Na nuna masa takardar, har yanzu kuma kukan nakeyi, nace “wannan cikin a jikin wa ake nufin yake?”. d'auke fuskarsa yayi daga kallona yana wani lumshe idanu, batare daya bani amsa ba ya taka zuwa wajen mirror, cikeda izza yace “sunanwa kika gani a jikin takardar?”. Da sauri Na ruk'o bathtub d'in jikinsa, cak ya tsaya, murmushin gefen baki yayi, saikuma ya kuma d'aure fuska sannan ya juyo yana fuskanta ta, inda Na rik'e

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});