Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 78

Chapter 78

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dake bayansa shima ya shak'a masa, harda mangareshi yana fad'in “kwallon shege taka ta k'are, inakai ina satar sarakunanmu insha ALLAH”. dariya taso kufcema Muftahu amma ya danne bakinsa da hannu yana girgiza kai saboda tsiyar Ameer. Fad'uwar wani da suka juyo ya sakasu kuma saurin waigawa wajen, Galadima ne ya sakeshi ya fad'i, “shegen k'arfin jinine dashi dak'yar abin yay masa tasiri”. Galadima ya fad'a yana halbinsa da k'afa. Gaban d'ayar baiwar dake la6e jikin labule ya fad'in, dan tabbas wannan muryar Galadima ce, kowa yasan bai iya R ba, zuface tashiga keto mata jikinta na 6ari, ta to she bakinta saboda kuka daya kufce mata, saigata tana tsilala fitsari saboda ganin Galadima yanufo ta wajen, shikenan itakuma tata tak'e, wannan zakin gagara badau d'in binneta kawai zaiyi da ranta. Waige-waige Galadima ya fara saboda jin numfashin mutum dayakeyi kad'an-kad'an ta wajen, har yayi gaba ya dawo baya yana yaye labulen wajen. shi da farkoma ya zata aljanace saboda yanda ta zazzaro masa ido. fincikota yayi ya Watso tsakar d'akin, mamaki ya kamashi ganinta da kayan manyan kuyangin gidansu. “tashi tsaye”. ya fad'a cikin matuk'ar d'aure fuska, kad'an yarage kashi ya kufcemata. “ina suke!!!”. Yafad'a cikin matuk'ar tsawa daya firgita hatta su Sauban dake saurarensu a waya. Wannan tsawar tasa ce ta saka d'ayan fitowa a tsorace da gun a hannu, Aunty Salamah dake bayansa bai saniba ta hankad'ashi yay gaba zai fad'in, Nuren ya ida tad'eshi da k'afa. Gun d'in data fad'i ta silalo gaban Galadima ya taketa da k'afa yana huci da taunar lips. Handkerchief d'in hannunsa yasaka ya d'auki bindigar, ya saita namijin da ita. Mazari jikinsa ya fara yana d'aga hannu sama, “dan ALLAH ranka ya dad'e karka kasheni, wlhy bansan komaiba, oganmu ne yasan komai da wannan baiwar”. Kunamar bindigar Galadima ya d'ana, nanfa su Muftahu duk suka rud'e, Nuren yace, “Brother please karkayi harbi, nasan zasu fad'a mana, dan ALLAH kayi hak'uri”. Gaba d'aya jijiyoyin kan Galadima sun mimmik'e, sai fidda huci yakeyi a wahalce. Muftahu ma yashiga rok'onsa, Su Saleem dake sauraren komai dagacan duk suka rud'e, Sauban yace “yaa Sam ALLAH ya huci zuciyarka, amma idan ka aikata haka a wajenwa Zamu samu hasken sauran abubuwan?, dan ALLAH kayi hak'uri badan mun isa mu saka ka ba, saidan halin da mahaifinmu ya tsinci Kansa tsawon shekaru, gakuma dama tazo mana ta Sanin sirrin 6oye, muyi amfani da ita ta sauk'ak'ak'iyar hanya....” Sakin gun d'in Galadima yayi ak'asa yana dafe k'irji, wani mugun bugawa zuciyarsa keyi, da baya-baya yanemi zubewa a k'asa, cikin hanzari Nuren da Muftahu suka taresa, da taimakonsu ya zauna akan kujera. Yana nuna baiwar da d'ayan hannusa. Aunty Salamah data fahimci mi yake nufi tace, “ina yaranne?”. Jikin baiwar Na 6ari ta nuna k'ofar wani d'aki, shiga Aunty salamah tayi itada Ameer suka d'akkosu. Saidai duk a firgice suke, dan yaran babu alamun rai tare dasu, zufa ta shiga ketoma Aunty Salamah, haka ta fito rungume da Abdurraheem da Amaturrahman, shikuma Ameer ya d'akko Abdurrahman yana fad'in “Aunty kamarfa yarannan sun mutu”. Wannan kalma caraf a kunnen Galadima. Wata muguwar zabura yayi yamik'e tsaye, sai ya kuma dafe k'irjinsa da sauri hajijiya tafara katantanwa dashi, basu fargaba sai jinsa sukayi kawai a k'asa. Gaba d'aya suka kuma rikicewa, sukayi kansa. Muftahu yace, “bamuda isashen lokaci, asuba ma ta gabato, dolene mubar gidannan dan ko yaushe zamu iya gamo da abinda bamu shirya masaba”. Duk sunyi na'am da wannan maganar tashi, nan fa suka fara kwasar wad'anda suka sumar suna kaiwa mota, sannan suka tasa k'eyar d'ayar baiwar da wancan, suma. Yayinda Nuren yad'an bincika gidan, ganin babu wani abunda zasu k'aru dashi yazo suka kama Galadima daya Suma suka fita dashi. Hankalin Sauban ya tashi matuk'ar tuk'ewa, ya fito yana nufarsu da ta6a jikin d'an uwansa, “Yaa Nuren miya farune? miya faru da Yaa Sam?”. “Sauban bamu hanya, ba lokacin wannan baneba yanzu”. Sole Sauban ya matsa baya hawaye Na kwarara a idonsa, suka shinfid'ar da Galadima a bayan mota, sai lokacin Sauban yaga yaran a hannun Aunty salamah da Ameer, da hanzari suma ya nufesu, Aunty salamah ta bashi Abdurraheem, jujjuya yaron yayi yaji kamar baya numfashi, “innalillahi....” yashiga maimaitawa zufa Na keto masa, dolene Yaa Sam ya suma, hawaye yafarayi yana rungume yaron a jikinsa, Tausayin dukkan ahalinsa da suka kwallafa rai ga yaran ya kamashi, musamman ma iyayensu, ya ALLAH nasan bazaka jarabcemu da abinda bazamu iyaba, ALLAH kabamu juriya”. Muftahu yace, “su shiga mota, duk shiga sukayi, Nuren dasu Ameer suka wuce da wad'ancan sauran wani waje daban, Muftahu kuma ya kira police d'in da suka shirya komai dasu, a hanya suka had'u, sai sukai joining d'insu tamkar tare sukayi aikin, suka kira manyansu suna sanar musu gashifa sun kama wani matashi da baiwar masarauta da yaran.... Wannan labari yama su d.p.o dad'i ya kira IG shima ya sanar masa, yaji dad'i shima, koba komai mai martaba zai yaba k'ok'arin dasukayi, akace yanzu suna inane?. Amsawa sukai da gasu a masarauta, dan harda Galadima sukayi aikin, yana kuma cikin wani yanayi shida yaran yanzu haka. Basuda za6in daya wuce suce musu to suma gasunan zuwa masarautar. Tun'a mota su Muftahu sun gargad'i baiwar nan da d'ayan mutumin akan suce su biyune suka sacesu, inhar sukace basu kad'ai bane wlhy saiya kashesu, sannan su tanaji fad'ar wani abun ba ainahin gaskiya ba, (dan Galadima baya buk'atar police su shiga cikin aikinsa yanzu, yafison saiya kama kowa sannan, dan inhar police suka shiga aikin mutane da yawa zasuyi escape ne) shiyyasa Muftahu yayma wad'ancan gargad'in tunma kan su k'arasa cikin masarauta. Da yawa wasu basu rintsaba a masarauta gagara badau yau. Munaya dai dole aka sake d'irka mata allurar barci mai k'arfi, dan kusan kuma haukace musu tayi gabannin asuba, dalilin wani barci daya figeta tayi mafarki mai matuk'ar tada hankali. Su inno Na zaune har yanzu suna kai kukansu ga ALLAH Muftahu da Sauban suka shigo d'auke da Galadima da suka kamo tamkar gawa, sai Saleem da police biyu dake falo d'auke da yaran sukuma. Zaram duk suka mik'e suna tambayar lafiya? Miya sami Galadiman?. Basu sami wata amsaba, saida suka kwantar dashi a gadon sannan Sauban ya share hawayen fuskarsa yana fad'in “suma yayi inno”. Aunty Mimi da mom sukayi kan Galadima suna kuka, inno tace, “kun samo yaranne?”. “eh gasu can a falo tareda police, saidaifa duk sun mutu, shiyyasa ma Yaa Sam ya suma”. yak'are maganar yana kuka. Hawaye suka zuboma inno, waya ta d'auka ta kira papi, Wanda shima dai a zaune suka kwana dagashi har Sarki jalaludden. A time d'in dama har ankai musu bayanin shigowar su Muftahu d'in. Yau dai kam tilas Manyan Sarakuna biyu suka nufo sashen Galadima da Kansu, abinda waninsu bai ta6a yiba kenan. Maganar ganin yara yafara baje Masarautar tun'a daren, dan kowa kunenensa a bud'e yake, da masu fatan a gansun da masu fatan kar'a gansun. Lokacinda papi da mai Martaban suka iso Inno Na rungume da yaran duka tana hawaye, sukuma su Aunty Mimi suna bedroom wajen Galadima. Kusan a tare Akash da Dr jalal suka iso dasu papi. Mai Martaban da papi suka kar6i yaran daga hannun inno, Suna zama bisa kujerun. Akash wajen Galadima ya nufa, dukda ba shine likitansa Na

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});