Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saikuma marasa tafiya. kuka nazauna rerawa babu mai lallashina. A wannan halin Samha tashigo ta sameni, itama hankalinta tashi yayi, takira Momma a waya ta sanar mata gani inata kuka. Babu shiri Momma tabaro jakadiya da aunty Mimi a hospital tanufo gida, dan itama a cikin damuwa take, na rashinjin Galadima. dan bai sanar da ita ina zaijeba, itakuma bata kawo yana Nigeria bane, tunda bai ta6a tafiya bai sanar mataba, tazata tafiyar kota shafi company d'insu ne. Ta iso ta iske Samha nata lallashina, jikinta a sanyaye tazo bakin gadon ta zauna, hannuna ta kamo ta jawoni jikinta, batayi maganaba tashiga shafa kaina da bubbuga bayana, munkai kusan 10minutes a haka, harna bar kukan sai ajiyar zuciya kawai. A tausashe tace, “kiyi hak'uri kinji Munaya, ni kaina hankalina a tashe yake da rashin kiran, dan baita6a hakaba”. (ALLAH Sarki momma ita ta zata saboda rashin kiran Galadima ne, shima rashin jinsa na damuna kam, amma yanzu na Abba ya danne komai). Samha tace, “Momma amma an gwada Number sa ta Nigeria?”. “Samha banyi tunanin can yajeba, amma bara na gwada na gani”. Wayarta ta d'auka ta kira number Galadima ta Nigeria, a mamakinta kuwa saita shiga, cikeda al'ajabi taciro wayar a kunnenta takuma kallon number d'in, tabbas itace dai da gaske. Harta katse bai d'aukaba, takuma kira a karo na biyu. Lokacin Galadima suna mota zasuje inda Accident d'in Abba yafaru. ganin momma saida gabansa ya fad'i, harta tsinke yakasa d'auka, sai da aka kuma kira Nuren ya d'aga yasaka masa a kunne. muryarsa a sanyaye yay sallama, daga can Momma tace, “lallai Muh'd, yanzu nan dan zakaje Nigeria shine ka 6oyemin? kabi ka tada mana hankali muda matarka, maimakon ma ka sauka kakiramu hankalinmu ya kwanta”. Runtse idanunsa yayi, muryarsa a sark'e yace, “ki gafarceni Momma, wlhy banason ki hanani zuwanne, nazo kuma na iske wani tashin hankali, shiyyasa ban kirakuba”. Mik'ewa Momma tayi tafice daga d'akin, ni da Samha muka bita da kallo, tace “innalillahi.. miya farune Muh'd? ”. Zuciyarsa na suya ya zayyane mata komai daya faru, dukta rikice, “kodai wani yafad'ama Munaya Muh'd?”. “banajin hakan gaskiya Momma, dan mutanen gidansu basuda Nutsuwar ma sanar da ita, amma miya faru?”. “hankalinta gaskiya a tashe yake, dan ina asibiti Samha takirani tana sanarmin Munaya nata kuka, babu shiri nabaro asibitin nazo gida, da k'yar na lallasheta, ni na zatama ko rashin kiran dabaka yi baneba”. “to maybe rashin kiran nawane gaskiya. Amma batasan komaiba, Momma kuma banason tasani harsai yafara samun sauk'i kin...........” Da sauri Momma ta katseshi “bazai yuwuba Muh'd, dolene anema mata ticket ta taho ko itada Sauban ne, mahaifi yawuce gaban wasa, ko kai baka sanar da itaba dolene wani a cikin 'yan uwanta ya sanar mata, bakuma zata ta6a samun kwanciyar hankaliba, mukuma saita mana wani kallo daban na 6oye matan da mukayi”. “to shikenan Momma, Sauban yaje ya bincika ko'akwai jirgin dazaizo Nigeria, saiya nema musu tickets, yanzu muna kan hanyar zuwa inda Accident d'in yafaru, idan na koma gida zan kiraki”. “to shikenan saina jika”. Momma ta kwantarmin da hankali sosai, sannan takoma asibiti da alk'awarin indai gida nakeso zatasa Sauban ya nema min ticket natafi, amma bata fito ta nunamin ainahin abinda ya faru zanje gidanba. Dukda inason tafiya gida sainaji kamar akwai abinda ake 6oyemin, saboda wannan tafiya ta gaggawa, sai dai ban tambaya ba nabarma zuciyata kawai. Sauban kuma yashiga mana shirin tafiya. ______________________________ Tunda Galadima ya ajiye wayar babu Wanda yayi magana a cikinsu, daga Nuren har Galadima kowa damuwar ganin halin da Abba ke ciki tanacin zuciyarsa. Su Dady ma suna mota kowa shiru, tausayin d'an uwansu da addu'ar samun lafiyarsa kawai kowa keyi. Police d'in dasuka musu jagora inda Accident d'in yafaru ne suka samu hanya da k'yar, dan motar Abba da thriller d'in data hau kan motar Abban sun tsare rabin hanyar, hakanne ya haddasa go slow sosai, Galadima kam yakasa koda motsi, saima tsirama motar idanu da yayi tacikin glass d'in motar zuciyarsa Na matuk'ar suya. Saida Nuren ya taimaka masa sannan yafito. glasses d'insa yad'auka yasaka, Wanda ya 6oye jajayen idanunsa. thriller d'in data hau kan motar Abbanmu Na gefe itama a kife take, duk Wanda yaga motar ta abbanmu zaiyi zaton mai motar bazai rayuba, saboda fita hayyacinta da tayi. Jingina da mota kawai Galadima yayi ya hard'e hannayensa a k'irji ya zuba musu idanu. Nuren kam yanacan jikin motar sosai tare da police d'in dasu Dady ana laluben wayar Abba acikin motar. Harsun fidda rai da samunta ma, da k'yar aka sami wayar, amma tayi rutsu-rutsu, ga jini dukya bushe a jikinta, cikin Leda aka Sanya, Nuren ya kar6a yabama sarkin mota. Sund'an k'ara bincikawa kozasu samu wasu muhimman abubuwa, takardune kawai sai abinda ba'a rasaba. Nuren ya kalli police d'in yana fad'in “amma kamarma wasu sun d'ebi wasu abubuwa a motarnan?”. “zata iya yuwuwa ranka ya dad'e, Kasan mutane da anyi accident maimakon taimako dasuke bayarwa sai wasu su 6ige da sace-sace kuma”. Nuren ya jinjina kai kawai, danshi ba mutane yake zargiba. Yafi zargin wad'anda sukaso kashe abbanne kawai. Dady da baba k'armi da suke gefe kam harda kwallan su, Dan kallon motarma kawai ya ishi bawa shiga tsantsar tashin hankali. Sund'an jima a wajen kafin su tafi, Galadima dai yayi d'if, ko magana yakasayi. Su baba k'arami asibiti suka wuce, sukuma birnin gayu plaza. Tunda suka shigo ma'aikatan wajen suka zube suna kwasar gaisuwa, Nuren ne kawai ke iya amsa musu, galadima kam hannu kawai yake d'agawa. Kai tsaye Office d'insa Na plaza d'in ya shiga, saima yazo k'asar sau nawa bai shiga Office d'inba kwata-kwata. Ya zauna tareda zame hular Kansa da glasses d'in, sannan ya jingina kansa da kujera yana mai lumshe idanu. Nuren ma zama yayi kawai ya zuba masa ido, kusan minti 2 da zamansu Manager d'in plaza yashigo, gaisuwa yakumayi ga uban gidan nasa cikin girmamawa, Galadima ya d'aga masa hannu batare da ya bud'e idonsa ba. hakan yakuma tabbatarma manager babu lafiya kenan. Kirane yashigo a wayar Galadima, yad'an bud'e ido kad'an ya kalli phone d'in, Harun ne, tun d'azun yake faman kiransa amma bai d'agaba, yasan labarin zuwansa k'asar yazo musune. Yanzunma bai d'aga ba, ya share, saima kwanciya daya kuma gyarawa a jikin kujerar, da hannu Nuren yayma Manager nuni da yaje. Manager ya gyad'a kai sannan yafice yana mamakin miya ta6a yalla6ai hakane?. Idon Galadima a rufe yace, “Nuren wane layine akan wayarnan?”. Wayar Abba da sarkin mota ya goge fes, duk babu jinin yanzu Nuren ya d'auka ya bud'e, Mtn ne da glo aciki. ya kalli Galadima sannan yace, “glo and mtn ne”. Galadima ya bud'e idanunsa akan wayar shima, ya d'an yamutsa fuska sannan yace, “dolene muje office d'insu kenan, dan zanso sanin dawa yake mu'amulla, k'ilama zamu iya samun wani abidance”. “o right, hakan yayi, amma waynote mu fara zuwa kaci abinci kasha maganinka, dan bazai yuwu muyita yawo bakaci komaiba, ni gamma ni nayi breakfast a hotel kafin na fito, kaiko nasan bakaci komaiba, gashi har time d'in lunch yayi”. “karka damu, banajin wani yunwa ni kam, muje dai muyi salla muje”.. “ina, bazai yuwuba, bara nasa amana oder a wancan restaurant d'in naga suma sun iya abinci”. Galadima bai sake cewa komaiba, Nuren

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});