Chapter 46
Chapter 46
kama da anmasa dole yace, “Haba yalla6iya, sokike ki haifamin abin cikin kwan mai saurin kuka irinkine wai shin?”. Bansan Sanda murmushi ya su6ucema fuskata ba, na lumshe idanuna saboda bana da jimirin jure kallon da yakemin, shima murmusawa yayi, sannan yakai fuskarsa dab da tawa yana huramin iskar bakinsa a saman ido. Ban iya hanashiba kusan mintuna 2 sannan ya daina, bud'e idona nayi nad'an kallesa, ya d'agamin gira yana fad'in, “ya dai?”. Cikin tunzuro baki nace, “babu komai”. “To miye abin jin haushi daga tambaya”. ‘yay maganar yana sakin kumatuna’. Binsa nayi da kallo, ganin zai fara k'ok'arin cire kaya, na mik'e zan fice, dan yanzu na lura lamarinsa kullum k'ara girmama yakeyi, baya shakkar cire kaya a gabana ko sakawa, sai dai ni na fita na bashi waje. Hannuna ya rik'o, na waro ido waje cikin mamaki. “ina zaki?”. ya fad'a cikin tsare gida. “ba wanka zakayi ba?, idan kagama zan dawo ai”. “toni dodone?”. “A'a na fad'a ina ta6e baki”. “to koma ki zauna ki kalli sadakinki”. Idanu na waro masa waje da hangame baki. Yiyai kamar bai ganniba ya basar. bai sakeniba yakuma cigaba da cire kayansa da hannu d'aya. Ni daifa k'in kallonsa nayi, dan wlhy kunya nakeji sosai, dukda 'yar shak'uwa ta shiga tsakaninmu hakan bai sa mun saki jiki da junaba, garama shi idan rashin kunyarsa ta motsa yakanyi abinda ya gadama yana basarwa a dole kar'a kawo masa raini. Yakan bani dariya sometimes, amma nima saina Basar saboda Jan aji. Iska kawai naji a cikin kunnena, da sauri na waigoshi, ganin sa dagashi sai boxer sai na juya fuskata. Bayana ya koma ya zagayo da hanayensa duka akan cikina, yayinda kansa ke a kafad'ata, muryarsa can k'asan mak'oshi yace, “miya sakaki kuka?”. Salon da yay maganar ya sakani lumshe idanu saboda tsigar jikina data tashi. Nace “kabari ka gama zan fad'a maka”. “miyasa ba yanzu ba?”. “ka saka riga to”. Murmushi yayi yana shafa cikina, “my friend sarkin tsiwa sarkin kuma Kunya, akwaiki da abubuwan bi........” Saikuma yay shiru yak'i k'arasawa, hannuna na saka na rik'e hannunsa da ke yawo saman cikina, nace, “ka k'arasa mana, akwaini da mi?”. “Humm” kawai ya fad'a yana sakina, yaja bathrobe d'insa dake jikin hangar ya sanya, saida naga ya fara k'ok'arin d'aure igiyar sannan na d'ago na kalleshi. “To mikuma kike kallo?”. Ya fad'a cikin tsare gida. Baki na ta6e ina fad'in, “miye abin kallon to?”. Ya d'an fiddo ido sannan ya matsoni, “zona nuna miki”. Nasan ko guduwa nayi saiya kamoni dan haka na duk'e ina fad'in “wash ALLAH cikina”. Tsayawa yay cak, saikuma ya tako da hanzari yana tambayar lafiya?. cikin marairaice face nace “Motsi yakeyi ALLAH”. rankwashina yayi aka yana cewa “ke d'inan ko”. Dafe wajen nayi, bai kulani ba ya shige bathroom, na harari bayansa ina masa gwalo, nasan inda banyi hakaba bakina ne zaisha wahala. Ina zaune ya fito, na d'auke kaina tamkar ban ganshiba, shima hakan yayi, ya wuce wajen frigate ya d'akko ruwa da Kofi, kujerar dake wajen karatunsa ya jawo ya zauna yana fuskantata, batareda yayi yunk'urin cire bathrobe d'in jikinsa ba, yanzun kam babu wasa a fuskarsa, ban damuba dan nasan halin kayana yanzu, yanzu zakiga yasaki jiki yana magana kamar ba shiba, anjima kad'an saiya koma Asalin Galadimansa dana fara gani a Hospital, Mara dariya mara later r😏. K'afarsa d'aya ya d'ora kan d'aya yana shan ruwa, yasha kusan rabi sannan ya cire, batareda ya ajiye kofinba ya maido dukkan hankalinsa kaina, “A kwana biyunnan kokin lura Abba yana cikin damuwa?”. d'ago idanuna nai na kallesa, a sanyaye nace, “abinda naji innarmu na masa Complain kenan yanzu, amma saiya nuna fusata”. “shine kika shigo kina kuka?”. Na jinjina masa kai batareda nace komaiba. Shima bai sake cewa komanba ya kauda idonsa daga kaina yana kur6ar ruwansa. kusan 2minutes sannan yakuma kallona, “Munaayaa mukawo k'arshen 6oye-6oye mana”. Kallonsa nima nayi, nace, “kamar ya?”. “humm” yafad'a yana cije lips, mik'ewa yayi tsaye ya ajiye cup d'in hannunsa a gabana, sannan ya shiga zagaye d'akin hannunsa goye a baya, nikam dai binsa kawai nakeyi da kallo kamar na samu television, maganarsa ta katsemin tunanina. “Munaaya! Mikuka ta6a gani a d'akin Abba ke da 'Yar uwarki?”. Zumbur na mik'e dan mamaki, “yalla6ai a ina kasan wannan?”. batareda ya kalleni ba yace “Munaya Sameer ya wuce dukkan tunaninki, dan haka fad'amin?”. Ajiyar zuciya na sauke, wadda ta tilasta masa juyowa ya kalleni, nace, “yalla6ai ba fad'a maka bane matsalar, kuskuren muhallin fad'arne da kuma makomata”. “bakida dukkan Matsala da wad'annan, idan bai danganceni ba zan d'auki matakin taimakon sirikina, makoma kuwa inada yak'inin kare martabar matata uwar d'ana ta kowanne hali”. Furicinsa yaban mamaki, dan haka nace, “matar Contract ko?”. “Well Duk yanda kika fassara dai-daine, abinda na Sani kawai wannan maganar batada nasaba da waccan, dan haka kibar kowanne a muhallinsa sai lokacin yinsa yayi”. “humm” kawai na fad'a na koma na zauna inda na tashi. Idonsa a kaina ko k'yaftawa bayayi. Na nisa sannan nafara fad'in, _“Na tabbata tunkan ka k'ulla alak'a dani saida kasan koni wacece, dan babban mutum irinka bazaiyi Abu babu wani tanadiba, banida matsala wajen maimaita maka sunana ko tarihin ahalin dana fito, kamar yanda kasani mu 'yan biyune hakan yasaka ba'a banbancemu ni da 'yar uwata, sai dai hallaya takan banbantamu ga Wanda ya sanmu, Munubiya mutumce mai hak'uri da yawan kawaici, a wajen gadon hali tabbas ta biyo mahaifiyarmu ne, sa6anin ni Munaya mai zafi da yawan tsokana, a lamarina babu ragi ko d'aga k'afa, inhar kaga nayi dogon zama da mutum babu sa6ani to ka tabbata ya tanaji matakan iya zama danine, basai amfad'a ba nima kaina nasan halayena na kamanceceniya dana Mahaifina da kuma kakata innaro, a wata litinin d'in da bazan ta6a mantawa ba sai mahaifinmu yayi wani bak'o, matsalar da aka samu shine yazo bai iske Abba a gidaba, a wannan ranar innarmuce da aiki, dan haka hak'in tarbar wannan bak'o saiya rataya a wuyanta, maimakon tayi da kanta saita saka cikinmu ni da Munubiya wani yayi”._.......................✍🏼 Mu had'u a page na gaba🤫 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu🙏🏻😭_* [7/3, 3:55 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉1⃣7⃣ _..................“Da haushi na d'auki ruwan da innarmu ta bani na fita, saboda muna tsaka da kallon wani film daneke masifar sone, Munubiya dan kartaje kaiwa saita hau barcin k'arya. Tunda na shigo shegen mutumin nan ya tsura min idanu yana lasar baki, kai kace tsohon mayene yaga nama, a zafafe na dire tiren agabansa ko k'ararsa zatasa ya dawo hayyacinsa, amma wawannan yayi nisa, na buga tsaki a zuciyata zan fice, caraf ya kamo hannuna, ban dubi girmansa ba na dage na watsa masa mari, hakan kuma yayi dai-dai da shigowar Abbanmu falon. Amma d'an iskan ganin Abbanmu da marin danai masa baisashi sakin hannunaba, saida Abba ya daka masa tsawa da fad'in “SD! wane irin iskancine wannan? a cikin gidana ka kama hannun 'yata?!”. Abba na rufe baki ina kuma bashi mari na biyu, tunda naga alamar shi bunsurune. a wannan karon ya saki hannun nawa, saboda janyeni da Abba yazo yayi, Abba ya nunamin k'ofar fita, koda na fita saina la6e a corridor d'in shiga falon bak'in._ _A
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92