Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 80

Chapter 80

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Yaseen yayi, yatashi rik'e da yaransa, kwantar dasu yayi sannan ya matsa ga Abdurraheem hannunsa dafe da k'irjinsa har yanzu, rankwafawa yay kan yaron ya sumbaci goshinsa da kumatunsa, sannan ya shafa kansa la66ansa suna motsawa alamun yana masa addu'ar fatan samun lafiya a garesa shima. A 6angaren Munaya Itama tana farkawa da kuka ta farka, tana kiran yaranta, itadai afad'a mata idan sun mutu kawai saita hak'ura. Rungumeta Munubaya tayi tana lallashi da mata albishir d'in dawowar yaran garesu, hakan yasaka Munaya d'agowa da sauri tana kallon Munubiya, “Sweetheart da gaske kikeyi?”. “da gaske nakeyi Sweetheart, yanzu haka suna tare da mahaifinsu”. Dad'i ya ratsa Munaya, ta kuma k'ank'ame Munubiya suka rungume juna suna kuka da dariya lokaci d'aya. Hakan kuma saiya sanya su inno kukan tausayinsu da sha'awar wannan k'aunar juna nasu. Saboda su mai Martaban sun shiga wajen Galadima sai akace ita Munaya tayi wanka kozataji k'arfi kafin su fito. Bata musaba ta amince, ruwa mai zafi laraba ta had'a mata, tashiga wankan. Tanayi tana kukan farin ciki. bata cuci kantaba tayi wanka sosai ta gasa jikinta. Kafin ta fito an gyara d'akin tsaf, sai k'amshin daddad'an turaren d'aki yakeyi, babu kowa duk sun fice. Su mai Martaban suna tare da Galadima, sunyi farin cikin tashinsa, hakama yaran. sunkuma yima Abdurraheem addu'ar tashi shima. Sun d'an jima a d'akin, dan har saida aka shigo dasu Dady da baba k'arami, Yaa marwan, Yaa Hameed suma suka gaidashi da masa jajen ALLAH ya kiyaye gaba sannan suka fita gaba d'aya. Daga nan manyan irinsu mama Fulani, inno matana Sarki da sauran su duk suka shigo suma, harda su innaro da akaita kuka. Galadima dai Kansa kawai yake iya d'agawa, idonsa a lumshe. Baya buk'atar kallon kowa a cikinsu. Su inno duk tausayinsa ya kamasu. Innaro aka share hawaye tace, “barka da arzik'i kaji, ALLAH ya kiyaye gaba, ya shiga tsakanin nagari da mugu, ya tona asirin duk makirin dake cikin wannan satar yara”. Duk da amin suka amsa. Galadima ma yace amin akan la66ansa. sai tunani yake ina Munaya take?, dan hankalinsa yafara tashi da rashin gilmawarta, musamman daya tuna a halin daya tafi itama ya barta. Yadai kasa daurewa ya bud'e baki da k'yar yace, “Mom ina Munaya wai?”. Saida mom ta matso da kunnenta sannan tajishi, tasan yana lafiya ma ya aka k'are da k'asaitar magana balle yanzun. Murmushi tayi, tace, “tana d'aki, itama sai yanzu ta farka, dan dole aka sake mata allurar barci bayan tafiyarka, waccan bata dad'eba ta saketa”. Tausayin Munaya ya kuma kamashi, ya jinjina kai yana yunk'urawa zaune sosai. Cikin yamutse fuska yace, “Mom nima yakamata nayi wanka Na rama sallolin dake kaina”. Mom tace, “to bara a kira su Muftahu su kamaka ”. Kansa ya girgiza mata da mata alamar, zai iya da kansa. Mom tace, “Alhmdllh”. Rigarsa ya jawo yasaka, dan da dagashi sai best. d'aukar Abdurrahman da Amaturrahman yayi ya fito, yabar mom tana gadin Abduraheem dabai farko ba. babu kowa a falonsa Dan duk sun fice. Da k'afa ya turo k'ofar, Munaya Na zaune a bakin gadon rik'e da mansa zata shafa amma dukta kasa, burinta taga halinda Galadima da yaranta suke ciki kawaine damuwarta, gashi har yanzu babu Wanda yazo yakirata akan su papi sun fita. bud'e k'ofar ya sakani d'ago ido. Zummbur na mik'e tsaye ganin Galadima rungume da yaran, ai yau nama manta dawata kunyar towel na d'aura, hawaye suka shiga zarya tsakanin idona da kumatu, Galadima ya tako a hankali zuwa gareni idonsa a kaina. Da sauri namatso garesa nima, nahad'ashi shi da yaran na rungume ina sakin kuka mai k'aramin sauti. Shiru yay kawai ya zubama gashinta ido yana tausaya mata daga ita har yaran, ansakasu a yak'in dabasu San mafariba, ya godema ALLAH da yarannan sunada sauran numfashi a duniya. Da baisan yanda zaiyi da munaya ba. Ganin kukan nata zaiyi yawa ya bud'e baki da k'yar yace, “ya isa mana”. d'ago idanu nayi na kallesa, cikin muryarta data dishe saboda kuka nace, “Nagode yalla6ai, dasun mutu nima mutuwa zanyi”. Murmushin gefen baki yayi, cikin d'age gira d'aya yace, “dama ana sonmu haka?”. Sai yanzu kunya ta kamani, nai k'asa dakai ina kallon k'afafunmu. Bai sake cewa komaiba ya ra6a ta gefena yaje ya shimfid'e yaran akan gado. bathroom ya nufa yana cire rigar jikinsa, nidai Na k'arasa gadon Na rungume yaran ina sumbatarsu, wani dad'i da tsantsar farin ciki Na ratsani, Na d'aukesu Na fara shayar dasu ko zasu rage nauyin da sukamin, aikam kamar jira sukeyi suka kama sha. Hannun rigar namijin Na d'aga saboda tanan muke gane shaidarsu, ganin Abdurrahman ne saina fara tunanin ina Abdurraheem shikuma?, hankalina yaso tashi amma saina daure ina jiran Galadima ya fito naji daga garesa. Galadima dake kallonta bata saniba ya d'an cije lips, ya tabbatar yanzu tana son yaransa, amma baisan miyasa take ignoring d'insu ba idan yana waje? Kokuwa tsabar jan ajinne oho?. Har Lokacin daya fito wankan tana shayar dasu, ta shafa kan wannan ta shafa Na wannan, sosai suka birgeshi itada yaran, jin kamar motsi yasakani kallon wajen, da sauri na janye yaran daga bakin nono naja towel d'in na rufe abinna ina turo baki gaba. Baki ya ta6e yashiga takowa inda muke, ya rankwafo kaina ruwan fuskarsa yana d'iso min a jikina, a kasalance yace, “wane darene jemage bai ganiba malama, tunkan su sha ni........”. Da sauri na saka hannu na toshe masa baki. Zama yayi yana janye hannunna, cikin waro idanu yace, “to mikike tunanin zan fad'a? lallai kinfi k'arfina, niba can Na dosaba to”. Sosai naji kunya, na sauke yaran a kan gadon na sakko, zuciyata cikeda mamakin sa, ya d'aure fuska yana basarwa yayta sakin magana kuma kamar bashi yayiba. Ficewata nayi bayan na d'auki bathrobe d'insa na d'ora akan towel d'in jikinna. Wani kallo ya bita dashi yana ta6e baki, kafin ya maida ga yaransa daketa kalle-kalle, ya shafa kumatunsu sannan ya mik'e zuciyarsa na tunanin su Momma, addu'arsa d'aya kar wani ya sanar musu. Kasa fitar nayi saboda jin kamar da mutane a falon da zanbi ya sadani da 6angarena. Badan nasoba tilas Na dawo baya. Galadima dake gaban mirror yana shafa mai yana kallonta ta ciki, amma sai yayi biris tamkar bai gantan ba. Komawa nayi na zauna a bakin gado ina tunanin mafitar yanda zan samu kaya, da jin haushin sharenin da yayi. Ana haka mukaji knocking, saida ya kalli Computer d'in yaga Mom Ce d'auke da Abduraheem sannan ya mik'e yana amsawa.. Zuwa yay ya bud'e mata, bata shigoba ta mik'a masa yaron da har anmasa wanka Ashe, ta mik'a masa kaya a leda tace na Munaya ne. Galadima yace, “mom ya tashine?”. “ya tashi, tunma fitowarka babu dad'ewa, harma an masa wanka”. Sumbatar kumatun yaron yay yanama mom sannu Idonsa akan yaron yana kuma sumbatar goshinsa cikin lumshe idanu ya k'araso inda nake dana zuba musu idanu cikeda sha'awa. Kusa dani ya zauna ya d'ora minshi akan cinya. nima rungume kayana nayi na sumbaci goshinsa, inason bashi abinci amma inajin kunyar Galadima, gashi ya zubamin ido yak'i tashi. Lura da hakan dayay ya sakashi yin miskilin murmushi ya mik'e yabar wajen. d'an hararan bayansa nayi ina fad'in mugunta dai babu k'yau a kan la66ana..................✍🏻 “Hummm fans nasan kwace wai

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});