Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

layinba, dan dukkan family nashi basu San da zamansa ba, ita kanta mahaifiyar su Munaya batasan anyi saving number a phone nata ba, suma da suka kirata basusan da number a wayarta ba, dan baita6a kiranta da shiba, akwai matakan tsaro dake tattare da Layin, hakanne ya tabbatar min da akwai abinda yake 6oyewa a Sim card d'in, dan sai time to time yake amfani da shi, kiran matarsa da sukayi da layin wannan shine kuskuren farko da suka tafka da Sameer ya samu hanyar musu takun sauro. zan fara aiki akan layin na shigesu ta hanyar da basu zataba”. Jinjina kai kawai Nuren yakeyi dan mamaki, Galadima da banne, kamar yanda basirarsa take daban, ya sauke ajiyar zuciya yana kama hannun Galadima da idonsa ke a lumshe har yanzun, cikin karsashi yace “lallai kai RAINA KAMA ne Sameer”. Murmushi kawai Galadima yayi, amma baice uffanba. Knocking akayi, Nuren ya kalli k'ofar yana bada izinin a shigo, Sauban ya shigo da sallama, su duka idonsu a kansa, Nuren yace “lafiya kuwa?”. Zama Sauban yayi yana sauke Numfashi da k'yar, cikin magana d'ai-d'ai da alamar a birkice yake yace, “wlhy Yaya binmu aka ringayi da wata bak'ar Jeep, da k'yar mukasha wlhy, ni dai yau zanbar k'asarnan gaskiya”. Sauban ya fad'a tamkar zaiyi kuka’. Gani kawai sukai Galadima yana dariya, saida yayi mai isarsa sannan ya tsagaita. Nuren da Sauban suka tsaya kawai suna kallonsa. Tashi yayi tsaye yana takawa cikin izzar k'asaita, ya dafa bango yana lek'en waje ta window d'in office d'in, yakai wasu adadin lokuta a wajen, sai kuma ya juyo yana kallon Nuren d'in da Sauban da suma suka zuba masa idanu. “my dear brother! daka tsaya sun kamaka ai, tabbas da wannan shine kuskuren da zasuyi Wanda bazasu ta6a mantawa da waye Muhammad Sameer Saifudden ba a tarihin rayuwarsu. Waya gaya maka kana yawo cikin 9ja ne batareda idon Sameer ba a kanka?”. Sauban ya sauke ajiyar zuciya yana share gumin daya jik'a fuskarsa, “wlhy yaa Sam daka fad'amin da bazan tsorata ba”. Daga Galadima har Nuren dariya suka kwashe da shi, Nuren ya dafa kafad'ar Sauban yana fad'in “matsoracin banza”. “uhm-uhm yaa Nuren bazaka ganeba wlhy, tsoro halak ne fa”.. Galadima dai baice komaiba ya koma ya zauna yana murmushi. ★)))*(((★)))*(((★)))*(((★)))*(((★ Ganin har anyi sallar Magriba babu baba k'arami balle Dady ya saka Innaro d'aukar gyale ta fito, lokacin gwaggo Safiyya tana salla, shiyyasa batasan innaro ta fitaba, habiba da Naja'atu dake tsakar gida suna tattare kaya saboda hadari na farkon damina dayake nuna alamar zai zubda ruwa. suka kalli juna, Naja'atu tace “yaya habiba tsohuwarnan fa bata da dama wlhy”. Dariya habiba tayi, “ai kad'anma kika gani Naja'atu, yanzu dai zataje ta tadama baiwar ALLAH hankali”. “to ALLAH ya k'yauta”. ‘cewar Naja'atu tana rik'e ha6a’. Lokacin da Innaro ta shigo gidan d'akin Innarsu Munaya ta nufa kai tsaye, sai dai ta iskeshi rufe, kwala kiran sunanta ta shigayi cikin masifa, “Ai'sha!! Ai'sha!! Nasan kina jina, wlhy ki fito kafin yau d'innan igiyar aurenki ta tsinke”. Mamansu yaa Hameed da gwaggon Haleematu ne suka fito, mamansu yaa hameed tace “aiko tafita fa inna, dan gab da magribar nan naga Fadeel ya shigo sun fita, bansan mike faruwa ba dai”. “yaza'ayi kusan mike faruwa tunda anyi k'ulle-k'ullen munafunci, lallai jafaru, wai yau da kaine za'a muzantani hannun mak'iyana, to nikuma naga ta yanda Ai'sha zataje wata k'asa jiyyar Auwalu da raina”........ haka taita zuba banbamin masifa matan gida na saurarenta, daga daddy har baba k'arami suna gidan amma sukak'i fitowa. Jarabar Innaro ta saka kowa na gidan fahimtar mi ake ciki, nanfa hassada da bak'in ciki suka kume zukatansu, dukda kuwa sunsan tafiyar bata dad'i baceba, maman fauziyyace kawai hakan yamata dad'i, koba komai inna ta huta da cin zarafin Innaro koyayane. Sai da Gwaggo Safiyya ta shigo tama Innaro magana sannan ta tafi gida, su matan gidanma sai yanzu suka San da zuwa gwaggo Safiyya d'in. Amma sunso ace innarsu munaya na gida Innaro tayi wannan rashin mutuncin. Hummm😕. **************************** Bayan fitowar su Galadima daga birnin gayu, sun wuce gidane, Nuren kuma yakoma hotel d'in daya sauka. Galadima kawai ne ya shiga sashensu, amma Sauban 6angaren mai martaba ya nufa neman yarima Mahfuz. Munaya na zaune a falon farko tareda sabbin kuyanginta guda uku, (dan bata amince su shiga falonta ba, saita gama tantance su sannan) ba wani hira sukeyiba, d'ayace a cikinsu ke sak'a shine abin ya birge Munaya take kallo, tana kwance cikin doguwar kujera ne, yayinda su kuma su ke zaune a k'asan lallausan carpet d'in falon. Dogarai biyune suka fara shigowa hannunsu d'auke da ledoji, sai kuma mai gayya mai aiki Galadima. Da sauri bayin suka mik'e tsaye, saida ya ida shigowa sannan suka d'urk'ushe a k'asa suna kwasar gaisuwa. A la66ansa ya amsa yana d'aga musu hannu, yayinda idanunsa ke kan munaya da itama ke satar kallonsa Duk d'insu kowa janyewa yayi, yayinda bayin da dogaran suka fice bayan sunkai ledojin falon Galadima. Baice da ita uffanba yafara takawa zai shige, tamkar mai tsoron fad'a tace, “sannu da zuwa”. Ysayawa yayi cak, sannan ya juyo da kansa tamkar mai ciwon wuya ya kalleta, bata yarda sun kuma had'a idoba takuma fad'in “nagode sosai”. “for what?”. ‘ya fad'a cikin isa’. Shiru munaya tayi, ta kasa cewa komai. Shima bai sake cewa komai ba ya taka ya shige abinsa. Harara munaya ta raka bayansa da shi, sai kuma ta sauke numfashi tana tashi itama, bedroom d'inta ta koma, a saman sofa ta zauna tana dafe kai, sosai take buk'atar zuwa sake duba mahaifinta, amma ta kula Galadima bashida niyyar cemata taje, kai itako wannan wane irin abune haka? shi dama gidan Sarautar haka yake bakada 'yancin kanka?, komai saida k'a'ida. tun d'azu kuma take kiran number inna bata d'agaba, tadai kira baba k'arami da daddy sun gaisa ta tambayi jikin Abba, shine ma har suke kuma sanar mata k'ok'arin da galadiman keyi. tabbas hakan da yayi yasata jin farin ciki, koba komai tasan shi adaline, ko anan gaba ragamar shugabanci ta riskesa zaiyima na k'asa da shi adalci. Galadima daya shiga tun a falo yafara k'ok'arin cire navy blue d'in jacket d'insa, ya wullata saman kujera, sassauta belt d'in yayi shima amma bai cireba, ya zauna cikin tsantsar nuna gajiya yana furzo iskar bakinsa, remote ya d'auka ya kunna tv, tamkar ya saita lokaci saiga hoton d'iyar minister mai amsa sunan Farhat ana nunawa, an saka 2.5 millions ga dukkan wanda ya kawota koya bada bayanan sirri akan wanda yasan wani Abu akan 6atanta. Wani mugun tsaki Galadima yaja a zuciyarsa yana fad'in wawaye, saiku k'ara yakai 100millions ba 2 ba, idan ubanta ya shirya kawo kansa gareni nima a shirye nake nabashi shashashar 'yarsa mai zubin ta6arya, ya kashe TV d'in kawai ya mik'e ya shige ciki. Ko ina fes da shi, yasan baida Matsala da Sauban a 6angaren tsafta dama. kayan jikinsa ya ida cirewa ya shiga wanka. Bayan ya fito samu yay yad'an kwanta, dan ya samu Hutu kona 2hours ne, dan yanzu akayi sallar zuhur. aiko kwanciyarsa babu dad'ewa barci yay gaba dashi. Munaya ta jawo wayarta da nufin kuma kiran inna, amma sai taga Ashe credit d'inta yama k'are, kanta ta dafe dan haushi, zuwa can tamik'e

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});