Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

“niba haka nake nufiba fa”. “mikike nufi to?”. ‘yay maganar yana janye hannunsa daga cikin nawa’. Fuska nad'an ya mutse, cikin salon yanga nace, “ina nufin ALLAH yabaka nasibin sarrafa Computer's ”. Yanda nayi maganar cikin salo saiya sakashi murmusawa yana ta6e baki, “toni miye namin yanga yalla6iya? saikace kina tare da masoyinki?”. Haushi ya kamani Na dalla masa harara. Bai kulaniba ya mik'e yana fad'in, “masu cikifa saida uzuri”. Harna yunk'ura zan mik'e yace, “oh haushi kikaji? to sorry zauna kiga wani abu”. Komawa nayi Na zauna INA k'unk'uni. Hotunane da yawa ya nunomin daga cikin Computer, ya danna hoton farko ya fito sosai. Batareda ya kalleni ba yace, “wannan sunansa *Kabiru Ibrahim*, nasanshi shekaru kusan 9 da suka shige a dalilin neman bayanan sirrina tacikin Computer, nabashi dama yashiga sosai saboda a time d'in yaci k'arfina, inada yak'inin wanine yabashi wani yanki sirri daga abinda nake da shi, ganin ya zuk'i bayanai 90 a cikin 100, saina tura masa goman gaba d'aya, saida ya zamana 99 duk sun shige ga Computers d'insa sannan Na nuna masa banbancina da shi, Na lalata abinda yake da shi da Wanda ya samu agareni, tundaga wannan ranar kuma nafara bibiyar rayuwarsa. Abin mamaki saina gano yanada Ubangida, shine wannan, *Timothy yoha*, dukkan abinda ya aikata agareni Umarnin uban gidansane Timothy, Na maida akalar tunanina ga Timo, saina iske shima aiki yakema wani, ba kowa bane face tsohon shugaban k'asarmu *Labaran Ahmad kachia*. shine wannan, nasan kuma k'ila kisansa dukda dai lokacin dayayi shugabanci bana tunanin an haifeki ma gaskiya, ta silar *Former p... Labaran Ahmad Kachia* nasamu wani kundin bayanai akan tsantsar abotar dake tsakaninsu su a k'alla 15, babu maijin sirrinsu saboda Kansu a matuk'ar had'e yake, ALLAH yayima 4 daga cikinsu rasuwa shekarun baya kad'an, saisu 11 suka rage”. Ya kumayin wasu 'yan danne-danne nidai duk ina kallonsa da mamaki, hotunan mutane 15 suka bayyana, sai dai an lik'e fuskar mutum 4 alamun wad'anda suka mutu kenan. Gaban frigate d'in d'akin yaje ya had'a Coffee a mug, sannan ya tako zuwa gareni ya mik'amin, kaina Na girgiza masa alamar a'a, ya d'aga kafad'a sannan ya juya zuwaga Computers d'insa. “wannan mutane hud'un sune jiga-jigan wannan abota, d'aya ya rasu a cikinsu saura uku, *Josaya Bamma* shine mataimakin *Alhaji Lawan tanderu*, bayan mutuwar tanderu shugabancin wannan abota ya dawo hannunsa, dukkan wani shigi da fici na man fetur dake faruwa a Nigeria josaya Bamma yasanta, dan sune masu yinsa, yanda ake fita da mai a k'asar da yanda suka mallaki rijiyoyin mai ba bisa k'a ida ba, gwamnati kuma batada damar magana domin sune masu fad'a aji, sune tsoffin shugabanni da suka San dukkan sirrin k'asar, sai *Bana baba gana*, dukkan wasu magunguna dake shiga Nigeria saida saka hannunsu, akwai wad'anda batareda k'a idaba suke kaita shi da *Alhaji balala* da *William Solomon*, domin manyan likitocine masana sosai, *Hajia A'i Barnawa*, babbar d'iya ga tsohon soja *Garba mai dala sokoto*, tashiga wannan group d'in sanadin k'awarta *Victoria*, dukkan wani cin zarafi mata ko cin dunduniya suke saka ido, kullum suna ik'irarin sune masu Kare hak'in mata a zahiri, amma a bad'ini ba aikin da sukeba kenan, suna aikin gyara aljihunansu ne. wannan shine *Mansur Habibu Abu*, wannan kuma *Abdul-Naseer Nafi'u*, da *Miracle Asun*, wad'annan dukkansu manyan 'yan kasuwa ne, amma a bayyane, amma a 6oye su sukasan tsiyatakun dasuke shiryawa a k'ark'ashin k'asa *Sagir sulaiman Sulaiman* minister mai mulki a yanzu, sai wannan da wannan duk sun mutu banida matsala a yanzu tsakanina dasu, Munaya inason sanin alak'arsu da Mahaifina, wad'annan mutanen, domin sune mahaifina yay zama dasu ana gobe wannan ciwon zai sameshi, a daren ranar kuma Abie yashiga wajen mama Fulani domin gaisheta, jakadiya data masa rakkiya ta tabbatarmin da lallai yafito ransa a 6ace daga wajenta. Sannan a wannan ranar matarsa ta uku ce ta kawana a turakarsa, alhalin kuma kwannan matarsa ta biyuce, amma saboda kud'in data bama jakadiya da dad'in bakinta saita kaita turakar Abie a wannan daren, takuma sanarma matarsa ta biyu cewa takawa bashida lafiya yana fama da mura. kwana biyu kuma kafin faruwar dukkan wad'annan abubuwan Abie yayi zama Na musamman da Hakimansa saboda kama Wazirinsa da yayi Dacin amanar Masarauta wajen d'aukar sirrin cikinta ya bama wasu bak'in turawa da ba'asan dalilinsu na yin hakanba, a bincikena d'aya a cikin turawan ya Mutu, amma d'ayan yana nan da ransa. Abie ya kwanta jiyya da sati biyu aka kashe babban malaminsa, limamin masallacin sarki maikuma bama Abie shawara akan addini. dukkan wad'annan dana ambata miki sunayensu a kwai hotunansu anan d'akin, akwai abokin mahaifinki da kika fad'amin, shine Alhaji Mamman k'afur Wannan babban yaron Alhaji Lawan tanderu ne, dan wannan group sunema suka tsaya masa ya fito takarar shugaban k'asa, babbar matarsa k'anwar matar tanderu ce, wadda a gidan tanderun ta taso tun tana k'arama. Senetor halluru garba abokin Alhaji Mamman k'afur Ne sosai, akwai wani 6oyayyen sirrin dake tsakaninsu kuma, sai dai ban saniba ko Abbanki yasan wani Abu a ciki. Idan nace zan cigaba damiki bayanin sirrikan dake cikin d'akinnan kanki bazai iya d'auka ba Munaya, amma nabaki damar kimin kowace tambaya ni kuma zan baki amsarta batareda shamakiba”. Ajiyar zuciya Na sauke, Dan tabbasa kaina bazai iya d'aukar wannan bayanan nashiba inhar suka wuce zurfin haka, Na yink'ura zan mik'e, saiya matso ya taimaka min da kansa, zaman silifas d'ina Na gyara a k'afata, sannan Na taka ga wasu hotuna, hotona na nuna masa dana muftahu, yad'an murmusa yana ta6e baki, kafin ya ajiye cofin hannunsa ya hard'e hannayensa a k'irji, “Ba manufar wannan hoton ke d'inba, dan haka manta da wannan kawai, sai nan gaba watak'il zaki iya sanin wani abu”. Zanyi magana ya girgizamin kansa, alamar karnace komai. Idona na janye daga garesa kawai, na maida kan hoton Muftahu tareda nunashi da yatsa. Takowa yay har inda nake, ya kama hoton yana kallo tamkar yau ya fara saninsa, “Muftahu d'an uwa nane, kuma abokina, sai dai bakomai ne nake sakin jiki da Shiba, domin lokacin muna yara mutumne shi mai yawan k'arya, hakanne yasaka ko yaushe muke fad'a, babu abinda na tsana ga hallayar d'an Adam irin k'arya dacin amana, wannan halayyar tasa saita gaza barin zuciyata har girmanmu, kullum kallonsa nake bai canjaba, wannan yasakani fin yarda da harun fiye dashi, saikuma yake gwadamin wasu halaye na rashin gaskiya a lokuta da dama, ban k'ara tsinkewa da lamarinsa ba sai a time d'in da abinnan yafaru tsakanina da ke a birnin gayu, Muftahu shine Wanda yakawomin shawarar mizai hana na aureki ko ta wannan hanyar zansan wani Abu, da farko na d'ana masa tarkone, na yarda da auranki na shekara d'aya, yanda yacigaba da rawar jiki sai lamarinsa yacigaba da tsoratani, randa ya saka mana pill's a fresh milk daga ranar na yarda 100% shi maicin dunduniya tane, kuma akwai wani 6oyayyan al'amarin da yake son cimma buri, wannan yasakani kauda idanu a kansa, nabashi dukkan dama, dukda kullum Harun kan nusar dani illar hakan, amma na share komai tamkar bana gani, sai dai wannan zuwan danayi maganar da kika ta6amin a wani dare ya sakani cikin dogon nazari, daga time d'in kuma na saka idanuna akan Muftahu da Harun, zuwannan da nayi na k'arshe Nigeria, naga

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});