Chapter 82
Chapter 82
iri d'ayace ga kowanne launin halitta na mutum ko aljan ko dabba, Dan mukan tainci kanmune akusan mizani d'aya, dukda ubangiji ya banbantamu ta halitta da ayyuka da tunani ko nace kaifin basira, ko'a jinsi launi biyune, akwai namiji akwai mace, dukkan rayuwa takan farane da mafari yalla6ai” na d'ago ina sake mik'a masa mug d'in tea d'in again, a mamakina a yanzu saiya kar6a, na lashi lips d'ina na k'asa ina gyara zama sosai da maida hankalina wajen juya kunun dana zuba a cup da tsokali, cikin nisawa nacigaba da fad'in, “mafarin rayuwa shine dasuwar bawa a cikin mahaifiya, mukanyi wannan rayuwarne a cikin halin su wanene mu? daga nan sai matakin haihuwa, shigowa duniya a bisa bigiren wane ahali muka kasance, dukkan ahalin daka Sani sunada matsalarsu, saidai tawasu tafi tawasu zafi, daga ranka ka iso filin gwagwarmaya wato duniya, shikenan littafinka dayazama rubutacce tun a cikin mahaifiya saiya fara aiki, mala'iku masu kula da fitar numfashi su dasa alk'alaminsu, masu kula da abinci suma haka, masu kula da ruwa ma haka, masu kula da magana ma haka, masu kula da kallo ma haka, masu kula da ji ma haka, masu kula da duk wani motsinka ma haka, tafiya, zama, kwanciya dadai sauransu, kowa ana haihuwarsa tsaftatatccene, iyaye suke fara juya akalar rayuwa, walau mai k'yau ko sa6aninta, (kaga kenan akwai hisabi tsakanin iyaye da y'ay'a ma kenan?) daga nan rayuwa zata cigaba da yad'o kamar d'an duma, tun ana maka, harka koma koya, harka fara iyawa da kanka, harma ka kware ka koyama wani, (wanne ka iya? ko ka koya? yarage ruwanka) duk Wanda kaga an masa a farko to tabbas za'a k'ara masa a k'arshe, kodai silar tsufa, ko ciwo, kokuma iftila'in rayuwa, kokuma na k'arshe shine hidimar gawarka, a dukkanin dunk'ulalliyar rayuwar da kowanne bawa yakanyi zakaga cike take da k'alubale masu zuwa da zafi kala-kala, yalla6ai kasan mike taushe wannan rad'ad'in zafin kuwa?”. nayi maganar ina d'ago ido na kallesa. A mamakina sainaga ya girgiza min kansa. na murmusa ina janye idona daga kansa na maida ga kofin tea d'in ina masa alamar yasha mana. Yamutse fuska yay irin kalar tausayinnan. Nima sainayi kwal-kwal da ido kamar zanyi kuka, na had'e hannayena waje d'aya alamar rok'o🙏🏼.. Lips d'insa yad'an ciza kafin yafara shan tea d'in. Nayi salute nashi ina masa jinjina👍🏻. Basarwa yayi, nima saina kad'a ido ina tunzura baki gaba, sannan nacigaba da fad'in, “Abinda ke taushe wannan rad'ad'in zafin shine *_HAK'URI_*. hak'uri muhimmun sinadarine dake jagorantar garkuwar jiki ta kowacce launin halittar jiki na d'an Adam, walau a fili take ko a 6oye take, saidai babban makarinsa da taskar adanashi shine *_ZUCIYA!_* a duk lokacinda k'arfin zuciya ya raunana to zaka samu madarar hak'uri ta salwanta, idan zafi yanata yawa babu wannan hak'urin bugu d'aya take duk wani ma'adani na cikinta saiya tarwatse, saikaga an rasa ayyukan jiki dana ruhi, shikenan wane yazama labari. daga lokacin da rad'ad'in fitar rai ya kusanci bawa dukkan mala'ikunan da suka kasance tare dakai a randa kazo duniya saisu fara janyewa daga gareka, wani bawan kafin ranar mutuwarsa zakaga ya daina cin abinci, hakan na nufin mala'ikan dake kula da abinci ka yagama aikinsa, domin ya zagaye duniya kaf duk yawan abincin dake cikin ta babu rabonka koda kwayan gero ne, ka gama cinyewa, wani kafin ranar Mutuwa ya daina shan ruwa, aikin mala'ikan dake kula da ruwa shanka yagama k'arewa kenan, duk yawan koramu da tafkuna na duniya bakada sauran rabo na ruwa, ka shanye naka, wani kafin Mutuwa ya daina magana, mala'ikan dake kula da furucinka yagama aikinsa, babu sauran wata kalma data rage harshenka ya furta, wani kafin Mutuwa ya daina ji, mala'ikan dake kula da jinsa ya gama aikinsa, babu wata kalma data rage kunnensa zaiji, wani kafin Mutuwa ya daina gani, mala'ikan dake kula da ganinsa ya gama aikinsa, kwayar idonsa bazata sake kallon wani abuba, wani kafin Mutuwa ya daina tafiya, mala'ikan dake kula da tafiyarsa ya gama aikinsa, haka-haka wad'annan mala'ikun zasuyita ja baya suma barinka, har yarage sai mai kula da fitar numfashi kawai, daga ranar da UBANGIJI yace yana buk'atar ganinka shikenan takuma k'are, sai rundinar mala'iku su had'u su takewa kwamandan mala'ikan d'aukar rai baya, idan kai mutumin kirkine fararen mala'ikune, idan na banzane mala'iku masu azaba zasu take masa baya, sauran al'amari kuma sai Wanda ya haliccemu yasan ya zata kasance😭. zakasha mamaki idanfa nace maka duk wannan zafin k'aramin zafine acikin kashi-kashin na abinda ya shafi haluttu, shi wannan zafin ana kiransa zafin na za6in kai, kokuma zafi na a haka tsarin yazo, ma'ana kaine ka had'ama kanka wannan zafin, kokuma wanine ya had'a makashi. Abu na biyu shine zafi na rad'ad'in Mutuwa, dolene kowa saiya d'an d'anashi, walau kafiri ko Musulmi, saidai akwai banbance-banbance na awanne tsari ka koma ga ALLAH, ba wannan zafinne kawai ke jiran d'an Adam ba, akwai zafin na *_BARZAHU_* shi ake kira kwanciyar kabari, mika tanada, mi zaka tarar shine abin tambayar, wannan kam ALLAH ne mafi sanin wad'anda zasu d'and'ana wannan zafin (ALLAH ka datar damu😭)”. Akan la66a Galadima ya amsa da amin, Munaya ta share hawayenta, ta cigaba da fad'in sai zafi mai gaba d'aya, shine na makoma, *_WUTA KO ALJANNA_*, yalla6ai wad'annan jimullar zafin ga d'an Adam tilas ne, na cikin rayuwa shine zafin da zaka iya controlling nashi ta hanyar hak'uri, to Ashe bai kamata ka tasirantar da wannan zafin ya cigaba da k'onaka ba, musamman idan zakayi dubi dawasu ni'imomin da ALLAH yamaka a cikin wannan zafin, ka kasance mai yawan hak'uri saikaga kanka cikin masu yawan riba, wlhy ta wannan hanyarne kawai zaka zama mai *_NASARA_* akan mak'iya ni..........”. Maganata ta katse saboda knocking d'in k'ofar da akayi, kallon juna mukayi ni da shi, yay wani luuu da idanunsa ya lumshesu, hakanne ya sakani bada izinin shigowa kawai batare da na jira amsa daga garesa ba. Sarkin k'ofane ya shigo, ya zube yana gaishe mu, nice kawai na amsa, boss kam hannu kawai ya iya d'aga masa, yay mana ya jiki again, nanma nice nakuma amsa shi, cikeda girmamawa yace, “ranki ya dad'e yalla6ai harun ne ke buk'atar iso”. Saida gabana ya fad'i, na had'iye wani yawu mai kauri ina kallon galadima dayay biris damu yanata shafa kan d'ansa, bud'e idonsa jajaye yayi akan Sarkin k'ofa, ya jinjina masa kai alamar ya shigo dashi. Kallonsa nayi tamkar zanyi magana saikuma nai shiru, a raina ina mamakin wannan munafukin dami yazo kuma?..... ban kai k'arshen zancen zucin ba Harun yay sallama, nid'ince dai na amsa cikin danne zuciya da fushina. Ya zauna fuskarsa d'auke da murmushi. Nima saina saki tawa ina fad'in, “barka da hantsi ranka ya dad'e”. “Barka dai gimbiyarmu, ya jikin ki dana yalla6ai?”. Na kalli Galadima dayay shiru kansan jingine da kujera ido a rufe, “da sauk'i”, na fad'a ina mik'ewa na koma saman kujera, dan bazan ta6a barin falonba sainaji uwarmi ya kawosa. Ya amsa da “masha ALLAH, ALLAH ya kiyaye gaba ya k'ara lafiya”. “humm” na fad'a ina amsawa da “Amin dai”. Hankalinsa ya maida ga Galadima, “Sameer ya jikin?”. Bud'e idonsa yayi shima, ya ajiye mug d'in hannunsa a teble d'in dake gefen damarsa, batare da yace uffanba ya sauke ajiyar zuciya yana taunar lips. Banga alamar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92