Chapter 39
Chapter 39
ruwa. Sauka nayi daga gadon dan zazzza6inna ya fara hucewa nima, freight na bud'e na d'akko masa ruwa, na had'o da Kofi, zama nayi kusa dashi a gefen gadon na tsiyaya ruwan a Kofi na mik'a masa. kar6a yayi ya shanye, ya mik'o min kofin, zan kar6a ya girgiza min kai tare da min nuni da in k'ara masa. Kuma tsiyaya masa nayi, yakai rabi ya d'aga min hannu alamar ya Isa, bayan yakuma shanyewa ya mik'a min kofin yana fad'in “Thanks”. Kar6ar kofin nayi, ba tareda na tashiba nace “Yalla6ai lafiya kuwa”.. “Mafarki”. ‘yafad'a yana komawa ya kwanta’. Idanu kawai Na zuba masa, kusan 4minutes ya juyo da kansa ya kalleni, “kizo ki kwanta mana”. K'aramar ajiyar zuciya kawai Na sauke Na mik'e, Na d'ora ruwan da Kofi a dirowan gefen gadon na koma inda nake na kwanta. Ganin ya sauya hannun da yay mafarkin kuma yana addu'a sai ban sake cewa komaiba, na kwanta shiru ina sak'e-sak'e a raina mafarkin mi yayi to? da har yasakashi firgita irin haka?. banida mai bani amsa dan haka nayi shiru. Saiya zamto da asuba na rigashi tashi, harma saida nayi alwala sannan na tadashi, da k'yar ya iya tashi yana dafe kai, binsa nayi da kallo kawai harya shige toilet. Lokacin daya fito na fara salla, dan haka saiya fice kawai. A mamakinsa saiya iske Aiyaan da Aryaan sun tashi suna alwala, hakan ya Burgesa sosai. Sai kawai ya kama hannunsu suka tafi massalaci. Bayan an idar da salla bai yarda sun had'u da Sarki ba, ya gudo. Sai dai abinda bai saniba shi Sarki ya gansa, dan yau ya makara salla shima. Wajen Around 9am nagama gyaran d'aki nayi wanka, saina d'an fito falon domin duba dubawa, natarar sabbin kuyangina suma komai sun gyarashi k'al, harma da mana break fast, banyi yunk'urin bud'ewa ba ma balle tunanin son ci, dukda kuwa natashi da yunwa, to amma Momma ta gargad'eni sosai akan cin abinci wani a masarautar, dan haka na fito daga kitchen d'in kawai. Tunkan na shigo nake jiyo maganarsu Aryaan, zaune na iske Galadima su Aiyaan na kusa dashi suna bashi labari, anmusu wanka tsaf, sunsha sabbin kaya iri d'aya. Har yanzu Galadima bayada walwala, na zauna ina gaisheshi, batareda yabar latsa wayarba ya amsa min, su Aiyaan suka dawo kusa dani suna gaisheni, kumatunsu naja ina murmushi, “oh my guys kunsha k'yau, waya muku wanka haka?”.. Atare suka amsa min da fad'in “Uncle ne, kuma ya saka mana tirare yanda kuke mana”. Murmushi nayi, na saci kallon Galadima da yay biris damu kamar baya d'akin, alhalin sanda na shigo na iske suna hira shidasu 'yan 2. Sallamar da wata baiwa keta kwad'awa na amsa, sannan na mik'e na fita dannaji minene? A k'ofar falona na isketa, nace, “miya farune?”. Duk'ewa tayi ta gaisheni, sannan ta mik'omin ledojin hannunta tana sanarmin Sarkin motane yace “na kawo wannan ranki ya dad'e”. Kar6a nayi, na koma ciki. Ajiye ledojin nayi a gabansa, “gashi wai inji sarkin mota”. Idanunsa ya d'ago ya kalleni, yace, “breakfast d'inku ne”. Tashi yay ya fita yana fad'in na shirya zaije ya dawo mu shiga cikin gida gaida mutane. Na amsa masa da to. ___________________ Tun a daren jiya wasu bayi sukaga Muftahu, dan haka suka shiga ihu, dandanan sauran bayin dake kusa da wajan suka firfito, manyan bayin cikinsu ne suka kai maganar cikin gida, shine akasakasu d'aukar Muftahu su shiga dashi. Lamarin yabama kowa mamaki, babu wani mummunan rauni a jikinsa, inbanda d'an jini dake gefen bakinsa, saidai sun sami kwanciyar hankali ganin yana numfashi. Maganar dawowar Muftahu bata baje masarautar ba sai washe gari. Bayan Galadima ya fito daga sashensa zaije fada yaji anata k'ananun magana akan dawowar Muftahu, saidai kuma miskilancinsa bai barsa ya tambayi kowaba ya nufi Fada. Ya isa mai martaba baikai ga isowa ba, dan haka suka gaisa da 'yan majilissar Sarki dake fadar, sannan ya nemi mazauninsa dake gefen Sarki Na dama ya zauna. Zamansa baifi da mintuna 10 ba Mai martaba ya iso, gaba d'aya suka mik'e tsaye, dogaran Sarki sunata kirari da fad'in gyara kintsi da k'yau, duksun baza riguna ba'a gani mai martaba, basu bar kowa ya gansa ba har saida ya zauna a kujerarsa. Baya suka mammatsa mai martaba ya bayyana, atare su Galadima suka rissinar dakai alamun girmamawa, sannan kowa yafito tsakkiyar fada ya mik'a gaisuwarsa ga Sarki, yayinda fadawa ke faman amsawa, tsakanin Sarki dasu kuwa shine d'aga hannu. Mai martaba yayi mamakin ganin Galadima yau azaman fada, bawai baya zaman bane, sai dai yakan dad'e bai zaunaba, an masa uzurine kasancewar ansan ba zaune yake dindin dinba, kuma idan yazo akwai harkokinsa Na kasuwanci da yakeyi, sai dai dolene yakan shigo yayi gaisuwa. Bayan fada ta nutsu aka fara fadanci. K'a idane fadar gagara badau takanyi fadancine a sati sau hud'u kawai, litinin ba'a zaman fada, domin ranace da ake tunawa da abinda ya faru ga tsohon Sarki mahaifin Galadima, talata, laraba, alhamis, asabar, sune ranakun da ake fadanci, ranar juma'a ma ba'ayi saboda muhimmancin ranar ga al'ummar musulmi. A wad'annan ranakun akanyi zamanne daga 10am zuwa 12:30pm, da an tafi sallar zuhur ba'a dawowa, idan kaga anwuce wannan time d'in a fada to tabbas akwai abinda ya farune. A wannan zaman fadancine maganar dawowar Muftahu ta fito, sun tattauna akai harda shirin kuma d'aukar matakai Na tsaro a masarautar. Bayan anyi sallar zuhur ne Sarki ya shige gida, sauran fadawa ma kowa ya kama gabansa, Galadima bai shiga gidaba saiya nufi sashen su Muftahu domin dubashi. Bayan an masa iso ya shiga, ya iske mahaifiyar Muftahu da 'yan uwansa zagaye dashi, har yanzu kuma yana cikin yanayin barci. Ya jajanta musu, Yakuma kwantarma da mamansu Muftahu hankali, kusan mintunsa talatin ya fito ya koma sashensa. Ya iske su Aiyaan kawai a falon Munaya suna kallo, suka taso da gudunsu suka rungumesa, fuskarsa cikeda fara'a ya tarbesu, ya tambayesu ina Auntynsu?. A tare suka bashi amsa, “Uncle tana d'aki ta kwanta kuma tace karmu tadata, inba hakaba jiki magayi”. Murmushi yayi yaja kumatunsu, “kuce zatayi zana kenan idan aka tada ita?”. Nanma atare suka amsa da “eh Uncle, kasanfa Aunty Munaya tacika fad'a, gidanmu tsoron masifarta akeyi, amma ita Aunty Munubiya babu ruwanta”. Galadima yace, “da gaske?”. “ALLAH kuwa Uncle, idanfa mukayi rashinji ita ke zanemu ba innarmu ba, kuma dukanta da zafi, gashi taita hararmu da katun-k'atun idanunta nan”. Sosai abin yabama galadima dariya, dan haka ya dara sosai abinsa yana fad'in, “kubari tajiku to, idan ta zaneku babu ruwana nidai, kunga bara naje naga kota tashi, karfa Ku shigo, dan zata iya zaneku”. Sukace “ai bazamu shigoba Uncle”. Yace, “good boys”. Da sallama ya shigo, amma saiya isketa baje a gado tana shak'ar barcinta, yad'an murmusa kafin ya k'arasa ya zauna a bakin gadon saitin fuskarta, yatsunsa biyu yasaka a gefen wuyanta dan yasan da wahala wannan barcin ya kasance na lafiya, aikam jikinta ringim yake da zazza6i, tausayinta ya kamashi, lallai uwa dabance acikin al'umma, Ashe haka sukeshan wala, tundaga d'aukar cikinma zuwa rainonsa, akoma rainon yaro, daganan tarbiyarsa, lallai masu raina mata ko kallonsu masu k'arancin tunani sune masu k'arancin tunanin ai, ya d'an lumshe idanunsa yana cije lips, ganin ta dunk'ule a waje d'aya saiya ja bargo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92