Chapter 85
Chapter 85
lafiyarsu. ★★★★★★ Tunda Harun ya fita saiya kira wata Number lokacin daya k'arasa d'akinsa, dukkan abinda ya faru ya labarta mata, daga can tace k'aryane bahaka akaiba, ita an sanar mata lallai da Galadima aka kar6o yaran, babu wasu police, amma itafa kamar tafara saka alamar tambaya akan wannan ficikar matar tasa. Harun yace, “haba dai, wannan y'ar yarinyar mizata iya, akwai dai abinda bamu saniba, yanzu dai kibari zamuyi maganar daga baya, zand'an bincika yarannan danni na lurama kamar ba wad'anda muka saka bane sukayi aikinnan?”. “sunefa gaskiya, abinda dai na lura dashi sun had'a aikin da wasune, shiyyasa suke 6oye mana Kansu, tunda kaga mudai baiwarnan bamu muka sakata ba, amma shi namijin yana cikinsu, nasan sunyi luff ne sai k'ura ta natsa su fito”. “ok shikenan to, zandai sake bincikawa, dan Sameer yanada wayo, shiyyasa naso bugar cikinsa akan batun, amma wannan shegen k'asaitar tasa ta rainin hankali ya hanashi tankamin, sai matarce ke bani amsa”.. “karka damu zamu sauke masa shine ai”...............✍🏻 🤣abin dariya, ku a naku zaton yaranku sun 6oye Kansu be?, to suna hannun Galadima, lafiya kawai muke jira ya samu ya yagalgalasu kuma ya cafkoku munafukai🙄😏. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*😭🙏🏼 [7/18, 2:19 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻2⃣9⃣ ..............Harmun kwanta zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason naje naga halin da yake ciki, Dan koda su Nuren suka wuce ban komaba, sakkowa nai daga kan gadon, laraba dake a tsakar d'akin kan katifa tace, “ranki ya dad'e lafiya kuwa?”. Banason ta kalli abun da wata manufa, dan haka nad'an murmusa, “uhmm iya inason duba Abbansu ne, ban saniba koyasha maganinsa kafin ya kwanta”. “eh lallai hakan yanada k'yau, badan ma jego ba ai bai kamata ya kwana shi d'ayaba”. “aiba shi kad'ai baneba iya, Sauban ne zai tare dashi ”. A to hakan yayi. Bance komaiba Na kar6i gyale wajen Samha Na saka na fita. Masarautar tayi tsit, da alama kowa yasamu nutsuwa a sashensa, ban tsaya knocking ba na shige kawai, a falo na iske Sauban zaune yana kallon ball, cikin tsokanar da ya iya yace, aunty gimbiya kin kasa barcine?”. Nayi murmushi, “yaa Sauban matarka taga ta kanta wlhy”. Dariya yayi kawai, nikuma na wuce abina. Saida nayi sallama kusan uku banji an amsaba, saina shige kawai. Zaune na iskeshi a bakin gado ya jingina da fuskar gado, hannunsa d'auke da Qur'an yana karatu a hankali, idonsa cikin medical glasses, gakuma system a gefe itama a kunne. naji dad'in yanda na sameshi, Addu'a da karatun Qur'an babban jigone dake wanke zuciya da damuwar d'an Adam (duk lokacin da ranki ya 6aci d'auki Qur'an ki karanta koki saurara, wlhy zakuji sassauci mai yawa). Har zan juya na fita sai naji yay gyaran murya, juyowa nayi na kallesa, har yanzu dai karatunsa ya keyi. na dawo na zauna a bakin gadon ta d'ayan gefen, shikuma ya cigaba da karatunsa, kusan mintuna 6 kafin ya rufe Qur'an d'in ya ajiye, ya cire medical glasses d'insa shima ya ajiye yana kallona, ko kad'an fuskarnan babu walwala, nuni yamin da inzo. Ban musaba na tashi nadawo 6angaren inda yake, zama nai d'an nesa dashi kad'an. Ya lashe le6ensa da cizarsa kad'an yana hard'e hannayensa a k'irji. Muryata can k'asan mak'oshi nace, “yaya jikin?”. Kansa kawai ya jinjina min cikin lumshe ido, sannan ya motsa baki kamar zaiyi magana saikuma yay shiru, saida yaja wasu seconds sannan yace, “Munaya!?”. “Na'am”. Na amsa ina kallonsa da janye idon lokaci d'aya saboda ya tsareni da nasa. Huci yad'an furzar, ya cire hannayensa daga k'irji yana gyara zama, “Nayi nazaci sosai akan maganganun ki na d'azun, nakuma fassarasu aji-aji, na fahimcesu a yanda tawa fahimtar take, so a wannan karon rok'o nake miki na k'arshe akan ki fad'amin abinda kika sani, ni d'an Adam ne, ban isa cewa komai na sanshi a rayuwaba ko na iyashi, sai abinda Ubangiji yaso in sani kawai, Munaya ada ba haka rayuwata takeba, mutumne ni mai yawan raha dason nishad'i, amma daga lokacinda nafara sanin kaina da matsalar mahaifina sai komaina ya canja, nazama mutum mai yawan rashinson magana, nafison kullum na kasance ni kad'ai a kuma ke6antaccen waje” yay murmushin takaici sannan ya cigaba da fad'in “Bawai hakan Na birgeni baneba ko a San raina, saboda Ina shiga k'uncine, amma banida za6in daya wuce hakan. nasha wahalhalu Na rayuwa kala-kala kafin na tsaya da k'afafuna, zuciyata ta bushe namance daga wane tsatso na fito, domin idan kinganni a lokacin da nake karatu da koyan sana'oi bazaki ta6a kawo ni jinin sarauta baneba, ko d'an wani, nayi gwagwarmaya sosai irin wadda d'a Mara gata yakeyi, badan mahaifiyata bata sona bane ta tsaya tsayin daka wajen ganin na horu kona nemi na kaina, hikimarta itace nazama jarumi mai yawan juriya, nakuma kwato mana y'ancinmu a lokacinda ya dace, duk wannan fad'i tashin da kikaga inayi wlhy badan nayi mulki baneba kamar yanda su suke tunani, Burina kawai nasan miyasa aka durk'usarmin da mahaifi? Tabbas ni jinin sarautane gaba da baya, kuma yana yawo a cikin jinina, amma rashin kwanciyar hankalin dake cikin sarauta baya birgeni, kallon kitse kawai akema rogo, ayau inason Kituna kema kin haifi yaranda sun rigada sun shigo cikin wannan harmutsi, tunda tazama jininsu, ki fad'amin kodan mu gyaramusu gobensu su rayu cikin salama koda bama numfashine, nasan hakanan bazakima Harun abinda kikai masa d'azunba saboda son zuciya kawai, please miyasa kika hanashi d'aukar Abdurraheem ne? Miyasa kikak'i barina na fad'a masa gaskiyar abinda ya faru?”. Shiru nayi nakasa cewa komai, sai faman had'iye abinda ya tsayamin a mak'oshi nakeyi, Dan bansan yanda zai kalli abunba koya fahimceshi, babu Abu mafi saka rud'u irin cin amanar makusanci, gashi dai a Ransa shifa ba k'aunarka yakeba, amma kulum yafi kowa kusanci da kai, da Nuna girmama alak'ar tsakaninku. (ALLAH ka Shiga tsakaninmu da duk wani Wanda yake tare damu a matsayin fuka biyu, Dan yanzu abinda yafi komai yawaita kenan a rayuwar d'an adam☹😭). Cikin katsemun tunani Yace, “please my friend say Something mana”. Kaina na jinjina masa, cikin nutsuwa nafara masa bayani, Dan yau nayi alk'awarin sanar masa komai, koda zai samu wani haske akan lamarin, shima yasamu nutsuwa a rayuwarsa. “Tabbas kamar yanda kake zargi aiki nakema wani, saidai fahimtar wanene d'in shine mai wahala, na fad'a maka tun farko a dalilin bak'on Abbanmu naji wani yankin matsalasa da bai ta6a sanarma waniba a ahalinsa, a lokacin da wancan abin yafaru Abba yak'i fad'ama kowa dalilin fishinsa a kanmu, dakuma abinda muka masa, hakanne yasaka innarmu zuwa tasamu baba mai kanwa abokin kakanmu na k'ut da k'ut ta sanar masa fushin da mahaifinmu keyi damu, ankuma bashi hak'uri yak'i sauraren kowa, gashi ba dad'in zama takejiba cikin matan gidanmu, wannan Abu daya faru sai sukejin dad'i damata arashi da habaici, harma damu kanmu. baba mai kanwa yace taje zai masa magana, bayannan bamusan misuka tattaunaba. Sai da bayan komai ya lafa harma mun fara karatu sai sanata halluru ya buk'aci abbanmu yabama y'ay'ansa biyu auren yara cikin yaransa, sunzo gidanmu har suka nuna mune za6insu, a lokacin tabbas naji a raina Sa'eed yamin sosai a rai.....” Galadima ya tsuk'e fuska yana taune lips dajan k'aramin tsaki. 'Dagowa nayi nad'an kallesa,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92