Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya d'auki waya yakira cikin ma'aikatan plaza d'in, saiga Saleem, dan Nuren yasan Galadima ya yarda da Saleem sosai, bayan ya gaishesu Nuren yabashi kud'in. Amma sai Saleem yak'i amsa, ya fita kawai. Kusan 30minutes saigashi da yaran restaurant d'in su uku, kowanne d'auke da babban tire, shiya dunga kar6a yana shigarwa office d'in. Da k'yar Galadima yad'anci abincin, danma tuwone, yanason tuwo sosai, maganin Nuren ya 6alla yabashi yasha, sannan suka nufi massallaci dan gabatar da sallar azhur. '*****'*********'*******'*******' Sauban ya sama musu tickets d'in tahowa Nigeria, Momma bata bari Munaya ta d'ebo wasu kayaba, tunda tanada kayanta anan, d'an abinda ba'a rasaba kawai ta d'akko, sunje asibiti sukaima Abie sallama sannan khumar yakawosu airport shida Samha da Khaleel dasuka musu rakkiya. Sunyi zama nakusan 1hour sannan jirginsu yasamu tasowa......................✍🏼 *_ALLAH ya gafartama mahaifanmu😭🤚🏻✋🏻_* [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 ~Book 2~ 👉🏻3⃣ ............Shiru kawai yayi yana kallon fuskarta ta cikin d'an hasken mai kalar jaa, sai fuskar tabada wata kala data k'ara mata k'yau. yaune ranar farko dazaice yamata kallon k'urilla irin haka, yadad'e yana kallonta kafin ya janye idanunsa dake cike da barci. hannu ya mik'a ya kunna ainahin fitilar, haske ya gauraye d'akin, cikin dabara yafara yunk'urin janye jikinsa, amma tak'i yarda, saima farkawa datayi, tabud'e idanunta dasukai nauyin barci a hankali, kad'an take kallon face nashi, ta lumshe idon tasake bud'ewa. “wannan d'aurin goronfa?”. ‘galadima yay maganar a hankali cikin muryar barci, yanabin hannun munaya da ta zagaye cikinsa da kallo’. Sosai Munaya ta waro idonta yanzun, ganinta a jikinsa kwance, gashi tawani dabaibayesa saita sakeshi da sauri tana matsawa baya da waige-waigen inda take kwance. gabanta ne ya fad'i, dan ita harga ALLAH tama mance ta hau masa gado, tayi saurin rik'e kanta dake sara mata tana tashi zaune. Shima saiya tashi yana binta da kallo, a mugun sanyin murya yace “bakida lafiya ne?”. Hawaye suka wanke mata fuska, muryarta na rawa tace “kaina kamar zai tsage”. Saida yaja 1minute kafin yad'an matso kad'an, yatsunsa biyu ya d'ora gefen wuyanta, saiyaji jikin zau da zafi, ya janye ya d'aura zuwa gefen kanta, jijiyar wajen sai motsi takeyi d'ass d'ass d'ass d'ass, alamaun kan namata ciwo sosai. hannun ya janye tareda sakkowa daga gadon gaba d'aya. Ya zagayo 6ari da take, hannu yasa ya zame nata hannun data tallafe kanta dashi, ta tad'ago idanunta dake cike da barci, sunyi d'anja sun k'ara girma, idonsa a kanta, Dan haka ta janye nata ta maida k'asa tana cigaba da hawayenta. Kad'an yad'an furzo iskar bakinsa, kafin a hankali yace “mike miki ciwo bayan kan?”. Saida takuma matso wasu hawayen sannan tace, “duk jikina”. “kin fad'ine?”. Kanta kawai ta iya girgiza masa, ya cigaba da tsura mata idanu batare da yace komaiba, ganin tana hawaye duk sai yaji babu dad'i, koba komai itad'in Friend nashice ai, kamar yanda yafad'a tun farko. yad'an sauke ajiyar zuciya mai sauti kafin ya mik'e, bayi yashiga, mintuna kad'an yafito, tana a inda ya barta dafe da kanta, yace “taso kid'an watsa ruwa, ko jikin zai huce”. d'agowa tayi ta kallesa, sai taga ya tsatstsareta da mayun idanun nan nasa, tayi saurin janye nata, amma takasa tashi. matsowa yayi kusada ita, ya mik'a mata hannunsa, alamar takama ta tashi, ta d'ago ta kallesa ya d'aga mata kansa yana mai lumshe idanunsa alamun tabbatarwa. Hannunta ta saka a cikin nasa, ya had'e waje guda sannan ya taimaka mata ta tashi tsaye, kallo d'aya yamata ya kauda kai, dukda kayan nata masu kaurine saida yaji wani Abu daban, dansu fidda surarta sosai. Har wajen wankan yakaita, sannan yafito batare da ya ce uffanba. da kallo tabi bayansa, a ranta tana mamakin sauk'in kai irin nasa, ada kallon mutum mai girman kai take masa, amma tunda suka fara rayuwa a tare saita fara fahimtar ba haka baneba, kawai dai shi mutumne dabai cika hayaniya da surutu ba, shiyyasa inbaka gama saninsaba saika dunga masa kallon mai girman kai. Koda ya fito saiya had'a mata tea, shi dama baya rabo dasu a d'akinsa, magani ya d'akko shima ya ajiye, yakoma bakin gadon ya zauna yana tsumayen fitowarta. Kusan mituna 10 tagama watsama jikinta ruwan, lallai naji dad'i sosai, saidai kuma bazan iya maida kayan dana cireba, inajin kunyarsa, kuma jinsu nake sun d'auki zafi, towel naja Na d'aura, saidai bashida girma, bazan iya fita a haka dashiba Galadima yana d'akin, kad'an nabud'e k'ofar Na lek'oda kaina, yad'an juyama k'ofar bathroom d'in baya kad'an, a hankali cikin muryata mai nuna alamun banida lafiya nace “please yalla6ai ka taimakeni da hijjab”. Waiwayowa yayi ya kalleni, alamun baijiba sosai, Na turo baki kad'an sannan nace “please yalla6ai hijjab”. Baice komaiba ya mik'e, inda nake ajiye hijjab d'in yaje ya d'ako, yazo inda nake ya d'oramin akan hannuna dana mik'o, kallon ido cikin ido mukaima juna, kowa ya janye cikeda basarwa. Bayan nasaka hijjab d'in nafito kamar wata muna fuka, sai k'asa nakeyi da idanu nakasa kallonsa, shima idonsa a lumshe ya jingina da fuskar gadon, wucewa nayi wajen akwatina Na d'akko wasu kayan barcin, bayi nakoma Na saka, saina yafo k'aramin Vail Na cire hijjab d'in. Yabud'e idanu kad'an a kaina, batare da yayi magana ba ya nunamin mug d'in daya had'a tea a ciki. nad'an yatsine fuska da marairaice murya tamkar xanyi kuka, “ALLAH yalla6ai banajin yunwa”. Shiru yay kamar bazai tankaba, saida yaja kusan 2minutes sannan yatashi zaune sosai, batare da yayi magana ba ya d'auki mug d'in da drug's d'in ya taso inda nake zaune a kan sofa, saman k'aramin table d'in gaban kujerar ya zauna yana fuskantata, d'an gaf d'in daya bari tsakanina dashi bai wuce tafin hannuba, Dan har inajin saukar numfashinsa, baya nad'anja kad'an Na jingina da jikin kujerar, amma hakan bai hana kusanci sosai tsakanina da shiba. babu magana babu komai naji dirar cup a bakina, d'ago ido nayi tamkar zan fasa kuka, danni wlhy banajin shan shayinan, yamin hararar data saka 'yan cikina harmutsawa, babu shiri nabud'e baki na kar6a, ya had'e girar sama da k'asa, baibar ko k'aramar k'ofar dazan kawo masa wargiba, haka naita kar6a ina hawaye, saida yaga Na shanye tas sannan ya barni yana hararata, nidai yau babu k'arfin mayarwa, yabani maganin, shikam babu musu Na kar6a nasha. ganin yanda naketa hawaye saiya zubamin ido kawai yana kallon ikon ALLAH, nikam banida niyyar daina kukan nawa, kuma nima bansan dalilin kukanba, kawai dai jinake hawayen Na tahowa. Ya zuba tagumi abunsa yana kallona kamar yasamu television. kallon dayake min saiya k'ara tunzurani, nafara kuka mai sauti harda shashsheka. Tagumin yacire yana wani k'asaitaccen murmushi, ya mik'e tseye yakoma kan gadon, filolin dasuke k'asa ya d'auka ya jera a tsakkiyar gadon kamar d'azun. nidai duk ina kallonsa, saida ya lullu6ama k'afafunsa bargo zuwa cikinsa sannan yace, “taso ki kwanta sarkin arhan hawaye”. Harara Na zuba masa batare da Na shiryaba, sai kawai ya ta6e bakinsa yay kwanciyarsa ya barni, tareda kashe fitilar ya maida ta barci. Kusan mintuna 4 Na zame Na kwanta a kujerar, amma sainaji duk babu dad'i, saboda maganin bai fara tasirin da jikina zai bar ciwonba, tashi nayi nakuma zama, kusan 5munutes sannan natashi sad'af-sad'af tamkar munafuka na haye gadon. Ni duk tunanina yayi barci.

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});