Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 62

Chapter 62

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

rahamar ubangiji saiga jinjiri yayi sallama duniya da kuka. tamkar jira itama Munaya ta kar6a, a time d'in Munubiya tayi shid'ewar wucin gadi, amma hannunta na cikin na Munaya datake shan azaba itama. Ba'a d'auki tsawon lokaciba itama tata mace tafito, saikuma sabuwar nak'uda ta tashi a tare suduka, yanzu Munubiya mace Munaya kuma namiji, na Munaya na fad'owa wani yakuma biyo baya😳. Turk'ashi, ALLAH sarkin rahama da tausayi, maiyin yanda yaso kuma ga Wanda yaso, Munubiya ALLAH yabata k'autar tagwaye mace da namiji, yayinda Munaya keda uku, maza biyu mace d'aya. Su doctor Farida duk sun kacame da murna da k'ok'arin gyara yaran, kaikace su akama haihuwar. Dandanan aka shiga goge yara da zaitun, amma cikin hattarar kar a had'esu agaza ganewa.. Su Munaya ma dai kulawa ta musamman aka basu, amma Munubiya ta suma, kuma bata farfad'oba, hakanne ya tada hankalin su doctor Farida suka rufu akanta suna bata dukkan wani taimako, sama-sama Munaya ma kejin 'Yar uwarta tashid'a, hakanne yasata kuma k'ank'ame hannunta hawaye na zurara mata, itama bawani k'arfine da itaba, Dan ko idanu dak'yar take iya d'agawa, dishi-dishima take ganin komai. Lamarin yana san zama babba, Dan saida wani babban doctor ya shigo dole, ganin shigi da ficinsu doctor Farida yayi yawa yafara ankarar dasu Galadima. Nanfa suka fara turkesu da tambayar ko lafiya?, sukuma suna basu amsa da babu komai, kowa dai bai yardaba, dukda suna jiyo kukan jariran. An d'auki wasu adadin mintuna kafin numfashin Munubiya ya dawo, ajiyar zuciyar da Munaya tasaki duk saida yasaka su doctor Farida kallon ta da tausayi, dukda tana cikin wani hali itama, amma hankalinta nakan 'Yar uwarta. Sun kimtsasu tsaf, daganan aka musu allurar barci dansu sami Hutu, yara dai kam Alhmdllh, duk da sun lura d'aya daga cikin na Munaya bai cika kuzariba, kamar sauran mace da namijin sun fishi lafiya, amma basuda tabbas tunda basu bincikaba. Nurse d'aya tafito ta kar6i kayan haihuwar takoma, duk an saka musu, dukda basu zama iri d'aya ba tunda sunzo babu tabbacin miza'a haifa, musamman ma su Galadima, gara su Yaa Marwan sunsan ita Munubiya dama biyune. Tunda su doctor Farida suka fito Galadima dake ta kaikawo shida Yaa marwan da Muftahu suka maido hankalinsu Kansu, Galadima bai iya matsawa ba, saisu aunty mimine suka k'arasa ga su doctor Faridan. Kowa yana k'ok'arin tambayar abinda ke faruwa. Doctor Farida tayi murmushi, tace, “to ai bakine bazai iya fad'a ba ma, inaga kawai angunan k'arnin su shiga daga ciki, idan sun fito kwaji komai”. Yaa marwan da Galadima suka kalli juna, kowa yana fargabar abinda zai tarar d'in. Aunty Mimi ce takama hannayensu tana fad'in “kuje mana, mi kuke tsorone wai?”. Kowa tamkar an doke masa gwiwa haka suka nufi d'akin, Yaa marwan ne gaba Galadima a baya.. Duk sukayi sororo a k'ofar d'akin suna bin gadajen matan nasu da jariran kusa dasu da kallo. Badan kowa yasan kayan jikin matarsa ba dabasu iya banbancewa ba (kunsanfa mu 9ja 'yan gargajiyane🤭, kod'an canja kayannan na asibiti bamayi🤣). Galadima da Yaa marwan suka kuma kallon juna, kowa ya kasa cewa uffan, doctor Farida dake bayansu tamkar ta kwashe da dariya, tadai daure ta danne. Ra6asu tayi ta shigo ciki sosai, ta tsaya tsakkiyar gadajen tana kallon hannun Munaya da Munubiya dake had'e da juna har yanzu, sunyi-sunyi su saki amma sunk'i, sai suka saka musu lokar asibiti a tsakkiyar aka d'ira hannayen Dan kar suyi sanyi.. Juyowa tayi ta kallesu da murmushi a fuskarta, tace, “wannan itace Munubiya ga babies d'inta nan 2 mace da namiji, wannan kuma Munaya ga nata 3 maza biyu mace d'aya. Ina muku fatan alkairi gaba d'aya, ALLAH ya rayasu akan sunna”. tana gama fad'a ta juya ta fita tabarsu. Binta sukayi da kallo harta fice, sannan suka maido ga iyalan nasu, saikuma kowa ya k'arasa da hanzari ga matarsa. Yaa marwan yasaki murmushi yana d'aukar macen, sanan ya d'auki namijin shima, dukya rungume. Galadima kam durk'usawa yay gaban gadon yasa gwiywoyinsa a k'asa ko k'yank'yami bayayi, dukda angyara wajen tsaf tamkarma ba'a haihunba. Hannunsa d'aya ya d'ora agoshin Munaya da duk yaga ta masifar rame masa yau, d'ayan kuma yafara tsafa kumatun yaran d'ai-d'ai, hawaye masu d'umi Wanda shikad'ai yasan ma'anarsu suka fara sauka a kumatunsa. Cikin lumshe ido ya matsa ya sumbaci goshin Munaya da hancinta, sannan ya dawo kan babies nashi yana sumbatarsu. Yaa marwan ma yanacan ya duk'ufa kan matarsa yana mata kalamai masu dad'i acikin kunne k'asa-k'asa, kai kace idonta biyu tana jinsane😹. Galadima ya share hawayen fuskarsa, cikin murmushi yace, *“UBANGIJINA ka gamamin komai, yau nine da k'yautar abin cikin kwan d'ai-d'ai har 3 a lokaci d'aya, badan k'arfina kabaniba, bakuma Dan nafi sauran bayinka ka baniba, suma y'ay'a jarabawace ga iyaye, ya Mahaliccinmu kabamu ikon bama yarannan tarbiyar da zasu zama cikin alfaharin MANZON ka da addininmu mu da mahaifansu mata, ka rayasu bisa turbar addinin islama, ALLAH yasa suzama masu tausayi da jink'ai gana k'asa dasu damu kanmu, su zama masu girmamawa da mutunta na sama dasu a duk inda suka shiga, ya RABBI ka rinjayar da zukatansu ga bautarka domin rabauta a duniya da lahira, ka nisantar da zukatansu da gangangar jikinsu ga sa6onka komin k'ank'antarsa dagasu har 'yan uwansu gasunan guda biyu da k'annensu masu zuwa da dukkan y'ay'an Al'ummar musulmi. I love you so more and more my Darling children's, ina muku barka da isowa duniya gidan gwagwarmaya, ALLAH yabaku damar cinye jarabawar da ubangiji ya k'addaro a cikin tsawon rayuwar da zakuyi a dunia kafin Ku koma garesa”.* Yaa marwan ya amsa da amin shima fuskarsa d'auke da murmushi. Tashi Galadima yayi yaje gareshi suka rungume juna. Galadima yace, “d'an uwana ina tayaka murna”. Yaa marwan ma yace, “ranka ya dad'e nima ina tayaka murna”. Sakin juna sukayi suna dariya, saikuma suka kuma cafke hannun juna cikin musabaha da nuna tsantsar farincikin dake baibaye da zukatansu a yau d'innan. Aunty Mimi kasa hak'uri tayi ta danno kai d'akin babu ko sallama. To shigowarta cefa ta fallasa komai, kowa yasan d'unbin alkairin daya sauka a wannan families guda uku a yau. Dan danan labari yafara karad'e asibiti da gidajen su Galadima Dana su Munaya. Masarautar gagara badau, masarautar su papi, su Momma duk labari ya Isar musu harda hotunan babies gaba d'aya, kafin kacemi labari yafara zagaye social media, *FANS NA RAINA KAMA FA* babu ala, dama duk sungama shirinsu, (danma ansamu sa6ani masu tafiya india🤣, Wanda basu kai ga tafiya ba ALLAH ya taimakesu saiku tattala kud'in jiyginku babu ruwana😹😂🤸🏻‍♀). Bakin Galadima da Yaa marwan da dukkan ahalin wad'annan dangi kam yakasa rufuwa, hardamu ma masoyansu. Yauma dai su doctor Farida da jama'ar asibiti sunsha k'yaututtuka, Dan Muftahu ya baza abin mamaki, ( lokacin da su sarkin mota zasu fitone yagansu kamar a rikice, shikuma zai fita daga masarautar shine ya tambayesu, sarkin mota ya fad'a masa, bai bisuba saiya wuce asibiti, shine yasaka aka canjama Munubiya d'aki, aka tanadi gadon Munaya kuma). dukda Galadima yayi mamakin ganinsa hakan bai sakashi tambayarsa ba ko katse masa hanzari, ko'a fuskama bai nuna mamakiba. *************** Mama Fulani Na kishin gid'e bisa kilisarta kuyanginta Na bautar da suka saba, Wambai na gefenta yana nuna mata pictures na gidaje dayake son za6ar d'aya daza'a gina masa shima

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});