Chapter 23
Chapter 23
ya sameshi da sallama, sai bayi buyu dake binsa a baya d'auke da ledoji. Galadima ya bud'e idanunsa yana kallonsu amma bai tashiba, bayan bayin sun ajiye suka zube sunama Galadima barka da hutawa, murmushi kawai ya musu ya d'aga musu hannu. Sauban yabasu izinin tafiya. Zama Sauban yayi a kujerar dake kallon Galadima, “kai yau ina cikin nishad'i wlhy yaa Sam...” Kallonsa Galadima yayi yana d'an murmushi, amma baice komaiba. Sauban yace “yaa Sam... Aunty gimbiya fa?”.. Galadima yace “barci takeyi”. “tofa Unborn babynmu yazo da sabon salo kenan”. Hararsa Galadima yayi, ya mik'e yana dariya ya shige bedroom. Galadima ya girgiza kai kawai yana tashi zaune. ledojin ya duba dan ganin mi suka sayo?. Abinda yasan zata iya ci ya d'auka ya fita. Saida ya d'anyi jimm a k'ofar d'akin sannan ya shiga da sallama, har yanzu tana a kwance tana kuka, lips d'insa ya d'an cija sannan ya ajiye abin hannunsa saman table d'in dake gaban gadon, idanu ya tsura ma bayanta nawasu 'yan seconds, ko alk'yabbar bata cireba, zama yayi a bakin gadon kusada ita, amma ya juya mata baya. Tun daga shigowarsa har zamansa tana jinsa, amma ko motsi batayiba, kusan mintuna 3 suna zaune a haka, ganin batada niyyar tashi ko kulashi ya sakashi juyawa yana kallonta, gyaran murya yayi sannan yace, “tashi kici abinci”. Shiru tayi ta shareshi, ko motsima bata yiba. Tsawa ya daka mata, babu shiri ta tashi zaune, jikinta sai rawa yakeyi, tunba yanzuba munaya akwai tsoron tsawa, bata barin saita kwana amma batason amata tsawa. Shi kansa yayi mamakin tsoratar tata, ya watsa mata harara yana kwafa, sai kuma yaja tsaki, alk'yabbar yacire mata, sai hawaye take zirarwa, bai kuma cemata uffanba ya bud'e abincin ya ajiye a gabanta, kafeta kawai yayi da idanu, hakan saiya tasirantar da tsoronsa a zuciyarta, dan haka tafara cin abincin, tanayi dai hawaye na zurara, cikin nata bamai tsurfa baneba, komai ci take hankali kwance, sai dai laulayi na ciwo. Dolenta ta saki jiki taci abincin, danya kafeta da idanu ga fuska cid'in-cid'in, duk jarumtarka dolene kaji shakkarsa. Kallo d'aga tamasa ta janye idonta, shi kuma ya harareta yana fad'in “kin k'oshi ne?”. Kanta ta jinjina masa tana matso kwalla. baice komaiba ya sauke sauran abincin k'asa, sannan yace “sauka kije kiyi wanka”. Baki ta bud'e zatayi magana ya dalla mata harara. sauka tayi tana k'unk'uni akan la66a. yana kallon motsin la66an nata, sai dai bayajin mi take fad'a. Yau kam Alhmdllh taji dad'in jikinta, ko k'arin ruwan da aka saka matane yasakata jin kwarin oho, ruwa mai d'an d'umi ta tara tayi wankan, tanayi tana hawaye, itafa ko mi zaiyi ba masifaba bazata bar cikinnan ba, babu yanda za'ayi ta reni ciki ta haifeshi sannan yazo daga baya ya saketa, bazata d'auki wannan rainin hankalinba, su maza a kullum d'aukar mace suke mai k'arancin tunani, kowane yayin rashin mutuncinsu suka kwaso saiya k'are akan mata, wlhy akan cikinnan tata d'aga masa hankali kenan harsai ya amince an zubar dashi sannan, kuma ana zubarwa zata k'ara gaba, mahaifinsa kam kobasa tare insha ALLAH zata cigaba da masa addu'oi ana aika masa. Jin shiru tak'i fitowa ya sakashi mik'ewa, bai wani kwankwasa ba ya bud'e k'ofar bathroom d'in kawai, danshi zatonsa ba wankan takeba ta tsaya kukane. A birkice munaya ta kalli k'ofar, ganin Galadima tsaye yana kallonta ta fasa k'ara, yay hanzarin ida shiga bayin ya rufe bakinta da tafin hannunsa dankar ta tara masa jama'a. Juyawa tayi ta ruk'unk'umesa, tare da saka hannayenta ta zagaye bayansa ta manne k'irjinta da nasa, ita duk bata son yaga jikinta ne😂😝. Shima fuskantar hakan da yayi ya sakashi sakin murmushi, saiya saka hannunsa biyu ya zagaye bayanta ya manneta sosai a jikin nasa. Shiru sukayi nawasu seconds, tana sauke ajiyar zuciya shima yana saukewa, saboda yanason ganin yanda zatayi saiya fara k'ok'arin janye jikinsa itama zai janye ta. K'ank'ameshi tayi ta fashe da kuka, jiyay tamkar ya kwashe da dariya, amma saiya daure, cikin dakiya yace, “malama sakeni mana? konaci bashinki ne wai?”. Cikin dasashshiyar muryarta datasha kuka tace, “to kabani zanina da hijjab na saka”. “to kin k'udunduneni ta ina zan iya baki wani zani? sakeni saina baki”. Kafad'a ta nok'e alamar tak'i. Murmushi Galadima yayi, ya shafa bayanta cikin murya k'asa-k'asa yace, “idan an hanani ganin can ai gashi ina kallon nan”. Da sauri tayi wata wulk'itawa ta koma bayansa ta 6uya. Kansa ya dafe yana fad'in “yau Sameer kaga ta kanka, ranar farin cikinka sai saka maka ciwon kai da zafin kai akeyi, wai ke yalla6iya mikike 6oyemin daban saniba ne?”. Baki ta murgud'a masa tana fari da idanu, dayake ba ganinta yakeba baisan hidimar datakeyi ba. K'ok'arin juyo da ita ya farayi amma tabi ta kanannad'e shi, rasa yanda zai mata yayi. yakula yarinyarnan 'Yar daruce kawai. zaninta ya jawo ya mik'a mata, saida ta tabbatar ta d'aura sannan ta sakeshi, yana juyowa ta juya masa baya ita kuma. Baice komaiba ya ta6e baki ya fice daga bathroom d'in. Harar bayansa tayi ta na fad'in “ALLAH ya isana”. Nace Humm.😏 Fita yay daga d'akin gaba d'aya, tunda dai yasamu taci abincin, harya kai k'ofarsa ya tuna batasha maganinta ba, dawowa yayi da baya. Ita kuma motsin fitarsa dataji yabata kwarin guywar fitowa. Shigowarsa tasata kwakumar hijjab ta saka, bakinsa ya ta6e ya wuce wajen handbag d'inta batare daya kalleta ba. Magungunan ya fido, ya zauna bakin gadon, “kizo kisha magani”. ya fad'a cikin k'asaitarsa. 6ata fuska tayi, tace “babu amfanin tattalin abinda za'a zubar ai”. Lips d'insa ya cije, sai kuma ya ajiye drugs d'in yana kallonta, mik'ewa yayi ya taka inda take, a bayanta ya tsaya, fisgota yayi ta fad'o saman k'irjinsa, saida ta rumtse ido dan zafin dataji, ya matso da fuskarsa daf da tata, a wani yanayin data kasa fassarawa yace “adadin nawa kike buk'atar na biyaki danki barsa?”. Rik'esa nayi da k'yau gudun karna fad'i, na janye idona dake cike da kwalla daga cikin nasa, “Bana buk'atar ko sisinka yalla6ai, cikinne kawai bana buk'ata, kuma bazan raineshi ba balle nakai ga haifeshi”. Wani murmushi mugunta yayi, sanan ya sakeni tamkar zai hankad'ani, mikuma ya tuna oho masa, saiya kuma damk'e hannuna, muryarsa a kausashe yace “wlhy idan kinga baki haifi cikin nanba to sai dai idan wanine a cikinmu numfashinsa yabar gangar jikinsa, sai kuma idan ubangiji ya kaddara Shiba mai Shak'ar iskar duniya bane, dan bani da hakk'in kowa, ubangiji kuma bazai barki ki shiga nawa ba”. yana gama fad'ar haka ya saki hannuna yafice daga d'akin baki d'aya. Yariga yasan zai fuskanci abindama yafi haka daga munaya, shiyyasa bai zafafama zuciyarsa akan wannan rikicin nata ba, shi babbanma burinsa yanzu Abbanta yabar k'asar nan, danya samu damar gudanar da aikinsa yanda ya kama ta. Da wannan tunanin ya dawo d'akinsa, ya iske Sauban kwance wai zaiyi barci, hararsa yayi yana fad'in “ kama tashi, time d'in zuhur yayi. Yana fita na raka bayansa da harara ina murgid'a baki, “oho dai, koma mizaka fad'a ka fad'a, nima ai bani tare da hak'k'in kowan, ALLAH kuma bazai baka damar danne nawaba, sokake nazama shashar mace ko? munyi auren contract batare da sanin iyayena ko naka ba, kazo kamin ciki na haifa maka ka sakeni na koma gidanmu,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92