Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 49

Chapter 49

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dan Alhaji balala baya son abinda zai 6ata record d'insa, kuma mamar yaronce ta Dage sai anyi auren dan ita mutuniyar kirkice, dan haka mu bama Malam Saminu wannan damar”. Ajiyar zuciya Nuren ya sauke, cikin mamaki yace, “duk ya akayi kasan wannan brother? ”. galadima ya murmusa, yana fadin “Nuren kenan, to bara nayi copy d'in my mata, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo, nasha fad'a maka bada kwanji kawai ake yak'i ba, sai anhad'a da dabarun tunani dana nazari, so kad'an nafad'a maka daga abinda ya shafi Malam Saminu, kaidai saina jika kawai, a time d'in da zakuyi maganar ka tabbatar ka had'a Communication dani ok?”. “babu damuwa aljanin munaya”. Dariya sosai Galadima ya shiga tuntsurawa da iskancin Nuren, wato shima ya maida Aljani yau, wlhy yaronnan yagama rainashi, wai Aljanin Munaya, d'an iska zan kamaka ai. Kashe komai yayi ya fito daga d'akin, bai koma cikiba saiya sakko k'asa, ya iske Sauban kad'ai a falo, shima shigowarsa kenan daga asibiti yake. Galadima ya zauna yana fad'in “jirgi sarkin tashi daga ina?”. Dariya sauban yayi, yace, “kai Yaya, nine kuma jirgin?”. “Kamafi jirgi ai. Wane shiri kakeyi gameda zuwa bautar k'asarka Nigeria”. Sauban ya 6ata fuska kamar zai fasa ihu “yaya yanzu fa ca za'ayi saina koma 9ja har zaman 1year?”. Hararsa Galadima yayi, “to zakayi anan k'asar ne?”. “Ni Yaya ALLAH da anayi da nayi, a manta da bautar k'asar kawai mana, nayi joining masters d'ina”. K'aramin tsaki Galadima yayi, yay crossing k'afarsa yanama Sauban wani kallon bammasan amsar dazan bakaba, saida ya d'auki wasu mintuna sannan yace, “rashin yin ai bazai zama matsalar kowaba sai taka, bakuma zaka gane hakanba sai nan gaba idan ALLAH ya kaika inda bakayi zatoba, idan kace bazakayiba it's better, nidai ai nayi nawa ko. tashi kabani waje”. Ganin ransa ya 6aci Sauban ya marairaice fuska zaiyi magana, amma sai Galadima ya d'aga masa hannu, sannan yamasa nuni da k'ofa alamar ya fice masa. Fita Sauban yayi yabarsa, shifa tsakani da ALLAH zaman masarautar ne baya son yi shi kad'ai. Galadima ya girgiza kai kawai yana fad'in “ALLAH ya shiryeka, gata kasamu tunda katashi kaga komai basai ka nema ba”. Jakadiya data fito ta rissina tana fad'in “Ashe ka shigo magajin gari, barka da dawowa”. Murmushi Galadima yayi, yanason matarnan saboda halaccin datake wa rayuwarsu, “yauwa jakadiya, ya gidan?”. “lafiya lau Ranka ya dad'e, a shirya abinci ko?”. Agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalla, sai kuma ya maida ga jakadiya, “bar abincinan jakadiya, akwai Inda zanje”. “to ALLAH ya dawo dakai lafiya”. Hannu ya d'aga mata kawai sannan ya tashi ya fice. mashin ya hau yafita. Abba dake can gefe a harabar gidan tsakanin wasu flowers yana hutawa ya sauke ajiyar zuciya, tundaga fitowar Galadima har hawansa mashin da fitarsa akan idonsane, rufe idanunsa yayi yacigaba da tunaninsa da tun d'azun yake zaune a wajen yanayi. Asibiti Galadima ya nufa, yay kici6us da Aunty Mimi Na shirin tahowa gida ta huta, ta kalleshi da mamaki, “my k'ani dawowa kayi?”. Gefen girarsa yad'an shafa da d'an yatsa d'aya, “eh , ina zakije k?”. “gida zanje nad'anyi wasu abubuwa”. “ok sai kin dawo”. yafad'a yana ida shigewa, ita kuma ta fice. Momma Na zaune tana waya da papi, ya zauna d'aya a kujerun yana kallonta cikeda sha'awa, uba da 'Yar sun birgeshi, juyawa yay ya kalli gadon Abie, barci yakeyi, har Momma ta gama wayar ison Galadima Na kan Abiensa ko k'yaftawa bayayi, shi kad'ai yasan mi zuciyarsa take sak'awa. “Muh'd daga ina haka?”. Maganar Momma ta katse masa tunani. Janye idonsa yayi daga kan abie ya maido ga Momma, “Daga gida Momma, har yanzu barcin Abie yakeyi?”. “eh tunda ka Fita bai farkaba, mike faruwa naganka cikin damuwa?”. Huci ya furzo daga bakinsa, zaiyi magana sai kuma yayi shiru. “Nifa tsiyata dakai kenan Muh'd, Yaya Abu nacin ran mutum bazai iya fad'ama kowa a taimakeshi da shawara ko addu'a ba, kaga yanda jijiyar kanka ta tashi kuwa? Haba Muh'd Sameer d'ina, kaifa yanzu ubane, girmanka ya k'aru, aringa rage damuwarnan da miskilanci mana, ni ALLAH ma yasa ba haka kakema d'iyar tawaba?”. “kai Momma”. ya fad'a amarairaice cikin 'Yar shagwa6a. Murmushi tayi tace “to fad'amin mike faruwa?”. Yay d'an tsaki, “Ni ai Momma bammasan ta ina zan fara baneba”. “kafara ta sama kawai”. Momma ta fad'a tana dariya. Shima dariyar yayi kad'an sannan ya gyara zama, kuma maida muryarsa k'asa-k'asa yayi yana maganar ahankali, tsaf ya zayyanema Momma yanda sukayi da Munaya, ya d'ora da fad'in “Amma kinsan wani Abu kuwa Momma?”. “a'a saina fad'a dear”. “uhm gani nake kamar bakomai ta fad'a minba, ta 6oye wasu abubuwan dai kamar, saidai bansan dalilinta ba. Momma ta jinjina kai tana murmushi, “To Muh'd mizai hana kacigaba da binta a hankali, nasan zata fad'ama sauranma, ni aganina kamar tana ganin kaima ka kasa yarda da itane shiyyasa tafad'i wasu tak'i fad'in wani, idan har ka yaba da hankalin matarka yakamata ka fara sakin jiki da ita wajen Neman shawararta da sakata cikin wasu al'amura naka Na tabbata itama zata fara fad'a maka nata”. “gaskiya kika fad'a Momma, dan naga fa'idar hakan kwarai da gaske, zan kula insha ALLAH. ya addu'oin Abie akwai saura?”. “saura kad'an, gashi bakuyi wasuba”. “mai k'arfin yince tazama sai a hankali, daga barci sai barci take yini”. “ALLAH Sarki d'iyata, ai tanama k'ok'ari, dama idan ciki ya fara tsufa hakane, ALLAH dai ya sauketa lafiya”. “To amin Momma”. Sun cigaba da 'yan hirarrakinsu har zuwa lokacin da Abie ya farka..................✍🏻 *_inata gaisheku da yawa da yawa, comments naku Na sakani nishad'i over🥰🥰🥰🥰🥰😍😍😍😘😘😘_*. I love you wijiga-wijiga sister's🥰🥰🥰🥰 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🤚🏻✋🏻 [7/4, 2:30 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻1⃣8⃣➖1⃣9⃣ .................Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gadon Na nufi Na watsa ruwa. Ina tsaka da shafa mai Samha ta shigo, saida tayi sallama nabata izinin shigowa sannan, ledar hannunta Na kalla ina fad'in “mikika samo mana 'Yar Uncle?”. Cikin dariya ta zauna kan sofa tana cewa “kayan dad'i ne Aunty gimbiyarmu, alfarma nazo nema wajenki keda Uncle”. Hankalina gaba d'aya Na maido kanta, “Alfarmar mi kuma?”. “Aunty gimbiya please ki lalla6a Uncle ya barki muje birthday d'in k'awata Dhibya, ALLAH yarinyarnan tana sonki sosai, kullum hirarki”. Nad'an zaro ido “kai Samha yaza ai naje wani birthday da wannan cikin? kuma kema kinsan bazai bariba tunda Na 'yammatane”. “kai aunty, cikin saikace Wanda yayi wani k'ato, kumafa a cikin gida za'ayi wlhy, iyamu goma ne kawai”. “to naji, ALLAH yasa ya bari, mikika kawo mana a ledar?”. “yes my sweet aunty, wannan wani sari ne yamin k'yau a wani shagon da muke zuwa siyan kaya, shine nayi alk'awarin siya miki, Uncle Sauban ya cikamin na siya, yanzu Na kar6o please ki gwada muga”. Dariya nayi, nace, “inye kaga 'Yar Uncle Anfara jink'an iyaye, to amma ni ina na iya saka sari?”. “kowama koya yayi nidai ki saka muga dan ALLAH”. “to shike nan bara na gwada, ALLAH ya saka da alkairi, ina alfahari da d'iyata”. Samha ta fita tana dariya, nikuma na warware kayan, masha ALLAH sarin ya had'u gaskiya, farine

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});