Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ko rufe motar baiyiba sai a cikin bayin ne wani yataso yarufe, a falo ya wuce Samha na barci itama, tunda muka shigo ta zube a wajen, tun yana taka steps d'in yafara cire bottom d'in Indian suit d'in dake jikinsa white color, burinsa yana shiga d'akin yagansa a gado kawai. Ganina baje a gadon yasashi yin turus yana kallona, yay saurin kauda idonsa gefe saboda kayan jikina sun kamani sosai, sun mugun fito da surar jikina d'as, gashi sun bala'in min k'yau, yau da ace matar dayake soce babu abinda zai hanashi yabawa harma yabata tukuycin wannan kwalliyar, tsigar jikinsa sai tashi takeyi, gashin jikinsa duk ya mimmik'e, rigarma yakasa k'arasa cireta, ya dafe kansa yanajan guntun tsaki, miya kawo yarinyarnan gadonsa?. Yayi maganar cikin zuciyarsa. Jin jiri na neman zubdashi a k'asa yay saurin zama bakin gadon, samu yay ya lalla6a ya ida cire kayan, duk da yafi buk'atar kwanciyar haka ya daure yad'an watso ruwa, sannan yafito yasha magani, koma shafa'i da wutiri baiyiba, a nufinsa sai zuwa anjima zai farka yayi. Abin dariya, saiya jawo dogayen filullukan gadon yajerasu a tsakkiyar gadon sannan ya kwanta can k'arshe, shima babu dad'ewa barcin yay gaba dashi. (Wlhy kafad'o babu ruwana fad'ama fans zanyi Galadima ya tik'o k'asa ehe😏🤨🤣🤣) Can cikin barci Galadima yafara juye-juye, yasaba shi kad'ai yake kwana abinsa, jin fillos a gabansa yasa hannu ya d'aukesu yayta wurgawa k'asa cikin barci, sannan yay juyi zuwa tsakkiyar gadon. Munaya kam tasaba da kwanciyar mutum biyu. dan haka ko juyin zatayi bata barin inda take kwance, duk da ma batasan da Galadima a gadon ba, tunda batasan ya shigoba. Barci yay barci saiga su yalla6ai Galadima masu jera fillos a jikin munaya😂, d'umin jikinta yasashi kuma nanik'e mata, saboda zazza6in daya rufeta, kasancewar yanajin sanyi-sanyi sai jikinta yamasa dad'i. Itama saita kuma lafe masa a jiki saboda jin sanyi-sanyi da k'amshin turarensa kuma, sunbi sun k'adandane juna kaikace ana shirin rabasune, kowa yana amfanuwa da yanayin jikin d'an uwansa. Humm, bara na lek'o su innaro 'yan Nigeria suma🤗, mai tuk'ulluma a goshi ba🤭🤫, ni nama godema mamansu yaa Hameed🤣 dama k'afar suka karya😝. _____________________________ Anbama innaro magani a wani camix suka dawo gida, gidanta aka kaita, innarmu tad'an dafa ruwa tazauna kusada ita tasaka k'aramin towel danta gasa mata goshin koza'a samu yarage tukullumar dayayi. Innaro ta 6ata fusaka zatama innarmu tijara. Baba k'arami yay saurin tareta da fad'in “haba inna, Dan ALLAH kibari tamiki, naga wad'anda suka miki abunma ko kallo baki ishesuba balle su nuna damuwarsu akai, wai shin minene laifin Ai'sha agarekine?”. Abbanmu da daddy suna zaune basuce uffanba sudai. Harara innaro tazuba ma baba k'arami kawai amma batace komaiba, itakuma innarmu ta saka towel aruwan tafara gasa mata. Tanama innarmu masifa dai har akad'an gasa mata, aikam saigashi wajen yad'an saki, baba k'arami yamik'a mata kofin tea d'in da maman fauziyya ta had'a. Kar6a tayi tana yatsine Baki, amma saigashi ta shanye tas, aka bata magani shima tasha ta kwanta. Basu bar gidanba saida tasamu barci, da innarmu tace zata kwana annan, sanin halin innaro Abba yace a'a tatashi suje gida tunda ga habiba d'iyar gwaggo safiyya dabata komaba. Badan innarmu tasoba tahak'ura, Dan aganinta innaro itama uwace agareta, kodan hallacin da mijinta yama iyayensu da darajar abbanmu, amma takula ran Abba a 6ace yake, kad'an yake jira a ta6ashi ya fashe, shiyyasa bataja zancen yay tsawoba ma. Koda suka shiga gida kowa sashensa yayi, innarmu harta kwanta saiga Abba yashigo d'akinta, abinda bayayi kenan, yakan shiga sashen matansa amma baya kwana, saidai mace tabishi nasa d'akin. Tana yunk'urin tashi zaune zata tambayesa lafiya? ya d'aga mata hannu kawai ya hawo gadon tareda janta a jikinsa suka kwanta. Bai bata damar maganaba Dan haka tayi shiru kawai kamar mai barci. Kamar yanda Abba bai isashen barciba hakama innarmu batayiba, Zarah ma kwana tayi kuka akan rashin shigowarsu Sa'eed. Hakama mamansu yaa Hameed da Gwaggon Haleematu basu rintsaba dasukaje gida. Kwana biyu da faruwar lamarin Abba yak'i cewa komai, yakuma k'i sauraren wayar da ake masa daga gidan matan nasa. Innaro harta fara samun sauk'i itama. Sa'eed kam dadynsa ya taso k'eyarsa washe gari gidanmu, an tattauna akan maganar, yafad'i dukkan abinda zarah ke masa, wani ta amsa laifinta wani kuma ta musa ba ita tayiba, sai wani cikin iyayenmu ya harareta take shiru. Nandai aka musu fad'a bayan itaba dad d'insa yace tafad'i abinda yake mata, saboda kar ahanata komawa saitace ita baya mata komai, wannan yasa aka musu fad'a da nasiha kawai akace yad'auki matarsa su tafi. Dad'i tamkar zai kar zarah kuwa, saitaji zuciyarta wasai, bata tareda damuwar komai, (kota manta uwarta bata gidansu itama a dalilinta kuma🤕?). Washe garin rana ta uku tunda safe saiga mamansu yaa Hameed tareda yayanta ya maidota, (dayake babanta ya tsufa sosai, komai nasu yanzu sai yayan nata, ko kud'inma dashi suke tak'ama yanzun, duk da mahaifinsu ya tara musu). Abba dai k'in saurarensa yayi, saida yaje ya kama k'afa da baba mai kanwa aminin marigayi mal. faruku, daddyne yamasu jagora zuwa gidan innaro dake kwance tana jiyyar goshi, damma kullum sai innarmu ta gasa mata safe da yamma, duk da masifar innaro da take sha batayin zuciyar ko nuna gazawa. Ansha fama akan Abba kafin ya sauraresu, danma akwai baba mai kanwa ne a zancen, amma ya tabbatar musu da Cewar shifa yagaji da iskancin dasuke masa a gida, tun zamanin k'uruciya har girma yafara kamasu sun k'asa canjawa, yabama kowaccensu damar k'arshe inhar suka kuma Tayar masa da rikici agida kowacce zata nemi hanyar gidansune, kuma tatafi kenan har abada, Dan bazai duba 'ya'yan dake tsakaninsuba ma. Tunda ga ranar mamansu yaa Hameed tadawo gidan, Gwaggon Haleematu kam bata dawoba, itada iyayenta sunce sai Abba yazo da Kansa koya turo anbasu hak'uri. Shikuma ya rantse saidai tayita zama inhar saiyaje bikonta. Gidanmu dai kam kwana biyu tsit kakeji, Dan baba k'arami da daddy ma summa matansu kashedi da sharad'in barin gidan gaduk wacce tasake fad'a da wata, wannan dalilin yasaka gidan yin lafiya, 'yan anguwa da makwafta sukaji kasiririt. Innaro ma ta warke abinta, saidai kam sun k'ulla da mamansu yaa Hameed, Dan yanzu ko 'ya'yanta basuda farinjini wajen innaro, ko Naziru autansu yamata Abu saita makeshi (ho innaronmu ta mutunci🤣😝). *************** Zazza6i dai yahana Munubiya sakat, yaa marwan yagaji da lalla6ata ga ciwo na cinta, yau dai yakwasheta zuwa asibiti tana kukan batason zuwa, amma yak'i saurarenta. Haka dai sukaje, bayan yankar kati dabin layi suka sami ganin doctor, gwajin farko doctor yabasu albishir d'in samun rabo na wata d'aya kacal (yaa marwan sharpshooter🤭, Munubiya dai inaga tuntu6e akayi🤫🤣). Wayyo zokuga murna wajen ogan miskilanci, babu kunya yakira Abbansa ya sanar masa, shima murna yaytayi ata cikin waya, kafin kace mi zance yabaje dangi, har innarmu labari yakai kunnenta. Harda kukan dad'i tayi, ikon ALLAH kenan, ita saida ta jera shekara 20 tana kuka da shan gori kafin ta samesu, amma ga Munubiya wata 1 da sati d'aya da aure har ALLAH ya kawo rabo. Saura munaya, k'ila itama d'indai an samu, tunda shekaran jiya dasukai waya take mata complain batajin dad'i. haka innarmu taita murnarta a d'aki ita kad'ai, babu Wanda ta sanarmawa tabarma cikinta, a cewarta idan yafita ko Munubiya tazo

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});