Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 69

Chapter 69

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Na gargajiyane, kar6a tayi ta shanye tana yamushe fuska, ta mik'a mata kofin sannan ta zauna sosai. Tausayinta ya kama Galadima, iyaye mata nashan wahala akan y'ay'a, ALLAH ne kawai zai biyasu. Ganin ta dawo dai-dai duk sai suka fita suka basu waje, bayan Aunty Mimi ta d'ora masa babyn a cinyarsa. Sannu ya kuma mata yana gyarama yaron kwanciya, murya a hankali tace, “ya daina ai, amma wlhy ciwon cikinnan yamafi haihuwar zafi”. ‘ta k'are maganar idonta cike da kwalla’. Tausayi ta kuma bashi, ya matso kusada ita sosai yana ruk'o hannunta, yace, “insha ALLAH Akash zai zo miki da Magani zuwa gobe, zai daina gaba d'aya ”. Kanta kawai ta d'aga masa amma batace komaiba. Kukan da macen tayi yasakasu kallonta su duka, nuni yamata ta d'auketa. Batayi musuba ta d'auketa ta saka a acinya, kamar jira suma sauran suka farka harna hannunsa, kai Munaya ta dafe tana fad'in “ni jikar fharuk ku shikenan da d'aya ya tashi kowa saiya tashi”. Murmushi yayi, “to basu birgeki ba ma, sunyo gadonku ne keda Munubiya, Ku ba haka kukayiba?”.. “a'a mukam ba irin wannan mukayiba yalla6ai”. “humm, ai inna ta sanarmin komai yarinya”. Da mamaki Munaya ta waro masa ido, ya d'aga mata gira yana kashe ido d'aya. 'Dauke idonta tayi cikeda basarwa. Shima saiya mik'e tsaye d'auke da yaron d'aya, ya kalli agogon dake a hannunsa sannan ya kalleta “inason ganinki”. daga haka ya sunkuya ya d'auki macen ya juya zai fita. “wai ina?”. ta fad'a da saurin dan karya fice. Juyowa yayi ya d'an kalleta, kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace, “sashena”. bai jira cewarta ba yay ficewarsa. Kanta ta dafe tana sauke ajiyar zuciya, shi bama ya ganin gida cike da mutane, fitinar yalla6ai yawane da ita wlhy. batayi yunk'urin binsa ba, saima zaman shayar da Wanda ya bari tayi, harsu Samha suka dawo ganin ya fita. Shikam yanacan kwance a gado ya d'ora yaran saman cikinsa yana shafa bayansu, yayinda zuciyarsa ta tafi wata nahiyar tunani, ganin lokaci yaja bata zoba ya kalli a gogon hannunsa, shidai bazai kuma kiranta akan tazo ba, idan ta gadama kartazo. Mom data lura babu sauran yaran ta tambaya, cikin kunya Munaya tace, “suna wajensa”. Banbancin babba da yaro saurin fahimta, mom ta fahimci d'an nata yana buk'atar ke6ewa da matarsa, shiyyasa ya d'auki abinda dole tabishi inda yake ta kar6o.. Tace, “to aiko jeki ki kar6osu, dan shirin barci zan musu nima Na kwanta, gobe ba zama za'a samuba hidimomi zasuyi yawa”. Kamar Munaya tai ihu haka taji, to a aiki Ayusher da Samha su kar6osu mana, ai ba dole sai itaba, amma babu yan da ta iya, dan bazata iya sa6a umarnin Mom ba dai. Dogon hijjab ta d'auka ta zumbula, Mom kamar tayi dariya, a ranta tace, Munaya shi namiji ai ba'a hanashi yanda yaso, balle naku na yanzu da suke a fetsare ma. Harzata fice mom tace, “shima zoki d'aukesa”.. Ta kalli mom d'in tana fad'in “mom aikuma zasuyi yawa wajen d'akkowa”. “eh d'auka, basai ya tayaki ku d'akko ba”. Babu yanda Munaya ta iya dole shima ta dawo ta d'aukeshi, sai wani k'yallo idanu yakeyi Lamar yasan mi akeyi. Babu kowa a afalon, harma television an kashe, babu yanda ta iya dole ta nufi bedroom d'in, saida tayi sallama yabata izinin shiga sannan ta shiga. Harta zauna idonsa a kanta itada babyn hannunta, saiyaga ta k'ara masa k'yau ma da girma. Yace, “kin gama jan ajin? ai saki bari sai randa nazo tad'i ki jamin bawai yanzu ba”. Munaya ta ciza lips d'inta kawai batare da ta tanka masaba, Yaran ya kwantar gaba d'aya, sannan yatashi zaune yana fad'in “taso”. “intaso kuma, ba magana kace zamuyi ba? please ka fad'a a haka”. ta fad'a kamar zatayi kuka, (Dan hirar innaro da laraba ta tuna da sukace jiya wata yarinya sati biyu da haihuwa ta yarda da mijin saiga ciki ya fito yaro Na wata uku, ciki wata biyu da sati biyu🤣, itama fa yanzu kaffa-kaffa zatakeyi da Galadima, inma baka badaba sai'a saka maka k'arfi🤭😂). Tsaf Galadima ya fahimceta, dan haka yay wani miskilin murmushi yana fad'in “oh kina min bak'in cikin sake ajiye abin cikin kwan ne?”. Sosai Munaya ta waro idanu, a firgice tace, “ban ganeba?”. “Zaki gane lokacin da kika zo hannuna”. Ta yunk'ura da sauri ta mik'e, ita tama manta da yaro ajikinta, ALLAH dai ya kiyaye tai saurin tarboshi, Galadima ma dirgowa yay daga gadon, saidai kawai ta gansa kusada ita. Rungume yaron tayi tana sauke ajiyar zuciya, gashi mai kamar mara lafiyarne. Shima Galadima had'ata yay itada yaron ya rungume, ganin haka saita mik'a masa shi ita ta janye jikinta. hannunta ya rik'o ya maidota, daga k'arshema janta yay zuwa gado, ya zaunar da ita shima ya zauna, fuskarsa babu walwala yace “Munaya badai haka kikemin ganganci da yaraba?”. A tsorace ta girgiza masa kai idonta Na cika da kwalla, “wlhy yalla6ai a'a, yanzu ma Na shafa'ane”. Taune lips d'insa yay tayi yana kallonta, haushima ya hanashi samo amsar bata, jima yake kamar ya maketa, anya zaibar yarinyarnan zuwa wani wankan banza can, taje tamasa wasarere da yara?. Yanda ya koma duk saitaji babu dad'i, shi yaronma bafa kuka yakeba, yad'an dai firgita ne kawai yay kamar zai shid'e. Saida ya gama cikarsa da batsewa sannan yay kwafa, ita shima abin yabata mamaki, shikenan yanzu y'ay'ansa kawai ya Sani, mutum bazai ta6a iya kuskure ba a Kansu saiya hauma mutane bala'i, shin ya fita sonsune itada tasha wahalar d'aukar ciki da haihuwa?. Kwantar da yaron yay yanata wani had'e fuska, itama tasha kunu ta shareshi. K'aton akwatin dake gefensu ya matso dashi, kayane Na jinjirai masu k'yau da birgewa, Wanda kallo d'aya zaka musu Kasan Na musamman ne, kala-kala ne amma kowanne set uku ne, abinda ya banbanta su wannan Na macene wannan Na mazanne. kowanne da takalma abindai masha ALLAH. tsaf Munaya ta gama gani, ta kallesa tana fad'in “Sunyi k'yau”. Yana basarwan nan tasa yace, “wanda zakuyi amfani dashi gobe ne, idan akwai abinda bai yiba saiki fad'a da safe a nemoshi, ga naki nan kema”. ‘yay maganar yana nuna mata d'ayan akwatin’. Jawowa tayi ta bud'e, duk an d'inka kayan, kayane masu tsadar gaske Na mace y'ar gata, bama tasan ta rungumeshi ba Dan dad'i, sai jero masa godiya da addu'oin fatan alkairi takeyi. Shima tuni ya manta da fushin ya rungume kayarsa yana murmushi. cikin kunnenta yace, “kinfi k'arfin komai a wajena friend dan kin gamawa Muhammad Sameer komai”. Munaya ta murmusa tana d'an dukan k'irjinsa, tace, “kana shamin k'amshin ne nagama maka komai?”. Hannunta ya rik'e yana murmushi, yamatso da fuskarsa gab da tata, murya k'asa-k'asa yace, “ke d'ince Zuma ce...... ” Harar data dalla masa ta sakashi fasa k'arasawa ya wani basar yana kashe mata ido d'aya, “dad'ina dake akwai mazurai, gaki babu k'arfi ga tsoron tsiya”. Munaya tayi dariya, “aka gaya maka banida k'arfi? kabari nakuma samun lafiya sai a gwada kwanji”. Wata dariyar mugunta Galadima yayi yace really?”. “yes” ta fad'a cikeda karsashinta. Ya mik'a mata d'an yatsansa alamar su k'ula. Babu musu tabada nata itama suka k'ula. Murmushi yaytayi saboda muguntar dayasan yana shiryawa, wadda ita Munaya bata fahimci komaiba a ciki saboda wauta.🤣 *_Washe gari_* Ta kasance safiyar

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});