Chapter 45
Chapter 45
Munaya Nada dalilinta na yarda da auren su na Contract? Mi Muftahu ya Sani gameda Munaya dahar ya d'anata a gareshi a matsayin tarko?, bayan shi yana nan yana ik'irarin yima Muftahu tarko da auren Munayar. Lallai kan yakula itama Munaya da 'Yar uwarta da Muftahu suna Neman zame masa RAINA KAMA. Baifi mintuna 15 ba da tura sak'on da Munaya tayi, saiga Munubiya ta kirata, duk Galadima yana kallo daga camera d'insa da kuma saitin wayarsa, dukda kuwa yana office ne, Munaya bata d'aga kiranba, saida ya katse sannan ita ta kirata, munubiya na d'agawa Munaya race, “Sweetheart kinga sak'ona kuwa?”. “Na gansa sweetheart, amma fa ni duk kin rikitani, kinga wata alamace data tabbatar miki ahalin Galadima ne?”. “Munu, tabbas alamomi da yawa sun nunamin hakan, sannanfa shima yasan Alhaji Mamman k'afur fa, kuma kinga ai a takardarnan munga sunan Alhaji Mamman k'fur d'in, gashi abokin Abbanmu sosai, nifa yau wlhy abubuwa masu yawa ya fad'amin game da sirrinsa, dukda kasancewarsa mutum mara yarda, duk dai da inaji a raina kamar ya fad'amin wani yankin sirrinsane danya bigi cikina be, amma ni wlhy tausayi guy d'innan yake bani da gaske”. Munubiya tayi murmushi daga can, cikin tsokana tace, “to ALLAH yabar k'auna dai, sweetheart”. “ban ganeba, k'aunar mi zai bari?”. “keda Galadima mana, ai soyayya kan fara da tausayine”. “Mtsoow dan ALLAH muyi magana mai amfani Munu, yanzu ya kika gani, danya rok'eni ALLAH akan nafad'a masa mina Sani, nikuma ina tsoron koba akansa d'in baneba Abbanmu yake cikin damuwar, karmuzo kuma muyi aikin Baban giwa”. Ajiyar zuciya Munubiya ta sauke, ta gyara kwanciyarta tana fad'in Munaya kodai mu sanar da innarmu ne kozata bamu shawara?”. “kai amma bakida hankali yasin, sokike innarmu taci k'aniyarmu Ashe, zatace miyasa tun a farkon lamarin bamu sanar mataba, k'ilama tayi fushi, Dan nima wlhy ayanzu ina ganin munyi wauta fa”. “to komadai miye munrigada mun aikata. Yanzu mafita zamu nema, mizai hana ki rok'eshi inhar bashi bane kokin fad'a Dan girman ALLAH karya tada zancen kawai, yakuma rik'e mana sirrinmu, idan kuma zai taimakemune akan Wanda kema Abbanmu barazana da mutuwa ai kingani munsamu madafa muma, kinga dai yanda sukaso cin galaba wajen kashesa, wlhy Munaya jinake kamar kar Abbanmu su dawo k'asarnan”. “Ni kaina tsoron dawowar tasa nakeji, musamman da jiya Yakuma maimaitamin, shiyyasa kawai na Yanke shawarar mu fad'a masa, idanma ba shi bane saiya taimakemu wajen gano wanene”. “to shikenan, sai naji yanda kukayi kenan, Yaya unborn d'inmu?”. “gashi nan ya isheni da motse-motse wlhy, na k'agara ma ya fito na huta, kema Yaya namu da lafiyarki?”. Cikin tsokana Munubiya tayi dariya, “aikoya fito nanda wata shekarar Munafata wani ya Shiga sweetheart”. “wlhy na kula bakida man kai Munubiya, sai anjima”. Munaya tafad'a tana yanke wayar. Galadima daga can yay wani k'asaitaccen murmushi yana shafa Kansa da cije lips, ya koma jikin kujera ya lafe yanamai lumshe idanu. 👭 🤣Galadima Kodai-kodai🤫 ************ Muna gama waya da Munubiya na sakko k'asa, babu kowa gidan dagani sai su innarmu sai jakadiya, a falon k'asa na iskesu suna hira. Jakadiya tace, “ranki ya dad'e kin fito?”. Murmushi namata, ina fad'in “na fito jakadiya, ya k'ok'ari?”. Tai 'yar dariya tana cewa “kuke fama da k'ok'ari ai, ALLAH dai ya raba lafiya”. Bance komaiba na zauna ina gaida Innarmu ta amsa tana tambayata ya jikin. “da sauk'i” na fad'a kaina a k'asa, nace, “innarmu Abba fa? ko barci yakeyi?”. “A'a sun fita ai shida Sauban tunda safe, zasuga likitansa daga nan sud'an zaga gari”. “Oh ALLAH ya dawo dasu lafiya to, zaisha yawo kam indai fita da Yaa Sauban ne”. Dariya jakadiya tayi, tace, “ai mai sunan manya sai a hankaki, shibama ya gajiya”. Inna tace, “a baya gajiya kam, ni ai birgeni yakeyi, babu ruwansa, sai tsokana da barkwanci”. “Ai tamkar gadone abin nasu, dan mai martaba lokacin yanada lafiya, dukda kasancewarsa shugaba hakan baya hanashi barkwanci da mutane lokaci-lokaci, to hakama magajin gari yake, daga bayane shi sai nasa halayyar suka canja, yazama shiru-shiru, amma shi mai sunan manya saibai canjaba kuma”. Ina jinsu nidai bance komaiba, sai murmushi danake tayasu dashi kawai. Mun dad'e a falon har su Abba suka dawo, masaukinsu ya wuce, Sauban kuma ya zauna muka cigaba da hira, tashi innarmu tayi tabi bayan Abba. Sauban ya mik'e yana cewa zaije ya watsa ruwa, itama sai jakadiya tashiga domin nunawa kuku abinda zai dafa, ganin haka natashi na nufi masaukin su innarmu. Nakama handle d'in k'ofar zan murd'a tareda yunk'urin sallana sainaji muryar innarmu kamar tana kuka, “Haba Abbansu dan ALLAH ka sanarmin damuwarka, Yaya kana cikin matsala amma ka gaza fad'ama kowa?, tunda tafiyarnan tamu ta gabato ina lura dakai baka ko barcin kirki, sannan inajinka kana sambatu cikin mafarki jiya da asuba akan kozasu kasheka bazaka bayarba, shin wai minene? kuma su waye?, nidai tun bayan haihuwar su Munubiya na fuskanci kana cikin wata damuwa, amma kullum cikin k'ok'arin 6oyewa kake, bansan minene kake 6oyewarba, haba Auwal, a tunanina yanzu munzama irin d'ayan da bazaka 6oyemin matsalaba kowacce irice, a nawa tunanin munkai bigiren raba farinciki ko sa6aninsa, ko kasan ranar da muka fita da dasu Samha naga lokacin da wani bak'in mutum yazo kuka ke6e gefe, kana kuma magana tsakaninka dashi cikin fushi”...... A rikice naji Abba ya katseta da fad'in Ai'sha kenan ido kike sakamin ban saniba?, dan kawai kin ganni da mutum saiki fassara da wani Abu, Toni banma sanshiba, dan kawai ya ganni bak'in fatane shine yake tambayata, amma daga hakan babu komai, tunba yanzuba kikemin tambayar mike faruwa ina baki amsa babu komai, miyasa bazaki yarda babu komai d'inba, ni nama matso da tafiyar tamu baya, dan doctor yakuma tabbatarmin da babu wata sauran matsala, ki sanarma Munaya ta sanar da mijinta gobe zamu koma kawai”. “gobe kuma Abbansu?”.. A fusace yace “eh!”. Ni kaina saida na razana da tsawarsa naja baya daga jikin k'ofar, da sauri nabar wajen jin alamun za'a bud'e k'ofar, tabbas akwai abinda Abbanmu ke 6oyewa da gaske, to wanene bak'in fatar da innarmu tagani tare da Abba ranar? a ranar tare dasu muka fita, saidai sun rigamu tafiya, saboda ni da Galadima mun biya asibiti wajen awo, saida akamin sannan mukabi bayansu, kenan kafin muje abin ya faru? dan tabbas na tarar Abba baya cikin walwalarsa, harna tanbayesa ko jikinsa ne? Amma yacemin a'a kansane kawai ked'an ciwo. Bansan na iso bedroom d'inmu ba saboda zirfi danayi a tunani, ko hawan benen ma bansan nayoba, juyowa nayi da sauri saboda jin an kama hannuna. ganin Galadima saina rajaza zanyi baya, da sauri ya rik'oni da k'yau yana fad'in “Nutsu mana”. Da k'yar na tattaro nitsuwa ta, shikuma ya zaunar dani gefensa, hawayrne suka shiga ziraromin a kumatu, Abbana yana cikin matsala, amma wani dalili ya hanashi fad'a, takai har inda yake jiyya ana bibiyar rayuwarsa kenan?. Ido Galadima shidai ya zubamin, bai hanani kukanba baikuma tambayeni dalilin yinsa ba, kusan 5minutes sannan ya kwanto da kaina jikinsa, jina a k'irjinsa saina fashe da sabon kuka, nanma k'ala bai ceminba, yadai cigaba da bubbuga bayana alamar lallashi, saida nayi mai isata nayi shiru sannan ya d'agomin kaina, dukkan kumatuna ya rik'e cikin tafin hannunsa, Kafin yay k'ok'arin saka idanunsa cikin nawa, cikin k'asaitacciyar muryarnan tasa mai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92