Chapter 22
Chapter 22
ya kalla yana fad'in “kona kwance miki igiyar ne?”. Sakin rigar nai da sauri ina share kwalla, cike da tsiwa nace “aini ba 'Yar iska bace ba”. Shikuma cikin gatse yace, “amma kikayi ciki?”. Hannu na aza akaina nakuma fashewa da kuka, “wlhy koma mi za'ayi sai dai ayi bazan haifi wannan cikinba, aiba haka mukayi da kaiba, kawai daga auren Contract sai aganni da ciki? ka tabbatar saina zubar dashi yau d'innan, dan bazanje gidan miji da agola ba, ba kuma zan haifi d'ana Na bari gidan wani ba matar uba ta kashemin”. Da k'yar ya iya danne dariyar dake k'ok'arin kufce masa, yay saurin cafko hannuna saboda zaburar danayi xan fita. “k yi ahankali karkimin asarar abin cikin kwan fa”. Wani bak'in cikine ya turnuk'omin, Na harzuk'o masa da masifa amma saiya wani tsare gida, dolena Na had'iye maganar nacigaba da kukana. Shikuma ya watsa mini harara yana jan tagwayen tsaki, sannan yaja da baya yakoma bakin gadonsa ya zauna. Durk'ushewa nayi saman carpet d'in gaban gadon Na fashe da kuka mai tsuma rai ina rok'onsa. “dan girman ALLAH ka kaini a zubda cikinnan, kafa tuna da Girman alk'awari, a auren yarjejeniyarmu babu wannan, aikin had'in guywa ka nemeni muyi, kaifa ka tabbatarmin da zaka kasance mai cika alk'awari aranda Na kwana biyu a masarautarnan, miyasa yanzu zaka kasa cikawa? kacemin a matsayin kuskure abinda yafaru ranar ya faru, dukda zuciyata Na cike da bak'in cikin faruwar tasa haka Na hak'ura Na danne Na yarda dakai, ka taimakeni mu rabu cikin salama batareda d'ayanmu ya cutuba, karka k'ask'antar da rayuwata saboda kana ganina mace kuma talaka wadda take k'ark'ashin mulkinka, kamin adalci Dan girman ALLAH Muhammad Sameer”. Tunda munaya tafara magana Galadima ya tsaya daga k'ok'arin fara shafa man da yakeyi, idanunsa ya tsura mata, dukkan maganarta ta shigesa, dukda yana k'aunar cikin dake jikinta shima baiso gudan jininsa yazo ta wannan hanyar da babu soyayya tsakaninsa da mahaifiyar d'ansa ba, sai dai wayonsa ko dabararsa bazai ta6a canja k'addararsu ba shi da ita. da k'arfi ya cije lips nashi tamkar zai hudasu da hak'ori. Ya mik'e tsaye yana mai fidda huci mai zafi, takawa yay zuwa jikin window n d'akin, ya zuge labilan yana kallon waje, bayi keta kaikawonsu hankali kwance, dukda kasancewar rana ta take. ya maida labilan ya rufe Yakoma takowa tsakkiyar d'akin yana fad'in “tabbas ni Muhammad Sameer mai cika alk'awarine, kuma dukkan alk'awarin Dana d'auka miki ina k'ok'arin cikasu, sai dai nayi kuskure d'aya a cikin AUREN YARJEJENIYA, Na manta da babbar rahamar da ubangiji yake shinfid'awa ga dukkan wasu ma'aurata dazasu iya killace Kansu a matsugunni d'aya, Na manta da ko babu aure tsakanin mace da namiji inhar zasu kasance waje d'aya shaid'an yakan iya zama Na ukunsu ya sakasu aikata sa6o, balle mu da Muke ganin akwai igiyar aure a tsakaninmu, gaskiya kika fad'a, munyi yarjejeniyar aure domin gano mak'iyanmu bata zama Abu d'aya ba, amma kuma sai bamu d'auki matakan dazamu nisanta kawunanmu ba, daga ni har ke bamu Isa hana ubangiji ikonsa ba akanmu, tabbas ALLAH shidane bada gangan Na kusancekiba a wancan lokacin, sannan bansan ciki ya shiga jikinki ba, to mizaisa kizo ki titsiyeni kina min bore akan zubda shi. Bara kiji Na tabbatar miki yarinya, koda ace ta hanyar aikata zina Na Samar da wannan cikin inason abuna, kuma baza a zubarmin ba, ballantana sadaki Na biya d'unbin mutane suka shaida ke matata ce, mu uku kad'ai mukasan da wani Auren Contract. Dan haka kima nutsu idan zaki nutsu, kamar yanda kikace Duk abinda za'ayi saikin zubar da ciki ko? to Nima duk abinda zai faru saidai ya faru, babu ubanda ya Isa yasaka a zubar da cikinnan, sai dai idan Wanda yabani ne ya kar6a banida ikon hana wannan, idan kin gadama kici gaba da duk abinda kikeso har k'udirin zubda cikin, ni kuma Muhammad Sameer ina mai miki rantsuwa da ALLAH saina nuna miki ainahin color d'ina”. ‘ya k'are maganar da buga yatsunsa biyu suka bada sautin d'ass! d'ass!! A saitin fuskarta’. Fita munaya tayi da gudu daga bathroom d'in tana kuka, ahaka ta isa bedroom d'inta ta fad'a saman gado. Shi kuma tana fita yaja wani wawan tsaki ya fad'a kan gado yana dafe kansa dake sara masa. ga wata yunwa dake cinsa, shi saima yanzu ya tuna ko breakfast basuyiba suka fita, tsaki kawai yaja yana jawo wayarsa. number Nuren ya kira, bugu biyu ya d'aga yana tsokanarsa da fad'in “ho angon k'arni”. Galadima ya danne 6acin ransa, dan baya buk'atar kowa yasan wannan matsalar data kunne kai tsakaninsa da Munaya, muryarsa a sake yace “kun gama ne?”. “eh mun kammala, saidai kuma baka fad'i dawa-dawa za'ama visa ba cikin 'yan gidan nasu?”. Ya cije lips nashi yana gyara kwanciya, “tokai dawa yaka mata kake ganin zasu tafi?”. “eh, indai tanine gaskiya yakamata ace cikin k'annensa d'aya yaje, sai kuma mummynsu gimbiyarmu itama, tunda kaga itace first wife nashi”. “Okay hakan yayi, zuwa dare sai muje gidan muji yanda zasuyi, nasan kai dai bazaka shigo nanba, please kabama Sauban Abinci ya shigo mana dashi, dan ko breakfast My mata batayi ba”. “kai brother amma wannan sakacine ai, gashi ba ita kad'aiba?”. “wlhy Na mantane, saboda kaga ai yanayin da take tun barinmu gidan, inaga zanma inno magana a bamu mai abinci kawai”. “hakan zaifi kam, bara Na bashi ya taho yanzu kawai, amma zuwa anjima fa saika fito mun had'u”. “okay babu damuwa”. Yana yanke wayar kiran papi Na shigowa, fuskarsa d'auke da murmushi yay picking. cike da girmamawa yace “ran papinmu ya dad'e tare da k'yak'yk'yawan aminci”. “tunda kamin laifi fa ai dole ka faramin da dad'in baki”. Murmushi Galadima yayi har sarki Abdul'fatah na jiyo sautinsa, yace “a gafarceni ranka ya dad'e. ina fatan kuna cikin k'oshin lafiya kaida inno da dukkan ahalin masarautarka?”. “Alhmdllh Muhammadu. sai kuma wasu k'yawawan albishir suka riskemu a wannan rana. to ALLAH ya inganta, ya sauketa lafiya, shi kuma mahaifinka ALLAH yaci gaba da d'orar da lafiyarsa”. “Amin ya rabbi ranka ya dad'e ”. “Muhammad mikuma ya faru da sirikinka haka mara dad'in ji?”. “humm, ranka ya dad'e bansan miya sakoshi cikiba shi kuma?”. Murmushi mai sauti papi yayi, ya gyara zamansa akan kilisarsa, cikin nuna kulawa yace, “akwai abinda bamu saniba ne kawai, amma a fiddashi daga k'asar kafin mu fara wani yunk'uri”. Kamar Galadima na gabansa yashiga jinjina kansa, “to insha ALLAH zuwa gobe da daddare idan ALLAH ya kaimu zasu wuce". “hakan yayi, aci gaba da hak'uri dai kaji Muhammad, hak'uri jarine, jarabawa kuma tsanice ta zuwa wajen nasara, ALLAH yayi muku albarka”. “amin ranka ya dad'e, nagode sosai”. “yaushe zaku shigo?”. Murmushi Galadima yayi, hakan yana nufin kakansa nason ganinsa kenan, a ladabce yace “dasun tafi insha ALLAH ”. “ALLAH ya kawoku lafiya”. Tunda suka katse wayar saiyayta sauke ajiyar zuciya, koba komai ya sami nutsuwa akan wayar dasukai da papi. tashi yay ya k'arasa shafa man, sannan yasaka kayan da bazasu takurashi ba. Falonsa ya fito, abinda ake nunawa a tv ya d'auki hankalinsa sosai, ana cigiyar d'iyar Minister Ce, wai an nemeta an rasa tun a daren jiya. Akan la66ansa ya furta “Nuren!” Sai kuma yayi murmushi kawai ya kwanta saman doguwar kujera. A haka Sauban ya shigo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92