Chapter 20
Chapter 20
“Momma bama Abie wayarnan”. Cikin tsokana tace, “nawa zaka biya? kasan mu yanzu komai Na kud'ine”. Sosai yasaka dariya, har jerarrun hak'oransa Na bayyana. Dogaransa duk sun saki baki suna kallonsa, duk da bajin maganar da yake sukeba, tunda suke da shi basu ta6a ganin yana dariya makamanciyar wannan ba, Sauban kan ai hotuna yaketa masa bai saniba. “shikenan Momma, inhar baki had'ani da Abie ba kema kuwa d'iyarki bazata dawo India ba ashe?”. “a'a miyay zafi? indai takawa ne gashi”. Nanma dariyar Galadima yayi, Abie da tun d'azu yaketa murmushi shima saboda a Hans free momma tasaka wayar duk sunaji, a hankali yace Daddyn Unborn!”. Galadima baiji mi Abie ya fad'a ba, amma tabbas yana jiyo alamun motsi, da sauri yace, “Momma video call please ”. Mota ya bud'e ya shiga, Sauban ma ya k'araso dan kuma taya d'an uwansa murnar k'aruwar daya samu. tunda aka bayyana maganar cikin Galadima bai samu Kansa ba, balle su ke6e. Motar yashigo shima, ganin video call Galadima ya had'a dasu Momma saiya matso kusada shi sosai yana d'aga musu hannu. Momma tace, “ho autana ina ka shige wai?”. “momma ina zaki ganni nazama Abban Unborn”. Dariya sosai suka sanya, Galadima ya rankwashi kansa. Wayar aka saka kusada Abie sosai, a hankali yace, “lallai wad'annan iyaye akwai zumud'i dai”. Basuji miya fad'aba. Amma sungane ta hanyar motsin la66ansa. cikin zaro ido Sauban yace “Abie!!”. Sai kawai ya rungume Galadima ya fashe da kukan farin ciki. Humm masu karatu, nabama kowa damar k'iyasta wannan farin cikin a zuciyarsa shima😁😉. ★*★★*★*★★*★*★★*★ A lokacin da Galadima suke can suna waya dasu Momma Munaya ta farka, doctor Farida ta cire mata k'arin ruwan danya k'are. Ta kalli doctor Farida tace “doctor Abbana fa? karki cemin dai Abbana ya mutu Dan ALLAH?”. Hannunta doctor Farida ta rik'o, fuskarta d'auke da murmushi tace, “gimbiyarmu Abbanki nanan da ransa, insha ALLAH kuma zai tashi, kedai kici gaba da masa addu'a kinji”. Kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, “to zanyi fitsari”. Doctor Farida ta amsa da to, da kanta ta taimakama Munaya tashiga bayi, fitowa tayi tabata waje, saida ta gama sannan ta kuma taimaka mata ta fito. “doctor 'yan gidanmu fa?”. Murmushi Dr Farida tayi, cikin tsokana tace, “Gimbiya Galadima yakamata ki fara tambaya ai”. Murmushi Kawai Munaya tayi, amma batace komaiba, Dr Farida tace “to bara Na musu magana”. Babu dad'ewa saiga 'yan gidanmu nata shigowa, yanda kowanne fuskarsa ke a washe sai suka bani mamaki, nakasa hak'uri nace, “Abba ne ya tashi? kuke farin ciki haka?”. “shima insha ALLAH zai tashi 'Yar albarka”. Cewar innaro tana dariya. Ni duk sun kuma d'auremin kai da addu'ar da sukeyi suna fad'in ALLAH ya inganta. Mamansu Fauziyya tace minakeso akawo min naci. Nace, “banajin yunwa mama, ni sonake ma Na kuma ganin Abba”.. “karki damu, Abba yana barci ne, kedai kisamu kici abinci babynmu yak'ara k'ato kafin ki haifo mana”. Ban fahimci maganar ta Fiddausi ba, Dan naga awajen akwai masu ciki da yawa, aunty Ramlah, aunty Khaleesat, aunty Hauwa'u, Siyama, Zarah, aunty Raihana duk cikinsu ya tsufa, haihuwa yau ko gobe. Na kalli innarmu dake tsaye batace komaiba, murmushi namata, itama saita mayarmin, nace, “wai har yanzu Munuhiya ba a cire mata ruwanba?”. Mama Rabi'a tabani amsa da cewar “an cire, barci takeyi”. Cikin marairaicewar murya nace “ALLAH sarki Sweetheart d'ina, ALLAH yabaki lafiya”. Duk suka amsa da amin. Doctor Farida tashigo tana sanar musu ga Galadima nan zai shigo. 'Yar rige-rigen fita iyayena suka farayi, kowa yana jin nauyin suruki ya shigo ya iskeshi, ni dariyama suka bani, nayi murmushi ina komawa Na kwanta. Saida suka fita kaf sannan nafara jiyo takun takalminsa. Idanu Na lumshe kamar mai barci. Tunda ya shigo idonsa Na kaina, yacigaba da takowa gaban gadon, duk tunaninsa barcin gaske nakeyi, maimakon ya zauna saiya dafa gadon ya rankwafo kaina, da sauri da sauri zuciyata tafara bugu saboda kusantoni da ya keyi, fuskarsa daf da tawa tamkar zai had'e bakinmu, mikuma ya tuna saiya janye ya maida saitin goshina ya manna min kisses guda biyu a goshi da saman hanci. Cikeda mamaki Na waro manyan idanuna, kallon ido cikin ido mukaima juna, ya d'aga min gira d'aya. Saurin kauda idanuna nayi gefe. Shikuma yaja kujera ya zauna dab da fuskata yana murmushi. Munja wasu seconds sannan yasaka hannunsa bisa kumatuna ya juyo da face d'ina inda yake, kin bud'e idona nayi Na kallesa, bai damuba yace “yalla6iya dama haka kike da saurin cafke Abu?”. Babu shiri Na waro idanuna kansa, nace “yalla6ai mina cafke?”. Idanunsa ya d'an jujjuya alamar tunani, saikuma ya kalleni, har yanzu hannunsa Na tallafe da fuskata, yace “uhuumm mima kika cafke? Na manta ma”. Ya k'are maganar da d'age kafad'a yana ta6e baki. d'an hararsa nayi ina tura baki, mutuminnan ya iya rainin wayo. Yanzunma murmushin yamin, saikuma ya d'ora hannunsa saman shafaffen cikina mai kama da babu ko kayan ciki balle kayi tunanin akwai mutum. Da sauri Na rik'e hannunsa ina fad'in “ yalla6ai lafiya kuwa?”. Cikin basarwa yace “itace ta kawo haka, bakimin murna ba”. Nace, “Murna kuma? tami?”. Cikin d'age gira d'aya yace “Muhammad Sameer Saifudden yazam pah-pah”. d'auremin kai maganarsa tayi, Na yunk'ura a hankali zan tashi, mik'ewa yayi ya taimakamin Na zauna yana fad'in “yi da kula karkima jama'ar gari 6arna, dan akwai sarkinsu anan”. Waige-waige Na farayi, nidai banga kowa ba bayan mu biyun dake zaune, saina d'auka da kansa yake, na d'an ta6e bakina kawai. Shima saiya ta6e bakin yana komawa ya zauna. kusan mintuna biyu duk mukai shiru. Zuwa can nace, “nikam dai na dawo normal, kace musu su sallameni kawai”. Batare daya d'agoba yace “nafi buk'atar hakan, mi kikeso Sameer yamiki k'yauta da shi?”. “k'yauta kuma? akanmi?”. “Abie ya fara magana”. Babu shiri na wuntsilo daga gadon ina fad'in da gaske?”. Da sauri Galadima ya ruk'oni, jikinsa har rawa yakeyi, jina nai kawai bisa cinyarsa. “yalla6ai!”. nafad'a cikin zaro idanu, sai kuma na hau waige-waigen kar wanifa ya ganmu. Daf yamatso da fuskarsa kusada tawa, numfashin junanmu na sauka bisa fuskokinmu, na marairaice fuska tamkar zanyi kuka, yanda yasaka idonsa cikin nawa tsigar jikina dukta mimmik'e, jikina har tsuma yakeyi, amma tsabar muguntarsa yak'i ya janye, yakuma hanani damar da zan janye nawa. A hankali tamkar mai rad'a, yace “ki kula, domin abin cikin kwan yafi kwan dad'i my friend ”. ‘ ya k'are maganar da d'age min gira sama’. Lumshe idanuna nayi kozan sami sassaucin daina ganin abinda ke yawo a idanun Galadima. hakan yabashi damar d'ora bakinsa akan nawa, shima ya lumshe nasa idanun. Babu shiri na bud'e nawa saboda tsorata, ni Munaya mike damun wannan bawa yau? duk yanda naso kwatar kaina hakan ya gagara, dole na sallama yayi iya yinsa sannan ya sakeni. Zumbur na mik'e daga jikinsa ina sharar kwallar takaici, shima saiya mik'e yana karkad'amin d'anyatsa, ya matso daf dani a hankali ya furta “k'yautar farko kenan”. juyawa yay yafita yana murmushi da gyara zaman hular kansa. Na bishi da kallo ina maimaita zancensa na k'arshe, “k'yautar farko? Kamar ya k'yautar farko? mi yake nufi to?”. ban kai ga samo amsarba doctor Farida ta shigo tana murmushi. “ginbiyarmu yalla6ai yace abaki sallama kuje gida ki huta gaba d'aya”. Saboda Banason tafiyar, sai nace doctor jikina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92