Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yakan d'an tizgid'a saboda matsala data samu, shima saika k'uramasa I done zaka fahimci hakan. Innaro dai dasu Aiyaan tuni suka koma saboda makaranta, sai dai duk Hutu Galadima yakansa azo dasu Aiyaan d'in, hakama Munubiya da yaa marwan sunzo sun mana sati biyu sukaga jikin Abba da Abie. A wattani biyar d'inna Galadima yaje Nigeria kusan sau hud'u, dukda bai ta6a fad'amin wani abuba ina samun bayanai ga Saleem da sarkin Mota. har yanzu kuma Farhan d'iyar minister tana hannunsa, hakama Malam Saminu driver Alhaji Balala. Yaran gidanmu masu cikkuna duksun haihu, su Siyama an zama iyaye, naji haushin rashin halartar taron suna ko d'aya, dan dana fad'ama Galadima inason zuwa banza yamin, naci kukana kuwa na hak'ura, sai turomin abubuwan da akayi sukaitayi ina gani. Cikina ya fito kwarai da gaske, dan yanzu yana cikin wattani 7 da wasi kwanaki, yamin d'as yakuma sakani k'iba, duk kamannina sun canja, kumatuna sunyi manya, dukdai wanda ya ganni zaisan na canja, hakama Munubiya, idan ta turomin hotonta nata dariya kenan. Tsakanina da Galadima kuwa har yanzu muna a yanda kowa ya sammu, canji d'aya zance ansamu shine nuna yawan tausayinsa akan cikin jikina, dan dukkan wani motsina cikin nuna damuwarsa yake. Idan yana wajen aiki kam yakan kirani sau uku sau hud'u dan yaji lafiyata kawai. A 6angaren iyayensa da danginsa kam banida abin fad'a sai godiyar ALLAH, dan tamkar a kainane aka fara ciki haka suke nunamin kulawa. Hakan nama Innarmu da Abba dad'i, hankalinsu na kuma kwanciya sosai akan aurenmu. baba k'arami yakanyi wata d'aya ya tafi Dady kuma yazo, haka suka dingayi har ALLAH yabama Abba lafiya. Jikin Abie ma said dai muyitama ALLAH godiya, dan bayan magana an kuma samun cigaba 6angaren motsa hannunsa, yanzu kuma maganarsa takan d'an fito yanda akeji, saidai duk wannan cigaban da ake samu babu Wanda yasan dashi, har mai martaba k'aninsa, kaf masarautar gagara badau da dukkan wani makusanci bai San komaiba a kai, dan papi yahana fidda maganar, ko zuwa akai dubashi yakan komane tamkar yanda ya saba kamar da, daga mama Fulani har mai martaba sunzo kusan sau uku dubashi, hakama Muftahu da Harun, 'ya'yan Sarki ma dama suna k'ok'arinzuwa lokaci-lokaci suma. Hakama Hayatuddin Autan mama Fulani. amma babu Wanda aka bama damar sanin wani sirri akan jikin Abie d'in. dagamu sai mu kawai muka Sani. Dukda fama danake da kaina haka na dage muka cigaba da addu'oin nan, zuwan innarmu ma yakuma sakamu ho66asa saboda taimakon da take bamu, sannan muka raba addu'oin ga wasu musulmai malamai dake nan suma suka cigaba da tayamu, aka cigaba da bama Abie yanasha da wanka, doctors d'in sunyi surutunsu harsun gaji sun barmu, dan munk'i fasa masa amfani dasu, tunda muna ganin haske a lamarin sosai. A wata ranar talatar da su Abba suke shirin tafiya k'arshen satinne ina zaune a falo ni kad'ai, dan Galadima ya fita aiki tun safe, zafine ya isheni na dawo falon na k'ure AC, dan Galadima ya saka ma na bedroom d'in key saboda k'urewa da nakeyi, gashi inata fama da mura, shi kansa abin cikina ance tana Neman shafarsa. nikam bana iya hak'uri da Abu mai sanyi konasha ko AC. Sosai na baje ina kwasar dad'ina, sai faman lumshe idanu nake a cikin kujera, gama wayarmu kenan da Munubiya itama tana bani labarin halin son Abu mai sanyin datake a ciki, kullum Yaa marwan fad'a shida mama Rabi'a amma bata d'aga k'afa, data faki ido saita sha, Ayusher da dole ta dawo gidan tayata wasu abubuwan saita gani ta sanarma Yaa marwan, shikuma yay ta jarabar masifa, amma hakan bazai hana gobe tagani ta shaba........ Jinai kawai iskar dake ratsani ta daina shigata, na bud'e ido sai naga Galadima tsaye jikin k'arfen bene daya shigo ta falon ya hard'e hannayensa a k'irji ya zubamin ido ransa a 6ace, hannunsa rik'e da remote d'in ACn. Tsorone ya kama ni, na tashi zaune ina wani marmar da idanu, da hura kumatu danaketa yi, takowa yayi inda nake, idonsa tamkar zai fad'o dan hararata “k kin rainani ko? bazan hanaki Abu sau d'aya ki daina ba, ki duba muran dake damunki tun cikinnan nada wata 3, shin ke bazaki tausayama kanki baneba?”. Shiru nayi bance masa Uffanba, sai faman kumbura baki dai nake yi. “kinsan ALLAH idan baki maida wannan bakinba na kamashi saiyayi jini”. Da Sauri na maida bakina, dan ban manta muguntar da yaminba kwana biyu daya wuce, ba k'aramin morata yakeba yanzu, saboda ALLAH yabani ciki mai sakani yawan buk'ata, sai komai ya lafa nayita masa kuka, shikam ya shareni saboda shegen miskilanci da k'asaita, idan na ishesa yace zai makeni, aibashi yace na kawo kaina ba, dan haka nabar cika masa kunne da ihu, anjima ma nazo yi zaiyi tunda ba fyad'e yaminba ninake kawo kaina. Sometimes nakanji haushin furucinnan nasa, nakuma yi alk'awarin nisantarsa, amma bana iyawa, kona d'auki alwashin saina karya, da yazo yara6u jikina nake mik'a wuya, mugun tunda ya gano lagona saiya dunga bina ta wannan hanyar, duk sanda yaji buk'atata yasan yanda zaiyi ya ra6u da jikina harta kai ga wani abinda nikuma zan mik'a wuya batareda na saniba, saidaga baya nake gane kuskurena. Ganin namasa banza nak'i tankawa saiya shige bedroom yana tsaki, komawa nayi na kwanta ina share hawaye. ga zafi ya fara addabata. Kusan mintuna 19 sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa k'ananu, da Alama wanka ma yayi, k'in kallon inda yake nayi harya samu kujera ya zauna, remote ya d'auka ya kunna TV. Haka mukaita zama tamkar wasu kurame, kusan 30minutes, kiran da Nuren yamasane yasakashi d'agawa, bansan miyake fad'a masaba naga dai ya mik'e ya shiga d'akin sirrinsa. Na dad'e ina kallon k'ofar, zuwa can nima na yanke shawarar binsa kawai. Doguwar rigace yellow a jikina, batada hannu, sannan bata kaimin k'asa ba, kad'an ta wuce guywata👗, banason kaya masu nauyi saboda jin zafi, sai silifas d'in k'afata jaa mai taushi. cikinan ya kaimin ko ina, jinake kamar na jawo haihuwar na juyeshi na huta. Ciki-ciki nayi sallama, bai jiniba, hankalinsa nakan Computers d'in d'akin dayake k'ok'arin dai-daitawa, duksun kawo wuta, har k'aton glass d'in dake jikin bango guda na d'akin, ban ta6a d'aukar shima Computer baceba sai yau, dukna d'auka saboda ado aka sakashi a wajen. Sallamar na k'ara yi, ya juyo yana kallona, idonsa na cikin medical glasses mai haske, dan har kwayoyin idanunsa ina hangowa. Kamar zai shareni saikuma ya amsa mini, juyawa yayi yacigaba da abinda yakeyi, mikuma yagani saiya juyo, ya jawo kujera ya gyaramin, yay min alamar da ido na zauna. Babu musu na zauna, ya d'auki remote ya rage gudun AC d'in d'akin, sannan ya juya ga abinda yakeyi. Yanda yake sarrafa Computers d'in saiya tafi da imanina, kai guy d'innan yasan Computer over. Bansan lokacinda bakina ya su6uce nace, “yalla6ai ALLAH ya baka”. Juyowa yayi yana kallona da mamakin furucina, ya saka pen d'in hannunsa a baki yana wasa da shi, kafin ya shiga takowa gareni, k'asa nayi da idanuna nabar kallonsa, yaja kujera ya zauna kusa dani, idonsa a kan cikina, ban Ankara ba naji hannun nasa a saman cikin, idanu Na d'ago Na kallesa, ya d'agamin gira d'aya yana fad'in “ALLAH ya bani k'yautar magaji?”. Murmusawa nayi ina girgiza masa kai,

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});