Chapter 77
Chapter 77
ALLAH zakaji dalilin shigowar tamu nan gaba. game da shiga gidan nan mungama komai, maza 5 ne da mata biyu, wad'anda shigarsu ta tabbatar min suna cikin hadiman masarauta su matan kenan”. Kai kawai Galadima ya iya jinjina masa. daga nan yaymata nuni da zasu iya farawa. Da taimakon su Ameer suka shiga gidan. ★★*★★★*★★★*★★ Fitar Galadima da kusan awanni hud'u, around 2am Munaya ta farka a firgice, Inno dake zaune akan Sofa, mom da Aunty Mimi kuma a gefen gadon suka kalleta, tashi Mom tayi da sauri ta nufeta tana rik'eta, itama Aunty Mimi ta taso. Kuka munaya ta sanya tana fad'in “Mom sun mutu ko? Nasan dama kashesu zasuyi, Aunty Mimi dan ALLAH miye laifinsu su? kwanansu 7 fa kacal yau a duniya, mi suka sani game da abinda ake tuhumarsu? An durk'usar musu da kakansu, an hana mahaifinsu nutsuwar zuciya data rayuwa, shin wannan tabon bai Isa a barsu su taso da shiba a rayuwarsu? Har sai an had'a da salwantar dasu kenan?”. ta fashe da kuka maiban tausayi. Tasowa inno tayi ta zauna a bakin gadon itama, kamo hannun Munaya tayi ta kwantar da ita a jikinta tana shafa kanta, yayinda itama kwallar kebin nata kumatun. Aunty Mimi da mom ma duk hawayen sukeyi, kalaman Munaya sun ta6a zukatansu. Lallashinta da magana mai dad'i suka shiga fad'a mata, sai sauke ajiyar zuciya takeyi, ga jikinta yayi ringim da zazza6i saboda nononta sun mata hak'e-hak'e, rabonsu da shansa tunda rana, tausayinsu ya kuma kamata, tasan yunwa da k'ishi ma kawai sun Isa su k'arar da numfashinsu, hawaye masu d'umi suka kuma gangaro mata a kumatu suna sauka jikin inno dake shafa kanta. Shayi Aunty Mimi ta had'o mata, amma fir tace ta k'oshi, da k'yar inno ta samu ta lalla6ata tasha Quarter d'in kofin. Mom tace, “wannan nono kid'an matsesu kozasu rage miki nauyi, dan shine yakawo wannan zazza6in”. Bata musaba aka kawo k'aramin bowl ta matse aciki, Aunty Mimi ta zubar a bayi”.. Tanason tambayar ina Galadima tanajin kunya, sukuma babu Wanda ya sanar mata komai, kodan gudun k'ara tada hankalinta. Magani suka bata tasha takoma ta kwanta, yayinda sukuma suka mik'e duk suka d'aura Alwala suna mik'ama Ubangiji kukansu, danshi masanin sirrin 6oyene, yana kallon komai, kuma shine zai kawo iyakar komai d'in. ★★★★★★★ Duk wannan abun dake faruwa su Momma babu Wanda ya sanar musu, saidai sukaji a jikinsu tamkar akwai matsala, sunta kiran numbers amma daga wadda zasu samu a kashe sai wadda network zai hanata shiga. Sai suka d'aura ko shagalin sunan ne yakawo hakan. ******************* Tunda Munubiya suka koma gidan kuka takeyi, ko kad'an tak'i sauraren yaran da keta tsula kuka suma, balle tabasu nono. Ba itaba hatta su Ayusher dasu feena kukan sukeyi, hakama Samha harda shid'ewa, dan itama su tabi bata koma masarauta ba, Yaa marwan da mama Rabi'a ne kawai ke k'ok'arin danne nasu suna lallashinsu. Yayinda dare yay nisa duk sai suka d'aura alwala suka zo suna mik'ama Ubangijin talikai kukansu da k'ok'on barar bama wad'annan k'anan alhaki kariya da fatan ku6ta. A 6angaren gidan su Munaya kam duk hassadarsu yau dai sun tausayama gudan jininsu da yaranta, sundawo gidane kowa yana sharar kwalla da addu'ar ku6tar yaran. Ita innarsu Munaya ma ai ba'a magana, ALLAH kad'aine yasan halin datake ciki, ta shige d'aki ta rufe kanta tana jera nafilfili, dan wannance kawai gudunmawar dazata iya bayarwa a garesu akan wannan lamari mai sark'ak'iya da yawa. Abban su munaya ma yau harda hawayensa, dukda bashi da tabbas akan hasashensa yasan komai zasu iya, saboda SD yanada kusanci da wannan masarautar sosai, duk abinda ke hannunsa da bayanan daya ajiye ya shiga tattarasu waje d'aya...............✍🏻 😿Duk nisan jifa dai k'asa zai fad'o, kwana 99 na 6arawo, 1 kuma tak namai kaya.👎🏻 Fans insha ALLAH dai abuwa sun fara warwarar zare, sai mubi su Galadima muga yanda zasu dawo mana da triplets d'inmu gida😭, yau Munaya tabani tausayi daga ita har Galadima, dan shima dai dannewa kawai yake saboda jarumta, ALLAH ya rabamu da sharrin mak'iyi komai k'an k'antarsa, Harun da sauran munafukai MAZA BISA KANKU🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻🏇🏻. Barkanmu da dawowa my sweet fans🤕😡. Yau bana cikin yanayin dariya😡 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [7/16, 5:34 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻2⃣7⃣ ................Tunda suka d'akko yaran suketa kuka, musamman Abdurraheem dahar shid'ewa yakeyi, ALLAH dai yabasu sa'a ne saida suka fito suka fara kukan, neman haukatasu ma sukaso yi tun amotar, jisukai tamkar su rufesu da duka, saidai babu damar hakan, dan basuga abin duka jikin wad'annan kwad'unan yaranba. Da farko sunga kamar ana binsu, sai daga bisani ne sukaga ba haka baneba, har dai suka iso gidan y'an uku basu barsu sun shak'i iska ba. Suna shiga suka danna musu wasu allurai, cikin mintuna k'alilan jikinsu dukya saki sukayi luf. ganin lokaci yaja har kusan 10pm babu alamar wani motsi hankalinsu ya kwanta, dan sunsan dai tabbas sun tsira, wayar wadda ta sakasu aikin suka kira, amma tak'i yin picking. Cikin matan d'aya tace, “kusan dai bazata d'aga ba, saboda nasan masarauta a haukace take yanzu, saidai mubari zuwa safiya”. Tsaki d'aya yaja, “kai nifa gaskiya a tsorace nake, gara ta d'auka asan mafita, bana buk'atar gawar yarannan takwana a hannunmu, kunsanfa babansu mayene wlhy, tsaf zai bibiyemu”. “kai dalla ai yanzu bashida wannan damar, caza'ayi a fad'ama police, sukuma aikinsu zai farane zuwa safiya, kafin sannan munma gama binne gawar yaran mun kama gabanmu”..... “eh kumafa hakane”. Suna tsaka da wannan hirarne su Galadima suke shigowa, gidan k'aton gaskene dan haka suka kasa fahimtar INA zasu dosa, Galadima Yakuma danne abin kunnensa da d'anyatsa d'aya cikin murya k'asa-k'asa yake fad'in “Sauban kufara muje”. “yauwa Yaya zaku shiga hannunku Na haggu, duk sunajin maganar dan haka sukabi hannun haggu, yayinda su Ameer ke binsu a baya suma. Galadima dake gaba ya bud'e k'ofar a hankali duk suka shiga, daga can Saleem yace, “duk Ku rarrabu sir, dan abin ya nuna yaran suna ainahin tsakkiyar gidanne”. Batare da sunyi magana ba duk suka rarrabu. 'Daya acikin 6arayin yace, “kai nifa kamar motsi nakeji gaskiya”. “to sannu mai kunnen maciji”. cewar d'aya aciki. Cikin matan d'aya tayi dariya tana fad'in “nakula kaidai bibo matsoracine halan?”. Hannu ya d'aga zai kwad'eta, a harzuk'e yana fad'in “k wlhy kacaccalaki zanyi, bar ganin kinfito daga masarauta, kubadan ma an had'amu aiki dakuba kun Isa saninmu ne? jimin y'ar iskar mara kunya”. Hak'uri y'an uwansa suka bashi, ya mik'e yana jan tsaki ya fito danya duba. Galadima dake la6e cikin labule yay saurin fitowa, abinka da dogon mutum dan danan yasamu damar shak'osa ya shaka masa abin hannunsa, tun yana k'ok'arin kare kansa har jikinsa ya saki ya kwantar dashi a k'asa. Jinjina Muftahu dake kusa dashi yamasa, sannan suka cigaba da shiga. 'Dayar baiwar tana kitchen tare da wani suna iskancinsu Nuren yasamu damar sad'ad'awa, (kunsan dai shahararren kidnapper ne🤭😂) yauma tsiyar ya aikata wajen jefa ma namijin handkerchief a fuska, macen tai yunk'urin zuba ihu yasa k'afa ya tad'ota ta fad'in, sannan ya danne bakinta da ya shak'a mata itama. K'arar fad'uwarta taso fargar da sauran, dan haka duk suka mik'e suna fara lek'e-lek'e, aikam Muftahu yasamu ya tad'e d'aya ya fad'i, Ameer
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92