Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shiri, dan lokaci yana gab kenan. Galadima yay k'asa da murya batareda ya kalli Munaya ba, yace “ki shirya, shirinsu na farko d'aukewar wutar hotel d'in nan gaba d'aya, na gaba kuma shine banida tabbas. Yara dai ALLAH yana tare dasu, gakuma su Aryaan suma”.. Cikeda mamaki Munaya ta kallesa, sannan ta kalli yaran dake gabansu a wani d'an gado mai k'yau. Jikinta har rawa yake tace, “yalla6ai mi su Aryaan zasu iya? Please k.....”. Hannu ya d'aga mata alamar karfa ta ishesa yace, “wani ilimin aduhuwar daji kawai ake laluboshi, kinsan kuwa dolene a gamu da had'arurruka Aciki”. batada za6i sainyin shiru, ta kalli su Khaleel daketa wasa da abinci a teble da suke zaune hankalinsu kwance. Hawayene ya cika mata idanu, yama za'ayi wad'an can sakarkarun yaran ace suna masu bama yaranta kariya? Yaushe suka gama sanin ciwon Kansu ma balle na waninsu? gaskiya wannan gangancine kawai, tasa handkerchief ta share hawayen da ke k'ok'arin zubo mata. Duk abinda take Galadima yana kallonta. duk tausayinta saiya kamashi, ya tuna da wahalar datasha, amma bashida za6in daya wuce hakan, kuma itace tabashi k'arfin gwiwa ai, yasaka aransa ko salwanta yaransa sukayi zaiyi tawakkali insha ALLAH. Duk Wanda yake cikin shirinsu Galadima ya gama shirinsa, haka suma mak'iya masu buri a shirye suke. Gaba d'aya saura mintuna 25 atashi, saboda gabatowar sallar magrib, a kuma time d'inne Sarki Abdul-fatah da Sarki jalalludden dadai duk wani babba Wanda sukazo tare suka mik'e domin tafiya, ganin haka Galadima yama Yaa marwan sigina da ido akan ya fita da Ameen and Ameena suma, yabi tawagar su papi, dan baya buk'atar a cuta musu.. Jikin Yaa marwan a sanyaye ya d'auki yaran ya fita cikin dabara, yana kallon y'an uku, shidai dan kawai Galadima ya dagene, amma bai kamata a saka yarannan a matsayin tarko ba. Munaya ma dai ta danne zuciyarta tayi shiru, tanason bama Galadima kwarin gwiwa. Su papi na fita y'an rawar k'oroso suka fara wasa, mintuna goma da aka basu ya k'are, sai wani mawak'i ya fara nashi, nanfa y'an mata da samari aka samu nayi, dama ganin su mai martaba ne ya sakasu nok'ewa, ana tsaka da cashewa hall d'in yay d'iff, wuta ta d'auke agaba d'aya hotel d'in, mutane aka fara hayaniya kowa na k'ok'arin damk'e dukiyarsa a hannu da k'ok'arin kunna fitulun waya. Gaba d'aya jikin Munaya yahau 6ari, ta fashe da kuka tana laluben gadon da yaran suke, ruk'ota Galadima yay yasaka a jikinsa, muryarsa na rawa yace, “please ki nutsu”. “bazan iyaba yalla6ai, karsu......”. Yay saurin rufe mata baki, da tattausan tafin hannunsa..... A dai-dai wannan lokacinne kuma wutar hotel d'in tadawo. Hall d'in ya kuma kaurewa da hayaniya, zaram Munaya da Munubiya suka nufi gadon da yaran suke ciki, wayam babu komai. Munaya tayi luuu zata fad'i, saurin ruk'ota Munubiya tayi, Galadima yataso daga inda yake shima zuwa garesu. hall d'in yagama rikicewa da tsantsar hayaniyar rashin ganin yaran, sai kallon kallo akeyi. Securitys d'in da aka baza sun rikice da wannan tashin hankali, dan sune mutane na farko da za'a fara tuhuma. Rufe hotel d'in akayi aka hana kowa shiga balle fita, Galadima ya shafama Munaya ruwa ta kawo numfashi, fashewa tayi da sabon kuka ta fad'a jikinsa, hannu biyu ya saka ya rungume ta shima yana had'iye kwallar bak'in cikin dake Neman zuboma idonsa. Tausayinsu ya kama mutane da yawa, innaro harda kukanta, hakama inno, abinda yabani mamaki shine tsantsar damuwar da mama Fulani ta nuna, dan itacema tabama Galadima ruwa ya shafama Munaya ta farfad'o. Da farko Munaya ta d'auka ko Galadima wasa yake mata yasan inda yaran suke, amma ganin damuwar da yake ciki saita kuma rikicewa, dandanan numfashinta yafara gagarar k'irjinta, ta mik'e a kid'ime, dan taji a jikinta kuka sukeyi, nononta sai tsitstsirawa suke, wani jirine yafara hajijiya da ita da zuciyarta ta k'iyasta mata zafa su iya kashe mata yara, luuuu tayi baya Galadima ya ruk'ota. sume musu ta kumayi. Hankalin Galadima kuma tashi yayi, dole ya d'auki Munaya aka sakata a mota suka bar hotel d'in. Sauran mutane kam kowacce mota zata fita sai an binciketa. Yayinda Securitys d'in suka bazu ko ina na hotel d'in ana bincikawa. Gida aka wuce da munaya, har suka isa tana jikin Galadima, yanata murza tafin hannunta kozata farfad'o, har d'ora bakinsa yayi akan nata ya jawo iskar numfashinta amma a banza, hakanne yakuma tada hankalinsa. Kai tsaye d'akinsa ya wuce da ita, ya shimfid'eta a kan gadon ya cire mata alk'yabbar jikinta, Akash suka k'araso da hanzari shima, taimakon gaggawa yafara bata shida doctor jalal, cikin amincin ubangiji saigashi takawo numfashi, bama su bari tadawo dai-dai ba suka mata allurar barci. Suna fita Galadima ya cire rawani da alk'yabbar jikinsa shima, ya sassauta bottom d'in wuyan rigarsa. Safa da marwa ya shigayi a tsakar d'akin yana Mirza agogon hannunsa Wanda daka gani kasan ba normal agogo bane,. Wayarsa datai k'ara yay saurin d'auka, d'agawa yayi yasaka a kunne, “Muftahu ya ake ciki?”. Cikin hakki Muftahu yace, “komai yana tafiya yanda ya kamata ranka ya dad'e, har yanzu gamu muna bin bayansu, amma munkai inda yakamata ka fara Controlling namu, yanzu mun.......” Da sauri Galadima ya katseshi ta hanyar fad'in “karka damu ina kallon Ku, saidai kilometer's d'in dake tsakaninku dasu fa yakai 1½, Saleem da Sauban sunfi kusa dasu, dan haka ku k'ara azama. daga lokacin da suka farga da abinda nasaka jikin Amaturrahman tabbas zasu cireshi, kuma zamu rasasune gaba d'aya”. “Ok babu damuwa, ranka ya dad'e”. Yanke wayar sukayi, Galadima ya bud'e wani k'aramin akwati ya fiddo kayan aiki wanda a ready dama yagama had'a komai, bajesu yayi akan gadon kusada Munaya, ya zauna yafara Control cikin matuk'ar kwarewa. Saleem ya kira aunty Salamah wadda itama take tare dasu Ameer yaran da suka sace Muftahu, d'agawa tayi jikinta na rawa, “Saleem kuna inane?”. “Aunty Salamah gamunan bayansu kad'an, amma mund'an basu k'afa saboda na kula sunfara fuskantar muna bin su, yanzu dai haka mun ajiye motarmu mun samu mashin”. “Hakan yayi, insha ALLAH indai ta Anguwar da muke tsammanin zasu shigane kamar yanda kaji Harun d'in yay magana to tabbas mu dai mun iso, saidai suzo su iskemu, ka kira yalla6ai ka sanar masa yakamata ya fito yanzu”. “no Aunty Salamah, bazai yuwu boss yabaro masarauta ba yanzu, saiya tabbatar mun Isa, saboda dukma inda suka shiga yana bibiyarsu, dan bazai saka yaransa a matsayin tarko ba babu tsaro k.......” Tai saurin k'atseshi ta hanyar fad'in “yauwa ina zargin kamar gasunan a wata bak'ar mota sun wicemu fa”. “Alhmdllh, su Ameer Susan yanda zasuyi su bisu bara na kira boss”. “ok”. Kawai Aunty Salamah ta fad'a ta yanke wayar. Kiran Galadima Saleem yayi, bugu biyu ya d'auka, “Saleem mike faru yanzu?”. “Ranka ya dad'e gamu dai biye dasu, amma Aunty Salamah tacemin gasu tagansu”. “wacece Salamah? ”. Gaban Saleem ya fad'i, dan ya manta Galadima baisan Salamah ba, “Am sorry sir, idan komai ya dai-daita zan maka bayani”. “Saleem!!!”. Galadima ya kirayeshi a tsawace. Saida Saleem ya janye wayar akunnensa, muryarsa na rawa yace “ka yarda dani sir, wlhy itama ta kwarai ce”. Ajiyar zuciya Galadima yayi, muryarshi cikin tsantsar damuwar yace, “wannan anguwar da kuke tanada hanyoyi da yawa, dan haka Ku fara amfani da live

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});