Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Koda suna mota taita gwadawa. A asibitin suka had'u da mama Rabi'a suma sunje, ganin innarmu a cikin damuwa yasata k'ok'arin fara kwantarma 'Yar uwarta da hankali. Innarmu ta sanar mata kato6arar da Aiyaan yayi. “to Yaya ko su Munaya sunzo k'asarne?”. Anya kuwa Rabi'a, naga jiya mijinta na nan amma baiyi maganar zata zoba”. “ito da wannan dan wanann, amma ai bama fidda raiba”. “hakane”. cewar innarmu. Babu dad'ewa da zuwansu saiga gwaggon Haleematu da matan k'annen ta sunzo duba Abba, (dayake har yau bata dawoba ita). k'in gaisawa tayi da innarmu da mamansu yaa hameed, innarmu bata damuba, amma mamansu yaa hameed saida taja tsuka, babu dai Wanda ya tanka. Sukuma suka shiga suka ga Abban, dayake yau ana barin na jikinsa zuwa su duba shi. Koda suka fito harda kuka takeyi, matan k'aninta suka tafi amma ita saita zauna, kaf 'yan gidanmu babu Wanda yace mata danmi, kowama tasa ta isheshi aransa. ★★★★★ Tunda motocinmj suka shigo harabar asibitin sai kallo ya koma sama, 'yan gidanmu dakeda yak'in Galadima ne kowa tsumayen fitowarsa yakeyi, sauran jama'a kuma da 'yan dubiya son ganin wad'anda zasu fito sukeyi. Sai da aka bud'e mana sannan muka fito, suma su Harun duk sun fito. Su yaa Hameed suka taho garemu sunama Galadima sannu da zuwa, cikeda kulawa yake amsa musu. Kowannensu fuskarsa ta nuna farin cikin ganina, yayinda nikuma naketa faman zirar da hawaye. Cikin d'okin ganina Fauziyya tazo ta kama hannuna itada Safara'u, saina rungumesu na fashe da kuka, kukana ya karyar musu da zuciya suma suka fara, sauran 'yan uwanama duk suka taso gareni, dama duk sun zo, ni kad'aice wadda nake nesa. Saida baba k'arami yamana magana sannan suka sakeni, na matsa ina sharar kwalla na gaida iyayena, Munubiya ce kawai ban ganiba, ina share hawaye na tambayi tana ina?. Aunty khalisat tace “sunje ganin doctor itada yaa marwan, dan batajin dad'i itama”. Kaina kawai na jinjina, na k'arasa gabansu innarmu na durk'usa ina gaishesu, duk sun amsamin cikeda kulawa, da tambayata ya hanya?, nace “Alhmdllh”. Matan gidanmu kowacce kallona take da mamakin canjawata a cikin wata 1 kacal. Na katse musu tunani da tambayar d'akin da Abba yake. Aunty Ramlah ce taja hannuna muka shiga corridor d'in dazai sadamu da d'akin da Galadima yasa aka canjama Abba. A ciki na iske Galadima da Harun da Sauban, sai doctor da yaa Shafi'u yaa Hameed. Takun takalmanmu yasakasu juyowa suka kallemu, na zare hannuna daga na aunty ramlah ina toshe baki saboda kukan dake Neman kufcenin, taka wa nayi gaban gadon da Abba yake, na durk'ushe ina sakin kuka mai tsuma rai da zuciyar mai saurarona, tare da kife kaina jikin gadon. Kukana babu zuciyar Wanda bai karya ba, Galadima ya tako a hankali inda nake, hannayensa biyu ya saka ya kamoni na mik'e tsaye, fad'awa nayi saman k'irjinsa na kuma sakin wani sabon kukan. Bashida za6in daya wuce kar6ata, dan haka shima saiya saka hannayensa ya zagaye bayana dasu, ya d'ora ha6arsa saman kaina yana lumshe idanu da cije lips. kad'an-kad'an yake buga bayana alamar lallashi. d'ai-d'ai su yaa Hameed suka zare jikinsu suka fice daga d'akin, aka barmu mu kad'ai sai Aunty Ramlah da muka birgeta, itama ganin sun fita saita fice taja mana k'ofar. Munkai tsawon lokaci ahaka, saida na tsagaita da kukan sannan Galadima ya d'ago kaina daga jikinsa, hannunsa yasa yana gogemin hawayen fuskata, amma ya gaza cewa komai. sai girgiza min kai kawai yakeyi. Ajiyar zuciya kawai nake saukewa a jere, da hannu ya nunamin hanyar fita. Banyi musuba nabud'e k'ofar muka fito, ina gaba yana bina a baya. tafiya nake a hankali saboda juwar dake Neman fara hajijiya dani, burina kawai nakai inda 'yan gidanmu suke zaune akan kujeru nima na samu na zauna. Muna gab da k'arasawa wajen na dafe kaina, sai nayi baya luuuuuu. Da sauri Galadima dake bayanta ya tareta ta fad'o jikinsa, gaba d'aya 'yan gidanmu da mutanen wajen suka mik'e tsaye cikin ambaton sunan ALLAH. sosai Galadima ya tallafota jikinsa, yayinda wasu Nurses biyu suka iso da gudu domin kar6ar Munayar. Amma saiya hanasu yana daka musu tsawa da ambatar su kira Doctor. Basu ba kowama a wajen saida tsawarsa ta rikitashi....................✍🏼 *_Comments d'inku shike k'aramin k'arfin guywar rububutun nan wlhy, amma da tuni na ajiye saina samu lafiya🤦🏻‍♀, amma yanda kuke k'ok'arin Comments sai bana iya barinku banyiba😃, ina godiya kwarai da gaske, I love you all🥰🥰🥰🥰🥰🤝🏻👍🏻❤_* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 ~Book 2~ 👉🏻7⃣ ................Gaba d'aya ya rikice ya rikita Nurses d'in da jama'ar wajen, cak ya d'auki Munaya, gadonma da aka kawo masa domin d'orata ko kallonsa bai yiba. Wani d'aki suka nuna masa ya shiga da ita. Da sassarfa doctor dazai duba munayar ya iso, dan dogaran Galadima tasoshi gaba sukaje sukayo. Kai tsaye Galadima yace baya buk'atar namiji mace yakeso ta duba masa matarsa. Hak'uri doctor d'in ya bashi, sannan yakira wata likita mace mai suna doctor Farida. Isowarta yasaka Galadima da yay bake-bake a k'ofar bata hanya ta shiga. Duk yanda taso yabata waje tayi aikinta yak'i, gashi duk yabi yagama rikitata da tsawarsa. Doctor d'in da Galadima ya hana ya duba Munaya ne ya matsa kusada su harun yana fad'in “dan ALLAH sir Ku lalla6a yalla6ai ya fito danta samu damar aikinta, wlhy dukya rikitata”. Murmushi Nuren da isowarsa kenan asibitin aka masa bayani shima yayi, suma su harun duk murmushi sukayi. Nuren ya kalli baba k'arami yana murmushi, “Abbanmu inharfa bakai kamasa magana ba bawai zai fito baneba”. Shikansa baba k'arami murmushin yakeyi, koba komai hankalinsu Yakuma kwanciya da zaman 'yarsu inda suke tunanin anfi k'arfinta. Bayan doctor yabi zuwa d'akin, Galadima dake zaune, kan Munaya na bisa cinyarsa sai murza tafin hannunta yakeyi wai kozata farfad'o, yayinda doctor Farida ke k'ok'arin lik'a mata oxygen ita kuma”. Shima baba k'arami da k'yar ya lalla6ashi ya fito. Tsawon lokaci doctor Farida tana ciki bata fitoba. Galadima dukya damu, danma ankawo masa kujera ya zauna, amma sai jan tsuka yakeyi time to time. Hankalin 'yan gidansu Munaya ma duk a tashe yake, jiran fitowar doctor Farida kawai akeyi dan aji mike damun munayar. Innarsu Munaya kam gefe ta koma tana sharar kwalla, itakam batasan yazata misalta wannan tsakaniba, miji da 'ya'ya duk babu lafiya, Munubiya ma fa sunacan ana k'ara mata ruwa. Fitowar doctor Farida yasaka kowa mik'ewa anason jin bayani, Galadima dai yana daga zaune ya zuba mata idanu shima. Doctor Farida tace su kwantar da hankalinsu ta farfad'o, amma tamata allurar barci, yanzu tanason ayo gwajin jinin Munayar data d'iba. Galadima ya lumshe ido yana ambatar “Alhmdllh” akan la66ansa. Sauban ne ya kar6a suka tafi shida Sarkin mota lab d'in. Dr Farida ta kalli Galadima tana murmushi, “ranka ya dad'e zaka iya Shiga ka ganta yanzun”. Nuren ya kalli Galadima ya jinjina masa kai alamar yaje. Saida yaja wasu seconds sannan yamik'e cikin takun nan nasa na k'asaita da izza, duk idon jama'ar wajen akansa yake, yana birge kowa. d'akin ya tura ya shiga, ya taka har gaban gadon da Munaya ke kwance, idanu ya tsura mata, tayi wani fayau da ita, ya jawo kujerar dake wajan ya zauna, har yanzu idonsa na kanta,

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});