Chapter 86
Chapter 86
amma saiya basar tamkar bashine yayiba, nima sharewa nayi na cigaba, “bamusan miya faruba sukace Zarah da siyama sukeso, wannan Abu ya 6atama Abbanmu rai, dan aganinsa anyi wani abune domin k'untatama mahaifiyarmu, hakkane yasashi zuwa ya sanarma Baba mai kanwa, dama duk dai wani Abu dazai taso gidanmu shine ake sanarmawa, yayi sasanci koya tsawatar, koda kuwa innro ce. bayan Abbanmu yaje da kwana d'aya, sai innarmu ta aikemu wajensa muka kaimasa goro da y'ar sayayyar da takan masa lokaci-lokaci, saboda yamusu hallaci a rayuwa a yanda take bamu labari, shiyyasa a kullum take d'aukarsa uba”. Mun iske baba mai kanwa a d'akinsa na zaure kamar ko yaushe, muka gaidashi cikin girmamawa da tsokanarsa a matsayinsa na kaka, shima ya tsokanemu tareda sakamana albarka kamar yanda ya saba, saiya murmusa tareda gyaran murya, hakanne yasaka muka nutsu dan fahimtar magana mai muhimmanci zaiyi, ya nisa cikin dattako na tsufa ya fara fad'in___”. _“yarana kuyi hak'uri da damuwar da kuka tsinci kanku a ciki, wadda tunkafin Ku mahaifiyarku a ciki take, amma nasan watan watarana kuda ita duksai kunci ribar wannan hak'urin, karkuyi bak'inciki akan hanaku wannan auren da akayi na y'ay'an halluru, dama can sud'in ba mazajenku baneba, hasalima aurensu ba alkairi baneba”._. “A razane duk muka kallesa baki bud'e”. Yayi murmushinsu na manya, _“abin ya baku mamaki ko? Humm ba abin mamaki baneba, yau zan fad'a muku wani sirrin dabaku saniba, domin ina hango wani tarin alkairi tattare da rayuwarku, inakuma ji ajikina kune wad'anda zaku fidda mahaifinku daga wata sark'ak'iya daya Shiga a dalilin taimako tun kafin a haifeku. Alhaji halluru da wata manufa ya nema ma y'ay'ansa auren d'iyan mahaifinku, amma Shifa na fuskanci bai fahimci hakanba, sabo da ya aminta da amintar dake tsakaninsu ta tsawon shekaru. Alhaji halluru yanason shiga jikin mahaifinku ne sosai danya kar6ama iyayen gidansa wani sirri dake hannun Auwalu, ina k'yautata zaton shine kukaji wani Abu a ciki, shi kansa Auwalu baisan minene a ciki ba, domin kuwa bashi akai amana ya Isar dashi ga Wanda yadace, kuma baita6a yunk'urin ya duba ba ya barsa a yanda aka bashi. Kuyi hak'uri akwai wasu k'alubale dake tunkaro rayuwarku, kuma yanada tsananin sark'ak'iya, saidai insha ALLAH zan baku dikkan gudunmawa inhar ALLAH yabani tsawon ran kaiwa wannan lokacin, Ku dage da yawan sadaka kudai da mik'a lamuranku ga ALLAH mai kowa da da sirrin komai, ALLAH kuma ya cigaba da tsareku.”_ “duk cikin tsantsar damuwa muka amsa masa da amin, haka muka baro gidan jikinmu duk a sanyaye, dan har innarmu tata bincikarmu a lokacin, sai muka fake da ciwon mara. sati biyu da faruwar wannan lamari sai Munubiya tafara min k'orafin yawaita mafarkin wani bawan ALLAH, kullum takan gansa ne a cikin dokar daji zagaye da wasu irin halittu masu ban tsoro suna kaimasa hari zasu halakashi, yakanyi k'ok'arin kare kansa amma saiya gaza, idan yanemi taimakonta kuma bata zuwa, saboda tsoro suke bata. Duk sanda tafad'amin wannan mafarki sainace bata addu'a ne, shaid'anune kawai. haka taita jera wannan mafarki kullum dare, kuma da gari ya waye bazata fasa fad'aminba, tundai abin na damunmu har muka watsar muka cigaba da harkokinmu. Ranar kuma sai nima nayi mafarkin makamancin na Munubiya, saidai nikuma na shige ina taya wannan mutumin kare kansa ga wad'annan halittun kamar yanda ya buk'ata, na jigata sosai dan harnatashi jikina duk yayi week, nima ban 6oyema Munubiya komaiba na sanar mata, abin yabata mamaki, kuma tundaga sannan nima na cigaba da mafarkin, kullum kuma ina taimakon wannan mutumin dako fuskarsa ban ta6a ganiba, itako Munubiya takan cemin saidai ta tsaya kallonsa daga nesa yana bata tausayi, kuma yana shan nuna mata tazo ta taimakesa, amma saitak'i ta nok'e kafad'a. nikam a nawa mafarkin duk lokacin da ya nuna na taimakesa nakanje nashiga muyita fama da wad'annan halittu, ita Munubiya tana ganin fuskarsa, amma da zaran ta tashi, saita manta, niko ban ta6a ganin fuskarsa ba ko sau d'aya. Muna cikin halin wannan mafarki ne aka shiga bikin salla, tabbas randa muka had'u dakai a asibiti sainaita jin haushinka akan dalilin da ni kaina nasan bai isa daliliba, (dan kawai ina maka kallon mai girman kai bai kamata naji haushinka ba, tunda bawai hud'ace ta had'amuba, banikuma da tabbacin akanka abbanmu ke a had'ari), saidai had'uwarmu ta filin idi tasha banban data asibiti, dan a filin idi tsoro-tsoro mai gauraye da mamakinka ne suka zaunemin a zuciya, bayan kabani wayarka kabar wajen inata mamaki da juyata da tambayar kaina kaid'in wanene? Sai wata murya ta bani amsa da cewar *Galadima!* saidai koda na waigo banga kowaba sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya, na dad'e soaai wannan al'amiri bai bar rainaba, a haka muka shiga shagalin bikin y'an gidanmu, harda kuma su siyama, anan ne muka had'u da Fu'ad, harga ALLAH bansan wanene Fu'ad ba, bankuma San daga wace tawagar ango ya fitoba, amma amamakin kaina lokaci d'aya na aminta dashi, dukda kasancewata mutum mai masifar tsarta, cikin kwana d'aya kacal na saki jiki dashi, dukda ban amsa masa Cewar na kar6i soyayyarsa ba, daga ni harsu Ayusher bansan miya shiga kanmu ba muka yarda ya kaimu birnin gayu plaza ba, dukda kowannenmu ransa akwai fargaba, musamman ni danakeji kamar akwai wani gagarumin Abu dake tunkaro rayuwata. hardai muka shiga muka fito abinda ya faru ya faru a tsorace nake. fitowar wannan jarida a washegari yasaka dukkan wani ahalinmu a rud'ani, Wanda bansan yazan musalta makashi ka fahimtaba, lokaci d'aya da akazo bincikar wacece a cikinmu na amsa, dan jinai bazan iya bari Munubiya ta amsa laifinba, saboda tanada hak'uri, amma tanada tsauri Wanda nikad'ai da mahaifiyarmu muka San wannan tsaurin nata, dan sometimes takanyi mugunta amma tayi tamkar ba ita baceba, kai tsayema sai'a zargeni ita ba'ayi tunanin zata iyaba....” Galadima ya katseta da fad'in, “kina nufin bakece kika kusa fad'iwaba a plaza?”. Nad'an murmusa ina gyaran mayafina dake zamowa saboda kayan sunada santsi, “tabbas bani baceba yalla6ai, Munubiya ce, tausayi. Y'ar uwata yasani kar6ar laifin. Bayan wannan Abu ya faru nanma kowa yata fushi damu musamman Abbanmu, haryace saina nemo miji cikin 2weeks kacal, wannan ya d'agamin hankali, dan nikam kaf samarina babu Wanda yamin, amma sainaga kamar zan iya auren Fu'ad, wannan dalilin yasani kiransa bisa shawarar su feena, amma saiya toshe sukkan hanyar dazamu iya yin magana. bansan yazan misalta maka halin dana tsinci kaina a tsakaninba, naji natsani Fu'ad matuk'a, a wannan time d'inma na cigaba da wancan mafarkin, amma yazomin dawani sabon salo, sannan ita kuma Munubiya ta daina, mafarkin ya canjane zuwa salon da mutumin kanyi yunk'urin ta6ani, amma nakan hanashi damar hakan ta hanyar ja baya da masa gargad'i, shikuma saiya ringa rok'ona da cemin karna masa haka, ni fitilarsa ce. Har sannan kuma still bana ganin fuskarsa, abubuwa da yawa sun had'u sun dagulemin, dukna fige na fice hayyacina. A lokacin da baba mai kanwa yaje dubani asibiti bayan maganar aurenmu da haidar ta rushe saiyake magana cikin murmushi, k'asa-k'asa kuma ta yanda wani bazai jimu ba”. _“Ki kwantar da hankalinki Hussaina, har yanzu dai mijinki bai kai ga zuwaba, kuma bayan wannan ko 10 zasu k'ara zuwa saisun barki, dan akwai k'alubale a gabanki kafin kisamu nutsatstsiyar rayuwa._” “Da mamaki na kallesa, amma saiyak'i bani damar neman k'arin bayanin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92