Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 52

Chapter 52

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

d'inne?”. Murmushi yamata shima, yace “aunty akwai dad'i ma sosai, ranar saida na cinye kharan a gidansu ma”. “da gaske?”. munaya tafad'a tana dafa kafad'arsa. Kansa ya d'aga mata, cike da d'oki yace, “Aunty na koya miki?”. Munaya ta d'aga masa kai. Game d'in ya d'ora a cinyarta, ya danna wasu Number, sai kuma ya zubasu cikin d'aya, duk suka shige. Cikin mamaki munaya tace “mikenan to?”. Shima dariyarsu ta yara yayi, yace “Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'ayane, amma sainayi ammafani da numbers daban-daban, kuma kowanne a cikinsu aiki d'aya yayi na canja da wani, kekuma zakiga kamar na had'a daban-dabanne, kuma kowanne da aikinsa, amma aiki d'aya ne na had'aka kuma akan Abu guda d'aya kacal”. Sosai abun ya birge munaya, tayi dariya har hak'oranta na bayyana, jawo yaron tayi a jikinta ta rungume. Iyayensa dake tsaye suna kallonsu tun d'azun duk sukayi dariya suma, sannan suka matsa kusada munaya suna bata hannu alamar gaisuwa. itama ta mik'a musu suka gaisa, d'aya tace sunanta Radha, d'ayar kuma tace Anjali, munaya ta fad'a musu nata suna itama, sannan takamo hannun saran yaran tana tambayarsu suma, d'aya yace vanish, d'ayan kuma Anjun, duk kumatunsu ta sumbata tana sakama rayuwarsu albarka. Wadda tace sunanta Radha tace “kiyi hak'uri da surutun Vishnu shi baya gajiyane ko kad'an”. Munaya tace babu komai. Daganan sukai gaba, munaya tana binsu da kallo tana murmushi, yaran sai waigenta suke suna d'aga mata hannu. Sunje wajen biyan kud'i akace subar kud'insu inji mai shagon, da mamaki suka tambayi wanene? Mikuma yasa ya barmusu. Mai kar6ar kud'i ya murmusawa yana fad'in mijin matarcan da kuka gaisane mai shagon ai. Munaya batasan mike faruwaba taga sun dawo, godiya suka shiga yimata, ta tambayesu akan me?. Suka bata amsa da cewar mijinta bai kar6i kud'in kayansu ba. Murmushi tayi, k'asan ranta tana mamakin dama shagon na Galadima ne?. Sun katse mata tunani da tambayar kozasu samu number ta, babu musu tabasu sukayi sallama suka tafi. Maida kallonta tayi ga Galadima dake zaune yanata latse-latsen laptop tamkar baisan mike faruwaba, da alama yana duba kayane ko wani Abu, dan time to time Wanda yake gefensa yakan nuna masa wani yanki na kayan dake shagon, shikuma ya waiga ya kalla, idan bai hango sosaiba saiya kalla ta cikin Computer d'in dake tareda cctv cameras d'in shagon. Munaya tace kai mutuminnan akwai son kud'in tsiya, kai komai kana saidawa, wata zuciya tace idan bai nemi kud'iba dame zai kula da mahaifinsa?. “hakane kuma”. ta fad'a a fili tana sauke ajiyar zuciya. Kusan mintuna 15 saitaga ya taso ya nufota. Zama yay kujerar kusa da ita yana fad'in “sorry friend na barki ke kad'ai. kin gaji mu tafi ko?”. Munaya tad'an yamutsa fuska tace “ba sosaiba”. Ya d'an murmusa, “ok tunda baki gajiba kozaki d'an mana taimako ni da abin cikin kwan?”. Hararsa tad'anyi, itafa haushin wannan abin cikin kwan dayake fad'a takeji. Hannu yasa ya dafe bakinsa yana fad'in “maida wuk'ar”. A tare suka dinga zagayawa cikin shagon, dayake babbane sosai, kayan yarane kuma zalla a wajen, komai bibbiyu take d'auka, baice komaiba, dan yasan dai bai wuce tana had'awa da cikin 'Yar uwarta Munubiya bane. Sund'an d'iba kaya babu laifi, yabada ATM d'insa aka d'auka harda na wad'ancan matan, yaran shagonne suka kai musu har cikin mota. Yanzuma haka suka taho tamkar kurame. Kowa da abinda yake sak'awa.... Danja data tsayar damune yasakashi juyowa yad'an kalleni, ganin hankalina nakan wasu yara 'yan makaranta dake mota yace, “dama haka kike da son yara?”. Juyowa nayi Na kalleshi, amma saiya d'auke kai tamkar bashine yay maganarba ma. Nima maida kaina nayi ga yaran, a kuma time d'inne muka sami damar barin wajen. Saida muka fara tafiya nabashi amsa da “yalla6ai kenan, waye zaice baison yaro, a duniya babu abinda yafi k'uruciya dad'i”. Kad'an ya juyo yad'an kalleni yana fad'in “really?”. Nima kallon nasa nayi ina fad'in “na tabbata amsarnan kowama zai baka idan ka tambayesa”. Bai kalleniba yanzun kam, hankalinsa naga tuk'insa, yace, “ALLAH ya kawoka duniya lafiya abin cikin kwan”. “shiru namasa bance uffanba”. Har muka isa gida kuma babu Wanda ya sake magana a cikinmu. Saida yay parking motar a harabar gidan sannan ya juyo gareni, ina niyyar bud'ewa Na fita ya ruk'o hannuna. kallonsa nayi da mamaki, yawani ci magani irin babu raininnan, kamar zanyi magana saikuma nayi shiru muka zubama juna ido, kowannenmu zuciyarsa Na bugawa da sauri-sauri. Cikin k'asaitarnan tasa yace, “Addu'a nayi amma jan aji yahanaki amsamin da amin”. Ni dariyama ya bani wai jan aji, hakanne yasakani murmusawa kad'an ina k'ok'arin janye idona daga cikin nasa, amma saiya hanani hakan, nace, “na amsa ai, bakaji bane kawai”. “aiba kurma kika auraba”. Uhm wannan aure ana tak'ama dashi, Na fad'a a raina, a fili kuma nace, “a zuciya Na amsa”. “k'arya haramun, banji wannan sak'onba a tawa zuciyar”. Da mamaki Na waro idanu waje ina fad'in “ban fahimceka ba”. Lips d'insa yad'an ciza da hak'ora yana matsoda fuskarsa dab da tawa, gashi ya sark'eni da idanu nakasa matsawa, d'an yatsansa ya d'ora saitin zuciyata, muryarsa k'asa-k'asa tamkar mai rad'a yace, “zuciyoyi aminan juna sukan kar6i sak'on juna alokacinda d'aya ya aikashi ga d'aya, karki jahilci kanki har yanzu akwai sauran dama”..... Yana gama fad'a ya saki hannuna, tareda bud'e motar ya fice. Galala nabisa da kallo tamkar wata sokuwa, nakasa motsi nakasa fassara zantukansa da ma'anarsu. Tsawon mintunan dahar bayin gidan sungama kwashe kayan da mukazo dasu ban fitoba, bud'ewa naji anyi, hannunsa kawai ya mik'omin alamar nakama Na fito. tamkar sokuwa haka Na d'ora hannun cikin nasa, ya kamoni ahankali Na fito, maimakon ya sakeni saiya jawoni Na shige jikinsa, ya d'ora kansa a dokin wuyana, cikin kunnena yace “wasu bayanan basa buk'atar fassara, ayanda sukazo ahaka ake barinsu, karki zurfafa tunani, dan yana kawo ciwon kai da hana Hutu”. Ya d'ago kaina tareda janye jikinsa yana d'agamin gira da salute d'ina, ya juya zuwa cikin gida. Binsa kawai nakeyi a baya tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki. A falo muka iske duka ahalin gidan, har Momma dazata kwana yau a gida, Abba ne kawai babu, muduka sun birgemu, Dan hira suke ta nishad'i da girmama juna. Dagani harshi gaishesu mukayi, Sauban da Samha dasuka k'arasa da kayanda da bayi suka shigo dasu suka sakko daga samanmu suna mana sannu da zuwa. Ni kad'ai Na amsa, Galadima hannu kawai ya d'aga musu. Momma tace, “kuje ku huta mana”. mik'ewa mukayi duk a kunyace, ina gaba a yanzu yana baya, suduka da kallon sha'awa suka bimu, dad'i da farinciki Na ratsa zukatansu, innarmu harda kwalla suka cika idonta, Wanda ita kad'ai tasan fasaarar kayanta. ★★★★★★★ Da daddare Galadima Na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda Munaya ke zaune a tsakkiyar gado tana karatun wani English novel na Galadima, buk d'in love story ne dan haka taketa faman zabga murmushi, lokaci-lokaci yakan d'ago ido ya kalleta, saboda idan tayi murmushi yakan jiyo sautinsa. Maida kansa yayi, yacigaba da aikinsa dayakeyi akan numbers d'in layin Abba na sirri, kwatsam sai maganar yaron d'azu na shago mai suna Vishnu ta fad'o masa a rai. *_Aunty ai wayo na miki, Abu guda d'aya ne, amma sainayi amfani da numbers daban-daban, kuma kowanne

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});