Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gidan sagani. Abin nema yasamu fa, yaa marwan tamkar zai maida Munubiya ciki, kokuma ya maido cikin nata jikinsa yarage mata wahalar laulayi haka yakeji, Dan tana d'an shan wahala gaskiya. ko girki yanzu bata iyayi balle gyaran gida. Hakanne yasaka mama rabi'a cewa yadawo da Munubiya wajenta harta samu sauk'i. Saiya fara fushi da rok'on tabarta Dan ALLAH shima zai kula da ita ai, abasu Ayusher ko feena takoma wajensu saita taimakawa Munubiya da aikin gidan. Mama Rabi'a tace a'a, Ayusher itake taimaka mata itama, feena kuwa ba cikakkiyar lafiyace da itaba, ba kowanne aiki take iya yiba ko agida (kunsan masu sikila dai🤦🏻‍♀, ubangiji ALLAH yabama dukkan masu irin wannan ciwo lafiya, ALLAH yasa yazamema rayuwarku kaffara kuda iyayenku da kullum suma hankulansu ba a kwance sukeba😢, duk mai wannan ciwon ina tsananin tausayinsa wlhy😭). Babu Wanda yaa marwan ya iya, dole ya tattaro kayansa shida Munubiya suka dawo gidan kawai, ai ko su Ayusher sunci dariya, danma fadeel bayanan, saidai a waya suka bashi labari. Munubiya tacigaba dasamu kulawa wajen mama Rabi'a, bata aikin komai saidai amata, sai idan boss nason rage nauyi ya janyeta d'akinsa da wayo ya kashe arna😉😎. Mama Rabi'a duk tana kula da su, amma saitayi kamar batasan bikin dasukeyiba, Dan taga idon yaa marwan a tsakar goshi yake😂😜. 🤥kai jama'a mu koma India.🛫⛹🏻‍♀⛹🏻‍♀ .................................................... ______________________________ .................................................... Zafin jikinane yafara masa yawa, dan yafara shiga sosai jikinsa, cikin barci ya laluba danson jin minene mai zafi ya rungume haka? jin kamar mutum yasashi k'ok'arin bud'e idonsa dasukai masa nauyi saboda barci, dishi-dishi yafara ganin fuskar munaya, hardai yasamu nasarar bud'e idon gaba d'aya a kanta🤫.................✍🏼 _ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🤚🏻✋🏻_ [7/3, 9:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_Haske writer's asso...._*💡 *_♦RAINA KAMA......♦_* _{Kaga gayya}_ *_Bilyn Abdull Ce_*🤙🏻 ~Book 2~ 👉🏻4⃣ .............Cikeda tsantsar mamaki Galadima ya jujjuya wayar a hannunsa, kai kace itace zata fassara masa ma'anar sak'on, kuma komawa yay yana karanta sak'on a karo na biyu, a fili yace, *“SURIKI! SURIKI!.* to nikam wanenen sirikina?”. A take zuciyarsa tabashi amsa da *Baban matarka ta contract*. wata fad'uwar gabace ta samesa lokaci guda, wadda ALLAH ya tak'aita bata buga da bugun zuciyarsa ba, cikin tsitstsinkewar tunani dana zuciya yashiga bitar message d'in kamar mai haddar karatu, idan ya fahimci sak'onan dai akwai mummunan al'amari daya faru akan mahaifin munaya kenan? “ya salam”. ‘ya furta a fili, cikin dafe kansa yakuma fad'in “to adalilin mi wani abu zai samesa kuma yazam kamar yashafeni?”. gabansa yakuma fad'uwa, mutuwar Alhaji Abdussalam Abba mahaifinsu Samha ta dawo masa a rai, (mijin aunty Mimi). dafe kansa dake shirin sara masa yayi, to mizai kawo Abban munaya cikin case d'insa kuma? Sam bazai yuwuba ma, koma dai by mistake wani yaturo masa sak'on ne?. “mtoww! K'ilama hakane”. ‘yay maganar a fili yanajan guntun tsaki, tareda jefa wayar kan gado yacigaba da shirinsa. Shiri yake amma yakasa fidda abin a ransa, koyayi k'ok'arin ture tunanin gefe sai yakasa, dukda zuciyarsa tak'i yarda ta gaskata sak'on nasane. shiri ya kammala cikin Ash color d'in shadda gizna dakakkiya, tamasa k'yau ainun, komai nasa saiya saka Ash, Takalminsa helf cover, agogo da hula duk ash, ya kwashi phones nashi a hannu, ya fesa turare da gyara zaman hularsa sannan ya ciro wayarsa d'aya a aljihu, dan yakasa daurewa, number yaa marwan ya lalubo ya kirasa. A time d'in yaa marwan nata lallashin Munubiya tasha shayi sutafi asibitin amma tak'i, ta gardame akan ta k'oshi itadai su tafi kawai, mama Rabi'a dasu Ayusher sunyi lallashi amma tak'i yin shiru tasha, sai kuka take, hakan yasaka feena zuwa d'akin yaa marwan takirasa, shine yaketa lalla6ata amma tak'i kar6a, sai kawai ya had'e fuska ya koma mata ainahin marwan da bai d'aukar raini, cikin daka tsawa da hargagi yamik'a mata shayin, jiki na rawa takar6a tafara sha, tayi nisa dashan tafara amai kuma, mama Rabi'a tarik'eta, sukuma suka shiga mata sannu, yaa marwan na dafe da kansa cikin damuwa kiran Galadima ya shigo masa, kamar bazai d'aukaba saikuma yaciro wayar a aljihu ya diba. Mamakine ya kamashi dayaga sunan Galadima ta Nigeria, (ko sunzo k'asarne?), da hanzari ya d'auka tana gab da katsewa. Yanda Galadima yaji muryar yaa marwan yayinda yake amsa masa sallama sai hankalinsa ya tashi, ko gaisuwar kirki basuyiba Galadima ya hau masa tambaya akan Abba. Yaa marwan yace “gaskiyane ranka ya dad'e, jiya misalin 12pm Abba yayi accident, sunyi taho mu gama da wata thriller, yanzu hakama yana general hospital”. Zufar dake tsatstsafowa a fuskarsa yasa handkerchief ya share, muryarsa na rawa yace, “Marwan da gaske?”. Kula yaa marwan yayi Galadima kamar ba a hayyacinsa yakeba, shima muryarsa na rawa yace, “da gaskene ranka ya dad'e”. “hasbinallahu wani'imal'wakil” Galadima yafara maimaitawa akan la66ansa, ya sauke wayar a hankali zuciyarsa na wani irin suya, yama rasa wane kalar tunani yakamata ace yayi? Yaya zai fassara wannan lamarin? Kenan akwai wani Abu dabai saniba, kodai Abban munaya yanada wata masaniya akan lamarinsa, kokuma bai saniba yafad'a tarko, tabbas yakamata ma akan kansa yay wannan tunanin kodan abinda yayta faruwa tsakaninsa da Munaya, cikin k'araji yace “MUFTAHU!! kasan komai, dolenema kasan komai muftahu!!!, tabbas duk da kasancewarka d'an uwana, jinina, saina binneka da ranka a tsakkiyar masarautarnan inhar mahaifin matata ya rasa ransa wlhy, wannan ALWASHI NANE!!. ya k'are maganar yana buga table glass dake gabansa da masifar k'arfi, aiko ya tarwatse a wajen, kwalba ta yanka masa hannu. baibi takan ciwon dayaji ba yamik'e a harzuk'e ya d'auki wayar ya fice. A yanda yafito sai hankali hadimansa ya tashi, ga hannunsa yana d'igar da mini kad'an-kad'an, kuma suna gaisheshi yak'i amsama kowa gaisuwarsa, ko hannun daya saba d'aga musu inbaya buk'atar maganar yau basu samuba, da kansa yabud'e motar yashiga, hakan yasaka sarkin Mora Shiga da hanzari shima shida sauran dogaran dakan bisa in zai fita. Ko takan zuwa fada yay gaisuwa baibiba, suna fita daga masarautar kiran Nuren yashigo wayarsa. Yana d'agawa yace, “kajiramu a plaza”. ‘abinda yace kenan kawai ya Yanke wayar'. Nuren yabi wayar da kallo, inhar kunnensa yajiye masa dai-dai to ran Galadima a matsanancin 6ace yake, to mi aka masa? kokuma shida mutuniyar tasane mama Fulani? Nuren ya girgiza kai kawai yana murmushi, mama Fulani da Galadima sai addu'a kawai, dan tamkar suna ganin hanjin junane. Tafiyar mintuna 30 takawosu plaza, amma basu shigoba, dan haka Nuren yana hangosu yataso yafito. Matashin Saurayine shima, mai kama da Galadima sosai, dan wandama bai saniba saiya d'auka tagwayene, abubuwa kad'anne suka banbantasu, dan a shekaruma zasu iya zuwa d'aya, shima Nuren dagani yana cikin Hutu sosai, gashi d'an gaye ajin farko cikin nutsatstsun matasa masu ji da kai. Da sauri dogari d'aya yafito ya rissina yana gaisheshi, hannu ya d'aga masa cikin sarauta (hakan ya tabbatar min shima jinin sarautar ne) dogarin yabud'e masa inda Galadima yake ya shiga. Kallo d'aya yayma Galadima ya tabbatar akwai Matsala, hannu yabashi sukayi musabaha, cikin tsantsar kulawa yace, “brother mike faruwa ne?”. Galadima ya kalli Nuren da idanunsa da suka koma jajaye, cikin matsanancin d'acin zuciya yace, “bansan alak'ar data sashi cikin tawa ba”. Nuren yace, “waye?”. Kauda idonsa Galadima yayi daga kallon Nuren, ya maida ga window yana kallon mutane daketa harkokinsu, wani murmushin takaici yayi, sanan yafurta *“SIRIKI!”* Nuren yazaro idanunsa waje, a zabure

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});