Chapter 48
Chapter 48
kwanaki kad'an na amince da tayin auren Contract d'in da kukaimin, dukda ba waccan binciken namu kawaine keda alak'a da amintar tawaba, akwai wani dalili daya shafi ahalina”. Mik'ewa Galadima yayi yana salute d'ina, yace, “kin cancanci yabo my friend, dukda tabbas a farkon aurenmu kema kina cikin zargina akan turoki akai gareni tun farko, amma yanda kike halayyarki da d'abi'unki sai kika kauda hankalina, a tunani na dukkan mutum dazai kwantarmin dakai yaringa nuna tsorona to tabbas wannan mutumin sunamsa *MAGE MAI KWANCIYAR 'DAUKAR RAI* a wajena, amma kece mutum ta farko kuma mace data iya mayarmin murtanin magana kai tsaye, batare da shakka ba, sai dai inason Sanin minene alak'arku da Muftahu to?”. “muftahu kuma? babu wata alak'a bayan wadda kasani, dan tare Na fara ganinku ai”. Takowa yay zuwa inda yake zaune a da, ya koma saman kujerar ya zauna, “kin tabbatar babu alak'a ta kowane fanni?”. “miyasa kake kokwanto? inhar zaka kasa gaskatani a nan bai kamata ka aminta da zancena Na farkoba kenan?”. Ya murmusa yana fad'in “kozaki gaji Abba ne?”. Nace, “akan me?”. “jaridanci mana, naga kin shahara wajen iya bincike”. Mik'ewa nayi saboda k'afata tafara yaamm alamar jinina yana buk'atar motsawa, nafara d'an takawa. hannaye kawai ya hard'e a k'irji yana bina da kallo, saida nad'an zagaya d'akin kafin nabashi amsa da fad'in “yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”. Kansa ya girgizamin kawai. Nace, “humm nifa nan daka gani, kwakwalwata tana aiki fiyeda yanda kake aiki da agogo”. “really?”. “baka buk'atar jayayya”. Ya d'aga kafad'a yana ta6e baki, “hakane kuma”. Sharesa nayi na zauna a bakin gadon danna d'an mik'e, a haka najawo filo na kwanta k'afafuna a k'asa. Tasowa yayi ya dawo ya zauna saman k'aramin table d'in gaban sofa, jinai kawai ya kama k'afata ya d'ora saman cinyarsa yana matsamin a hankali. Da mamaki na d'ago kai na kallesa. Ido d'aya ya kannemin yana d'an ta6e gefen bakinsa, ya maida kallonsa ga k'afar. Sabon salo, na fad'a a raina. a fili kuma nace, “yalla6ai kaine......” Bai bari na k'arasa ba yay saurin fad'in, “ba dole na taimaki lafiyar abin cikin kwan ba”. Harara na dalla masa ina janye k'afata, ya kalleni da mamaki, “ya haka? ko haushi kikajine?”. “miye zai Sani jin haushin? saika bari idan yafito duniya ka matsa tashi k'afar”. “oh ni Sameer naga ta kaina”. “zama kaga ta k'afa bata kaiba, Sunan nakama bazaka iya fad'arshi da r ba”. “oh nan kuma kika dawo?”. Matsawa nayi baya saman gadon sosai batareda na bashi amsaba. shima saiya taso ya hawo gadon, hakan yasani yunk'urawa zan sauka na bar masa, fan nasan hawan nasa bazai haifar da d'a mai ido ba, yasa hannu ya rik'eni, “yalla6iya ai saikin maimaita mikika fad'a dalla-dalla”. “lah wasafa nake maka, kaga rigar wankace a jikinka kaje ka cire kar mura ta kama ka”. “Ai kinga dai-dai kenan”. Yay maganar yana k'ok'arin kwance igiyar rigar. Hannunsa nayi azamar rik'ewa ina marairaice face alamar yaji tausayina. Baki ya ta6e yana ture hannuna, na kuma k'ank'ame nasa nak'i bari. Murmusawa yayi, ya kwanto gefena tareda sakani jikinsa ya rungume. “Nace please wankama zanyifa, zafi nakeji”. Maidani yayi ya kwantar, cikin kunnena yace, “kedai fad'i gaskiya, ko kina son a.......”. Rufe bakinsa nayi da tafin hannuna ina kukan shagwa6a, ya shiga k'ok'arin cirewa amma nak'i bari, shi dariyama na bashi, irin wannan hak'ilo haka. duk yanda yaso na barsa k'i nayi, saida barci yafara fisgata hannun ya zame. Kansa ya girgiza kawai yana murmushi, a fili ya furta “mai bakin tsiwa”. Ya k'are maganar da sumbatar goshinta yana gyaramata kwanciya a jikinsa. Ya tsira mata idanu yana kallon yanda take fidda numfashi a hankali, a zahiri idonsa a kanta, amma zuciyarsa maganganunta taketa cud'awa, shi baima ta6a ganin mace yarinya k'arama mara tsoro da shiga rikita-rikita irinta ba, bata gudunma shiga had'ari? ya sauke ajiyar zuciya yana tashi zaune, k'afafunta yashiga mammatsa mata a hankali, aikam harda gyara kwanciya su madam munaya, yad'an murmusa, yasan ko'a d'azun tanaso fa, amma iyayi yasata hanashi ya mata. Ya d'auki tsawon lokaci yana mammatsa mata jikinma gaba d'aya, yayinda zuciyarsa kuma ke tattance bayananta dalla-dalla, daga k'arshe sauka yay daga gadon ya fice zuwa d'akin sirrinsa, duk abinda tafad'a yasamu sabon file ya bud'e masa, baya wasa da evidence komai k'ank'artarsa, balle ma nata ya wuce Na wasa, ya dad'e yana rubuce-rubucensa kafin ya koma kan Computers, sunan SD kawai ta ambata masa, dan haka yafara searching gameda SD d'in kawai, babu abinda ya fahimta akan hakan, dama baiyi tunanin fahimtarba, waya ya d'auka ya kira Nuren, bayan sun gaisa yace, “Nureddin acikin yaransu Tanderu kasan SD?”. “SD! SD! kai anya kuwa? amma dai ina zuwa bani mintuna 30”. “ok saina jika”. Galadima Na yanke wayar ya nemo number d'in Abba da bakowa ya sani d'innanba yafara aiki a kansa, dukkan Contact d'in ciki suka bayyana, d'aya bayan d'aya ya dinga binsu yana nazarin adadin kiran da aka ta6ayi, sau nawa aka kira Abba sau nawa ya kira shima? Mafi yawa ma kiransu yafi yawa, yad'an murmusa yana wasa da tsinken hannunsa a kan la66a da nazarin yanda zai 6ullo musu, dan duk hanyar daya kamata yayi bincike an d'auki mataki a kanta, tsawon lokaci bai fahimci komaiba, sai zuwacan wata dabara tafad'o masa, nutsuwa yay yana sarrafa Computer's d'in cikin tsantsar kwarewa da gwaninta, ya kafa musu tarko ne a wayar innarsu Munaya, dan ya tabbata watan watarana zasu iya kira ko sak'o, amma abinma haushin saiya iske wayar inna a kashe, ya dafe kansa, saifa da yacema dady aringa barin wayar a kunne. Babu shiri ya d'auki waya ya kira daddy, bayan sun gaisa yaymasa maganar kunna wayar innar. cikin mamaki Dady yace, “ai a kunne take koda yaushe, Change ma baya k'arewa nake kuma sakata, idankuma zan zo nan nakan sanarma Jafar shima ya kula, amma ina zuwa dai”. Galadima ya amsa da to, amma k'asan zuciyarsa tana mamaki. babu dad'ewa Abba ya sake kiransa, “Ashe Change ne ya k'are babu dad'ewarnan ban lura ba, amma gashinan Na sakata”. “to Dady, Na gode sosai”. Sunayin sallama da Dady Kiran Nuren Na shigowa, d'agawa yayi, Nuren yace, “inagafa brother hanya d'ayace dazata saka musan shi wanene SD d'in, dan abinda Na lura dashi baya amfani da hakan ta kowanne fanin yanar gizo, maybe da full name yake amfani. yanzu zan sayi ticket insha ALLAH zanje domin bincika a wajen Malam Saminu, nasan ya magantu yanzu, zai amsa mana dukkan tambayarmu”. “ok hakan yayi, idan ka fahimci bai saniba karka takurashi, ka binciki yarinyarnan itama, koma ka fara bincikarta dan ita bama wayo ta cikaba sosai, k'ila kafi samu cikin sauk'i a wajenta, abinda yasa Malam saminu baison fad'ar komai, babbar 'yarsa cikin 'ya'yan Alhaji balala wani ya mata ciki, kuma sun dai-daita akan idan ta haihu za'ama yaran aure, wannanne yasakashi tsoron fad'ar komai, dan karya lalata waccan alak'ar, dan tabbas yasan yana fad'a auren bazai yuwuba, to nima banason shiga hak'in kowanne ahali akan aikina, shiyyasa nabashi dama kaga bankuma waiwayarsa ba, yanzu haka yarinyar ta haihu kwana hud'u kenan, amma shi yaron ya kawota nan Dubai ta haihu ne, a nufinsu bayan haihuwar da sati d'aya zasu dawo Nigeria a d'aura musu aure sannan su dawo Dubai d'in,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92