Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 70

Chapter 70

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suna, inda aka rad'a sunan yara bayan sallar Asubahi, *_Abdurrahman, Abdurraheem, and Amaturrahman_* masha ALLAH Babies ALLAH ya raya Ku akan sunnah da tafarkin addinin Islam. Yara sunsha Addu'oin fatan alkairi sosai, tun kuma a safiyar shagalin suna ya fara, dan kowa yana cikin walwala da farinciki, mai jego munaya ansha k'yau itada babies har an gaji, kamar ka sacesu ka gudu, hotuna dai suna shansu kala-kala a yau d'inan, Su Momma ma da basa kusa anata sambad'a musu, dan duk wani motsin da za'ayi Sauban da Samha basa gajiya da tura musu, sai sukaji tamkarma suna nan suma, saboda kallon komai suke tamkar live, farin ciki da walwala sun yalwatu a zuciyar Abie, bakinsa yakasa rufuwa dan tsabar nishad'i daya tsinci Kansa yau aciki. Hummm babbar magana, kayan barka dai sun iso, fans yaufa nasha kallo, kaga Inda akeyi don ALLAH, ta bakin Munaya tace INA zasu da wad'annan kaya haka, lamarin tamkar fariyya, gashi kowanne sashe sai kawo nasu sukeyi, gidan sarauta manya, babu Wanda zaiso aga kasawarsa, ballema wannan kana k'inyi za'a CE bak'inciki kakeyi, shiyasa mama Fulani aka ware aka zuba kayan barka Na gani Na fad'a, daga gidansu Munaya ma su inna sun taka rawar gani dai-dai k'arfinsu, daga ita har Munubiya komai iri d'aya aka musu, kayan babies ne kawai Na munaya yafi Na munu saboda su su uku ne ita kuma Nata biyu. Nanfa y'an gidan suka Shiga k'us-k'us d'in gulmar Ina inna ta samu kud'in yin wannan hidima haka? dansu basuyi zaton hakanba, musamman da abin yazo da yawa ma, itadai inna ma ko kallo basu isheta ba, hidimar gabanta da farincikin datake cikine a gabanta, bakinta yakasa rufuwa saboda farinciki da godiyar ALLAH mai sassauya al'amura a yanda yaso a kuma lokacin da yaso, idan ALLAH ya jarabceka karkayi bak'in ciki, hak'urinka zai iya zama sauyin alkairi a gareka, inama iyayensu Nada rai suga wannan k'yak'yk'yawar rana, ta share hawayenta tana murmushin farin ciki, sannan ta kira y'ar uwarta a waya suka cigaba da tattaunawa. ***** K'arfe uku da rabi kuma za'a gudanar da gagarumar walima da aka kama babban hall Na musamman. A wannan rana yara dai har fada aka kaisu sukayo gaisuwa da hotuna da mai martaba da gayyar y'an uwa da abokan arzik'i, su Harun dai sune gaba-gaba, uban gayya kuwa Muhammad Sameer Saifudden Galadima Baban y'an uku😂 ai ba'a cewa komai, koma ganinsa ba'ayi saboda tsabar shiga hidima, wannan suna ko bikidai iyaka kenan. Nasan kuma fans duk kunyi shirin wannan walimar baje dad'i😋😋. Nifa buhu Na tanada walle😆, saura kuce Bily tacika zari da son banza kuma🙄, har y'an anguwarmu saina kar6oma gifts d'insu😜😂🤸🏻‍♀. **************** Alhmdllh yaran Mununbiya ma an rad'a musu suna bayan sallar Asubahi, Namijin *_Aminudeen macen Ameenatu_* ALLAH ya raya wad'annan yara masu albarka😘😘🥰. Yau daikam farin cikin da Abba da innarsu suke ciki 6ata lokacine ma, kai da dukkan masoyansu irinmu, masu bak'inciki kam Ku k'ara himma, hassada ga mai rabo takice😏🤷🏻‍♀. Kowa nabashi dama ya k'iyastama zuciyarsa yanda bidirin suna yake guna, dan Alk'alamin Bily yau yayi k'ank'anta wajen wallafowa, sai mugama Na wannan satin bikin sunan bai k'areba😁.................✍🏻 Kuyi manage da wannan yau inada uzuri🤦🏻‍♀. ☺my Guy's a kafta kawai danjin yanda bikin suna zai gudana gobe idan ALLAH ya kaimu, kowa dai ya k'ure adaka dan karfa a kawo mana raini😕, kunsan dai halin mama Fulani, tana iya hanawa abarmu shiga😩🥺. *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~Book 2~ 👉🏻2⃣5⃣ ................Aunty Salamah da kanta tazo yima Munaya kwalliyar zuwa wajen walima, saida tafara biyawa tama Munubiya sannan ta wuto nan, ta iske su duk a damuwar kukan da Abdurrahman ketayi, sai faman jijjigarsa akeyi amma yaro yak'i yin shiru, an basa nono yak'i kar6a, innro ta kar6esa ta hura masa kunne, ya kuma k'yak'yacewa da sabon kuka yana dunk'ulewa waje d'aya, tace “inaga kunnensa ke ciwo yaronnan”. Munaya Na gefe zaune ta zuba tagumi kawai tana kallonsu, ita kad'ai tasan suyar da ranta ke mata, gashi Galadima baisan wainar da ake toyawa ba, yanacan tareda su Akash da suka iso yanzu. Innaro ta dungureta, d'ago idanu tayi ta kalleta, ta mik'a mata Abdurrahman daketa sauke ajiyar zuciya, “d'iga masa ruwan nono kad'an acikin kunnen insha ALLAH idan aka dace zai daina”. Kar6arsa tayi, ta d'ora kan cinyarta, dukma ta rikice ta rasa yanda zatayi, saboda sai mimmik'ewa yakeyi azaba na cinsa, ga Amaturrahman itada Abdurraheem suma sun d'akko nasu kukan, laraba ta rik'e matashi ta samu ta d'iga masa, ruwan nonon Na shiga yakuma mimmik'ewa yana kwalla ihun sabon kuka. Saiga hawaye a na zuba a idon Munaya, tasaka hannu ta toshe kunen ta kozataji sassaucin jin kukan nasu dake d'aga hankalinta. Tausayinta saiya kama laraba, tasan indai wannan ne yanzu ma aka fara, yaro d'aya ma ya kake k'arewa balle yara uku. Cikin amincin ubangiji kuma duk sai sukayi shiru, innaro da laraba sunata faman jijjiga, itama Aunty salamah ta kar6i Na hannun munaya, tun suna ajiyar zuciya har barci ya kwashesu. Munaya ta shige bayi tana share ragowar hawayenta. Baki innaro ta ta6e tana fad'in “lallai aiki yasamu mata, yo indai kukane yanzu ma kika fara”. Daga Aunty salamah har laraba dai babu Wanda ya tanka. Munaya kuwa data jiyota daga bayi tace “aniyarki ta biki, mai mugun fata kawai”. Wanka tayo ta fito, Aunty salama kawai ta tarar a d'akin sai bayi biyu dake morping, suka durk'ushe k'asa suna gaida Munaya. Hannu ta d'aga musu kawai dan batasonyin magana, har yanzu raunin tausayin Abdurrahman baibarta ba. ta kallesu duk suna kwance kan gado barci ya d'aukesu, yayinda Aunty Salamah ke zaune kan sofa tana warema yaran kayan da za'a saka musu. Ta d'ago ido tana kallon Munaya, “haba auta kuka kikayi da gaske? Please kidaina musu kuka, ba'ason uwa Na zubarma d'a hawaye dukda wannan Na tausayine kinji”. Munaya ta had'iye abinda yamata tsaye a mak'oshi tana gyad'ama Aunty salamah kai. Saida Aunty salamah ta gama ware kayane sannan ta taso suka fara kwalliyar, anutse sukeyin komai, dan da sauran time, hakama Munubiya a nutse aka mata tata, anama Munaya tana kallon hotunan Munubiya, taji dad'in yanda y'ar uwarta tasha k'yau, dukda ma batakai ga saka kayaba. ★★★★★★★★★★★ Muftahu nata kai kawo a tsakar d'akinsa, tunanin tawace hanya zai fargar da Galadima kawai yakeyi, dan dolene saida hannunsa zaiyi wannan aikin, saboda had'arinsa, gudun kar reshe ya juye da mujiya, sannan aikin yana buk'atar takune da sirri. Fitowa yay yanufi can cikin k'aton lambun masarautar indasu Galadima suke tareda mafi yawan y'ammata da samarin masarautar. Wasu sunata hirarsu in group, wasuko hirar tasu ta masoya ce, Muftahu ya k'araso inda su Galadima suke, sun baza babbar darduma anata hira, Bama zaka ta6a Sanin suna lambun ba saboda sunacan ciki nesa da sauran yaran. Galadima na zaune a gefe cikin kujera, ya d'ora k'afafunsa a wata kujerar, sanye yake da farar shadda d'inkin boda, fuskarnan babu walwala ko kad'an, gaba d'ayan hankalinsa yanaga system d'in daya d'ora bisa cinya yana latsawa. Muftahu ya mimmik'a musu hannu sukayi musaba cikin fara'a. Amma tsakaninsa da Harun ba hakan baneba, kowa murmushi mai cikeda ma'anoni yay ma d'an uwansa, kafin su saki hannun juna. Muftahu ya matso kusada galadima shima

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});