Chapter 11
Chapter 11
abinsa. tsaye tayi tana binsa da kallo, jitake kamar ta tsala ihu, harma tafara tunanin ko shid'in kurmane?. cikin matuk'ar mamaki ta hango wasu masu kaya iri d'aya sunyo wajensa, daka gansu kaga jama'ar masarauta. da k'yar ta had'e yawun bakinta, kenan shid'in jinin sarautane?. Batada mai bata wannan amsar, Dan haka taci gaba dabin motocin Galadima da kallo har suka fice abinsu. Driver d'in da yazo d'aukarta yak'araso inda take, gaisheta yafarayi kafin ya k'ar6i handbag d'in hannunta. amota take tambayarsa koya San wanene Wanda masu kaya iri d'aya sukazo d'auka?. Yace, “ma'am Galadima Sameer kenan, d'an tsohon Sarki, kusan 1month kenan da aurensa ai”. Hararsa tayi cikin daka tsawa tace “ina ruwana dawani aurensa, bashi Na tambayeka ba. Punishment d'inka Na fad'amin abinda ban tambayeka ba shine ka nemomin number sa”. “ALLAH ya huci zuciyarki Ma'am”. Banza tamasa, yayinda shikuma zufa keta karyo masa dukda AC n dake motar, tunaninsa a ina shikuma zai Samo number babban mutum irin Galadima Sameer shikam? yasan idan bai samo d'inba yashiga uku, dan yarinyar nan ba mutunci gareta ba. ********************* Tun bayan tafiyar Galadima saina zama wata sukuku, abin mamaki saigani da kewar Galadima wai, gaba d'aya yinin sai nayishi wani babu dad'i, ga gabana yanata yawan fad'uwa, jinake kamar wani al'amari yana shirin faruwa da rayuwata. Sauban ma sarkin tsokana kasa shiru yayi saida yay magana. Bayan ya dawo school sai muka tafi asibiti, tunda Na gaida Abie da Momma da Aunty Mimi saina koma gefe nayi shiru abina, ciwon jikine kawai ke nuk'urk'usata, dan ga6o6ina masifar ciwo sukemin, narasa wannan dalili? zazza6inma banaji yanzun, ga yawan fad'uwar gaban dana yini inayi, sai kasa kunne nake naji ko Galadima zai kira wani a 'yan uwansa yace ya sauka lafiya, dan zuciyata tafi karkata da fargaba a kansa. Shirun da Sauban yaga nayi shine ya kalleni yana dariya k'asa-k'asa. “Aunty gimbiyarmu har kin fara kewar Hubbin naki halan?”. Idanu nad'an waro ina kallonsa, ganin su Momma Na dariya saina 6oye face d'ina cikin veil d'ina ina fad'in “kai yaa Sauban ALLAH a'a”. Dariya suka kuma sanyamin, Abie nata murmushi shidai, Momma tace, “A'a Mrs Galadima kifad'a gaskiya dai?”. Kunya takuma lullu6eni, saina k'udundune kaina gaba d'ayama a gyalen saboda. ina k'aunar wannan family sosai a raina, saboda nima suna nunamin tsantsar k'auna, ko yau nabar cikinsu auren contract d'inmu yak'are bazan manta da alkairinsuba a gareni. Haka nagama shirin barci Na kwanta a gadonsa ina shak'ar k'amshin turarensa danakejin dad'insa fiye da da. nadad'e ina juye-juye banyi barciba saboda damuwace cinkushe da raina, ga zazza6i mai zafi ya rufeni, bansan ina Galadima yajeba balle nayi tunanin samun number na kirashi, Na gwada number shi ta nan India tak'i wucewa, dama a wayar Samha Na d'auki number bama ta saniba, yau babu mai kulawa dani, sainaji wata kewar innarmu da Munubiyata sun dawomin sabo fil a zuciya. Sai da dare yakusa rabawa kafin barci mai nauyi ya d'aukeni. _____ .★. _____ .★. _____ Har yamma ba'abari kowa yaga Abba ba, 'yan gidanmu sunci kuka harsun gode ALLAH, Su Munubiya da dukkan yaran gidanmu Na ma'auri tuni labari ya iso musu, kuma duk sun tattara a asibitin suma. Doctor d'in dayake kan Abbanmu ne yafito yana basu hak'uri akan suje gida hakanan, dan gaskiya baza'a bari suga Abba ba a yau. Sabon kukane yatashi, musamman ga innaro, idan ka kalleta dolene tabaka tausayi wlhy, yau babu jarabarnan da rashin mutunci, kuka take da fad'in Auwalu karya tafi ya barta.......... Sambatunta yakuma raunana zukatan mutane da yawa a wajen. Munubiya tayi yunk'urin kirana amma network yahana, da Yaa marwan yakula da hakan kuma ya hanata, yace karta sake ta sanarmin yanzu. Wannan dalilin yahana a sanar min d'in. Kowa zuciya babu dad'i suka tattara suka tattafi gida, dady da baba k'arami, yaa hameed yaa shafi'u da ya Naseer aka bari a asibitin zasu kwana. Ranar duk Wanda yasan gidanmu yasan babu lafiya, Dan gidan yayi tsitt, kowa tashi ta isheshi a zuciya, barcima k'alilanne daga cikinsu suka yisa. ___________________________ Sosai hadimansa sukayi farincikin ganinsa, kamar yanda shima yay farin cikin ganin Nasu, sud'in mutanene masu muhimmanci a rayuwarsa, sunzama wasu 6angare na duniyarsa. Kwance yake a bayan motar idonsa a lumshe, ya saki guntun murmushi saboda tinano yanda zata k'are masa a wajen Momma, koda wasa bai sanar mata Nigeria zai zoba, yayi hakane kuma dan kartayi yunk'urin dakatar dashi ma. jin alamar motar ta tsaya ya bud'e lumsassun idanunsa tareda furzo k'aramar iska, duk da isowar dare yayi hakan baisa sauran hadimansa sun kwanta ba, ya iskesu zazzune a k'ofar sashensa suna jiran isowarsa. Dogarin daya bud'e masa k'ofar yafara k'ok'arin d'aukar briefcase d'insa domin shigar masa. Shima ziro k'afarsa d'aya yayi ta inda aka bud'e masan, ya zuk'i iskar masarautarsa tareda fesota tabaki yana lumshe idanunsa, ko ina kwanyar yake da hasken lantarki tamkar rana, duk lokacin daya zo cikin masarautarsa, mahaifarsa, yakan tsinci kansa cikin tunano abubuwa masu d'aci da rad'ad'i a zuciyarsa, yakanji inama ace shid'in ba kowa baneba, inama ace shid'in talakane fitik mai tarin kwanciyar hankali, da za'ace yaza6i rayuwar dazaiyi, da zai za6ama kansa zama talakane, dan babu Wanda yakai talaka kwanciyar hankali inhar yanada k'yak'yk'yawar zuciya da wadatar zuci, amma babu komai a cikin dukiya da mulki sai damuwa darashin kwanciyar hankali, kai kenan kullum cikin rashin nutsuwa, idan kayi wasama ibadar da ubangiji ya halicceka dominta bazakayiba, ya had'iye wani Abu mai d'acin gaske a mak'oshinsa. sannan yashiga k'ak'aro murmushin dole ga sauran hadimansa dake gida basuje tarbarsaba. daka kallesu kasan suna cikin tsantsar farincikin ganinsa, dan sunyi kewarsa, shima hakance agaresa. bayan sun gama gaggaisawa ya tambayesu lafiyarsu sannan yashige ciki. Ko ina k'al yake tamkar yanda yake buk'atar ganinsa, (hadimansa nada k'ok'arin tsaftace sashensa koda baya k'asar). Zama yay bisa kujera yana fad'in “ya ALLAH! Alhmdllh”. Dogarin daya shigo masa da jakka yakuma masa sannu da zuwa sannan yafice. Yakai mintuna 5 a wajen zaune, sai k'ullawa da kwancewa kawai yakeyi, ga gajiyar zaman jirgi na nuk'urk'usarsa data rashin isashen barci dabasa samu shida Munaya. da k'yar dai yamik'e zuwa bedroom d'in, komai need sai k'amshin mayen turarensa da air fresheners mai sanyin dad'i ke tashi, ya ajiye jikkarsa a kan gadon sannan yafara zame kayansa danya samu ya watsa ruwa. Ya d'an jima a bayin sannan ya fito d'aure da towel, yana tsane fuskarsa zuwa kai dawani. wardrobe yabud'e ya d'akko boxes kawai yasaka, sannan ya saka jallabiya, sallolin da suka riskesa a hanya ya rama, yana idarwa yacire jallabiyar, matsawa yay jikin mirror ya fesa turare kad'an ya hau gadonsa da yay missing. harya kwanta yatashi zaune, briefcase d'in dayazo da ita ya bud'e, ya Ciro wayoyinsa tareda layinkansa na Nigeria duk ya saka, sannan ya ijiye wayoyin, insha ALLAH zuwa lokacin da zai tashi yana fata komai ya dai-daita. Addu'ar barci yayi ya gyara kwanciya, amma sai barci yace bai gadaba, tunanin ahalinsa daya baro wata k'asa ya dabaibaye zuciyarsa, wata kewarsu ke tsikarar zuciyarsa, yanzu yasan Abie yayi barci, hakama Momma watak'il ta kwanta, dan macece mai yawan k'iyamull laili, duk da a asibiti takan kwana hakan baya hanata kusanta kanta ga mahaliccinta, Aunty Mimi da Samha ma yasan sunyu barci, Sauban ne dai dakamar wahala ace ya kwanta,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92