Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Raina Kama Book 2 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Ashe duk abinda nake yanajina da kallona. murmushi yayi kawai yana lumshe idonsa, a ransa yana jinjina irin rashin wayona. Ajiyar zuciya Na sauke a hankali, sannan naja bargon dayake babbane Na lullu6a, mintuna kad'an nafara zufa, alamar zazza6in ya sauka. Bargon na janye don insha isaka, bansan sanda barci ya saceni ba. Juyowa yayi ya kalleni, yaga ina sauke numfashi a hankali alamar nasamu barci, k'aramar ajiyar zuciya ya sauke kafin yasake addu'a shima ya gyara kwanciyar sa. ★★★★★★★ Yau gidanmu sun tashi cikin tashin hankali, Abbah yay Accident yayin dawowa gida daga wajen aikinsa, innarmu Na kwance ciwon kai dukya isheta, tunda ta tashi da safe dashi ta tashi, gasu Aryaan sun isheta da ihun fad'ansu, sai mugun wasa sukeyi suna guje-guje a falon, amma takasa d'aga kai ta tsawatar musu. Zuciyarta cike da kewar su Munubiya, inda suna nan da yanzu suke bata taimako, koyaya tace batajin dad'i zasu rud'e, amma gashi yau ko wanke-wanke tama rasa mai matashi, sai Zainab maman fauziyya tasaka tayi mata, amma 6angarenta ko shara bai samuba yau, kuma tun d'azun tafara jin mamansu yaa hameed tana k'ananun magana akan tak'i fitowa ta aza musu girki, maimakon sunga shiru su lek'o suji ko lafiya? A'a su babu ruwansu, kawai a dafa abasu suci da 'ya'yansu... Wayarta dake ring ta katse mata tunani, ta kalli su Aiyaan dake danbe Aryaan Na kuka saboda dukansa da Aiyaan yayi a baki. “wani cikinku ya d'akkomin wayata saman freight”. Cikin kuka Aryaan yace “Innarmu kingafa ya dokarmin baki”. “kukuka Sani, nidai nace wani ya d'akkon waya acikinku, idan kuma kuka bari Na tashi sai jikinku yagaya muku”. Aryaan ya d'akko mata wayar ya kawo mata, lokacin harta tsinke, ganin Abbanmu ne yasata bin kiran, bugu biyu aka d'aga, ko gaisuwa bai bari sunyiba, yace mai wayarne yayi Accident, yanzu haka suna general hospital. “innalillahi wa'inna'illaihirraji'un” innarmu tafad'a tana mik'ewa zumbur, ga wata zufa Na karyo mata, batasan tayo waje tana kwalama matan gidan kiraba. Kowacce tafito jiki Na 6ari, azatonsu wata acikinmu aka sako, musamman ma ni dasuke kiran aurena auren d'ori d'afini. tana hawaye ta sanar musu da abinda yafaru. Nanfa gidan ya rikice, yara suka garzaya suka sanarma innaro. Ko takalmi babu haka tanufo gidanmu tana shar6ar majinar kuka da kiran tashiga uku, Awwalu zai mutu ya barta. wannan kwakwazon natane ya ankarar da jama'ar anguwarmu. A rikice baba k'arami da Dady suka nufi asibitin, Dan matan gidanmu sun kira suma sun sanar musu abinda ke faruwa. Kafin wani lokaci jama'ar gidanmu sun gama cika asibitin, sai koke-koke sukeyi suna son ganin Abba, amma an hanasu, Dan bak'aramin buguwa yayiba. ______________________________ Alhmdllh natashi jikina da sauk'i, Dan kuwa babu zazza6in da ciwon jikin, hakama ciwon kan babu, bai tadani ba saida yadawo massalaci, lokacin har gari yafara haske ma. Na idar da salla ina zaune ina addu'a yafito daga bathroom, da alama wanka yayo, Dan sanye yake da bathrobe sky blue, yana rik'e da k'aramin towel a hannu yana goge ruwan fuskarsa. Kallo d'aya namasa Na d'auke kaina, shikoma bai kalleni ba ya wuce gaban mirror ya zauna, saida yafara shafa mai sannan Na tsinkayo muryarsa yana fad'in “ya jikin naki?”. Yanda yay maganar a cinkushe yasakani d'agowa Na kallesa, ganin hidimarsa kawai yakeyi saina d'auke kaina, nace “da sauk'i”. Bai sake magana ba, harya kammala yabar gaban mirror d'in, wajen wardrobe yakoma, nidai kaina Na k'asa bansan hidimar dayakeba. Koda ya d'auki kayan saiya koma bayi ya saka tamkar yanda ya saba, ya fito ya iskeni ina gyaran gadon, ta gefen ido Na kallesa, yayi k'yau cikin wani bak'in lallausan yadi, Wanda akaima ado da jan style, nakula yanason kayan al'adarsa, dukda baitashi ya girma cikin k'abilar tasaba, sock's ya d'akko da bak'ak'en takalma sau ciki ya zauna saman sofa, yana sakawa yana magana, “uhm Zanyi wata 'yar tafiya Na kwana 2 kacal, mikike da buk'ata?”. Tsayawa nayi daga gyaran gadon danake, Na d'ago ina kallonsa kawai, jin nayi shiru kuma yanajin alamun ana kallonsa ya d'ago shima. Ido muka had'a saina janye nawa. “kallon fa?”. ‘yafad'a yana k'ok'arin saka d'ayan takalmin’. Cikin la6e baki nace “yoni yalla6ai mizan kalla anan?”. Banza yamin, saida yagama saka takalminsa sannan yamik'e tsaye yana fad'in “hakanefa, Ashe babu abin kallo anan”. Nima shiru namasa ban tankaba, ya saka laptop d'insa dawasu 'yan abubuwa a k'aramar briefcase d'insa, ya zuge zip d'in yana fad'in “ki shirya muje kiga likita kafin Na wuce”. Da sauri nace “a'a kaje abinka, Indai nice Na warke”. Idanu ya tsuramin alamun tuhuma, nikuma nak'i kallonsa, ya girgiza kansa kawai sannan ya ajiye min kud'i akan gadon, “ni Na tafi, a yafi juna”. 'Dagowa nayi ina kallonsa da mamakin kalmarsa ta k'arshe, bansan sanda bakina ya su6uce nace “ALLAH ya tsare hanya, ya dawo dakai la fi ya”. ‘na k'are maganar da d'aid'aya’. Cak ya tsaya abakin k'ofar, saboda yanda addu'ar tawa tazo masa a bazata, dan bai tunanin hakan daga gareniba, yajuyo a hankali tamkar maison gaskata abinda yaji, kallona yayi muka had'a ido, amamakina saiya sakarmin wani tsadajjen murmushi, irin Wanda zan iya rantsuwa ban ta6a gani daga garesaba. Baice komaiba yajuya yafice da sauri. Yabar zuciyata da luguden dabansan dalilinsa ba. Wata ajiyar zuciya Na sauke, tare da zama jagwaf a bakin gadon na dafe kaina da mamakin murmushin da Galadima yamin. Bai dad'eba sosai a hospital yamusu sallama yafito, dama tun a daren jiya ya sanar musu zaiyi tafiya, ga jirgi kuma ya kusa tashi. yafito sunata binsa da addu'oin dawowa lafiya, yayinda shikuma yake amsawa cikeda murmushi. Saida yafara xuwa sukayi magana da doctors d'in dake kula da Abie, yaji babu wata Matsala sannan yafito. Dama Khumar ne ya kawoshi, Dan haka yanzu ma shine yatafi kaisa airport d'in. Zaman da baifi 30minutes ba jirginsu yataso zuwa 9ja. Zaune yake kusa da window, yayinda wata matashiyar budurwa ke gefensa, tunda tazo da nufin zama yawani kuma had'e fuska, a d'age ma ya amsa mata sallamar data masa, yasaka belt tareda bud'e Newspaper yahau karatu. Budurwar sai satar kallonsa takeyi, tanason masa magana amma bataga fuska ba. Sai da akazo tambayar misuke buk'ata?, yace Coffee. Itama da sauri tace Coffee d'in. juyowa yayi ya kalleta, ta sakar masa wani tsadajjen murmushi. Janye idonsa yayi yanajan tsaki a zuciyarsa. duk yanda taso yamata magana ko sau d'ayane Galadima yak'i yayi, ya had'e gabas da yamma abinsa. Haka kawai sai tunanin tahowarsu da Munaya ya fad'o masa a rai, yatuna yanda tadinga wani dakewa irin itafa ta saba da hawan jirgi. jaridar yasaka ya rufe fuskarsa yana murmushi da jinjina jan aji irinnan yarinyar, ita bata yarda aga marenarta ba. ya tuna diramarsu ta daren jiya, wani murmushin yakuma saki...... haka abubuwa da yawa sukaita dawo masa akan Matar tasa ta auren Contract. wani abun nata abin dariya, wani Na mamaki, ita bata yardaba adole big girl Ce. Koda suka sauka baiko kalli inda yarinyar nan takeba, da sauri tabi bayansa tana fad'in “haba yayana babu sallama? Ai kodan darajar makwaftaka mayi sallama”. Yana sauka daga step d'in k'arshe Na jirgin ya juyo ya kalleta, aransa yace yarinya sai nacin jaraba. Ta kuma fad'in “kozaka bani Number ka muke zuminci”. Yanzu kam wata uwar harara ya zuba mata kafin yay gaba

Table of Contents

Chapters

92 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});