Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Abie dake murmushi ya kalli Galadima da shima yake zaune ya hard'e hannaye a k'irji yana kallonsu da Murmushin, da ido Abie yamasa magana ya matso gareshi. Galadima ya tashi daga inda yake ya matsa kusada gadon, Aunty Mimi tabashi kujera ya zauna, hannunsa ya saka cikin na Abie yana d'an matsa masa, ada komi zakayi awani sashe Na jikinsa bayajin komai, koda zakaita dukansane bazaijiba, amma wannan hannun da aka samu canji da k'afarsa d'aya yanzu ko Yaya aka ta6asu saiyaji, yanda Galadima yake matsa masa hannun a hankali sai yakeji tamkar tausa, yad'an lumshe idonsa cikin jin dad'i yace, “ALLAH yay muku albarka gaba d'aya Muh'd Sameer, Na taya kaina farin cikin samun jikoki a tsatsona biyu, nakuma tayaka murna da samun y'ay'a a karo Na farko, bazan 6oye makaba ina k'aunar matarka, ina jinta a jikina tamkar kud'innan, tun randa Na fara ganinta ALLAH ya samin k'aunarta amatsayin d'iya, ina fatan ALLAH ya cigaba da saka albarka a cikin aurenku, ALLAH ya d'orar dashi har mutuwa”. Babu abinda zuciyar Galadima take sai lugude, auren dake gab da tsinkewa akema wannan doguwar addu'ar? Shikam yaga ta Kans....... Girgiza hannunsa Abie yay ganin ya fad'a duniyar tunani, ya sauke ajiyar zuciya yana murmushin yak'e da fad'in Amin akan la66a. Sun jima a haka Abie nata masa hira, kunsan dai halin mutumin naku, saidai yayta zuba murmushi, inda ya dace ya bada amsa kuma ya bayar, sun dad'e a asibitin kafin su koma gida, amma su aunty Mimi sun riga Galadima tafiya, danshi saida yaje Asibitin su namasu ciyon zuciya yaga likitansa, saboda a tsakaninnan dauriya kawai yakeyi, amma bayajin dad'in jikinsa. Duk wani abinda ya kamata Doctor Subash yamasa, Yakuma k'ara masa da Shawarwari. Lokacin daya iso gida har Samha ta gyara masa samansa da taimakon Sauban, ko ina yayi fes, dama suna sauka asibiti suka wuce, saboda d'okin son ganin jikin Abie. Ya fara zame kayansa idonsa bisa Sofa, ya lumshe ido yana cizar lips d'insa, bai kuma kallon sofar ba ya shige bayi, acanma dai bata sauya zaniba, dukkan abinda Munaya ta ajiye Na amfaninta irin Na mata idonsa Na wajen, haka dai yay wankan ya fito yana goge fuskarsa, sallar zuhur yafara gabatarwa sannan yadawo bakin gado ya zauna, wayarsa ya had'a, ya maida dukkan layikansa Na k'asar aciki. Knocking k'ofa da akayine ya sakashi kallon k'ofar, batare daya tankaba ya d'auke kai, aka kuma knocking, gutun tsaki yayi kafin yabada izinin shigowa. Samha ce d'auke da babban tire, kallo d'aya tamasa ta d'auke kai saboda ganin yanda ya d'aure. itadai ta ajiye ta lalla6a ta fice abinta. Yaja wasu adadin mintuna kafin ya mik'e zuwa wajen abincin, bubbud'ewa kawai yayi, yad'an ta6e baki yana rufewa, sai yama fice daga d'akin gaba d'aya zuwa d'akinsa na sirri. Komai yana nan yanda yabar kayansa, sai y'ar k'urar daba'a rasaba, amma dukda haka saiyaji yana k'yank'yamin d'akin, fita yay ya sauka k'asa, babu kowa a falon, da alama kowannensu gajiya ta kadashi, tsayawa yay yana tunanin wama zai tado? idonsa ya tsaya d'akin Sauban, can ya nufa, Sauban na kwance a gado yana danna lap-top Galadima ya Shiga da sallama ciki-ciki, tashi yay zaune da sauri, “Yaya Sam lafiya dai?”. “Shi wancan d'akin laifin mi yamuku dabaku gyarashi ba?”. Sauban ya marairaice kalar tausayi “ALLAH yaa Sam bayana ciwo, duk mun gajine”. Hararsa yayi, yana masa nuni da k'ofa, ya juya yay ficewarsa. Sauban yad'an tura baki yana sakkowa a gadon kamar zaiyi kuka, cik'in k'unk'uni yace, “shi Yaa Sam d'inna yanda yake aiki kamar wani ingi baya gajiya ya d'auka kowama haka yake”. Sanda ya fito har Galadima ya koma sama, shima hawan yay yanata kunkuninsa, a falo ya iskeshi zaune ya zubama wata kujera ido, baiyi maganaba ya shige d'akin, saida ya Shiga sannan ya Sanya dariya, dan ya kula kujerar da Munaya ke yawan zamace Galadima yakema kallon har hanji😂. Tsaf ya gyara ko'ina sannan ya fito, yanzu kam a kwance ya iskesa ido a lumshe, yace, “yaya Everything is done”. Hannu kawai ya d'aga masa, Sauban ya wuce abinsa, saida ya sauka ya juya ya kalli benen yana fad'i “Chiii yaa Sam He is too stubborn wlhy”. Aunty Mimi dake bayansa bai saniba tai dariya, “kadage ya jika dai, kasan ko kurar wasa saita fika gata agidannan”. Juyowa Sauban yay ya kalli aunty Mimi yana dariya shima, “Aunty babba ai lamarin boss ne sai addu'a” ya matso kusa da ita yana rage murya alamar gulma, “kinsan mineme kuwa?”. Kanta ta girgiza masa. Yacigaba da fad'in “Wlhy Ku taimakemu Ku amso masa matarsa da wuri, dan yafara rikid'ewa zai koma asalin Muhammad Sameer d'insa saboda kewarta”. Idanu Aunty Mimi ta zaro waje, cikin sakin baki da tafa hannaye tace, “Sauban! Yaushe ka fara sanya masa ido?”. Dariya Sauban ya tuntsure da ita ya shafa kansa yana fad'in “Aunty jeki sama kisha kallo mana”. ya shige d'akinsa yana cigaba da dariyarsa. Itama dariyar tayi, a fili tace, “Munaya kin biyamu wlhy, ALLAH ya bamu ikon miki halacci kema fiye da wanda kikai mana”. Nane, “amin waunti mimi😄”. )*()*()*()*()*()*()*()*()*()*()*( To yau dai ga Munaya ga Munubiya a gida, gaban innarsu, ga y'an k'annensu, abin sha'awar harda k'arin y'ay'ansu, ita kanta Innarsu kallo d'aya zai tabbatar maka da farin cikin datake a ciki, badan aureba mixai rabata da y'an y'ay'anta masu tausayinta. Ranar dai haka muka kusan kwana hira da labaran yaushe gamo, kota yaranma bamayi sai laraba ce da innarmu kemana magana akan mu shayar dasu. Washe garima mun tashi cikin farin cikin kasancewa da juna, aka dama mana kunun kanwa mai rai da lafiya, yanata k'amshin kayan yaji, ga k'osai mai dad'i a gefe, munacin kayanmu muna hira, Fauziyya ta shigo itama tsaf da ita, jegon ya kar6eta sosai, rungume juna mukayi ni da ita cikin kewa, itama ta zauna muka cigaba da karin kumallon tare, anan take bamu labarin wahalar datasha wajen haihuwa, yanzu hakama ita ba'a mata wankan jegon, saboda jininta yak'i sauka, sosai Muka tausaya mata, da fatan samun lafiya a gareta, nace muma ai munsha wahalar, nabasu labarin nak'udar kwana uku danasha kafin mu taho Nigeria, Munubiya harda hawayenta, dukda itama tasha tata azabar. Inna dai da Laraba najinsu daga tsohon d'akin su Munayar suna musu dariya, sunsha hirarsu har d'agawar hantsi, saida aka aiko kiran Fauziyya yaronta Na kuka sannan tamik'e ta tafi. A sannan ne Innaro ta shigo gidan, dama kullum takanzo taga masu jegon, d'akin kowa ta shiga taga sauran, Dan ita Safara'u ma takusa komawa, tunda itace ta fara haihuwa itada Haleematu. Ni da Munubiya muka gaida Innaro, amsa muna tayi babu yabo babu fallasa, hakkane ya sakani shareta nacigaba da latsa wayar Munubiya da ke hannuna. Innarmu ta fito daga d'aki d'auke da Abdurraheem daya farka yana kuka. Innaro ta wani bud'e baki da rik'e ha6a tana kalon innarmu, cikin tafa hannaye tace, “O ni Marwanatu, yanzu nan Ai'sha jikan farinne kike mamuk'a haka tamkar wani autanki?”. Kallon juna Mukayi ni da Munubiya, sannan muka kalli innaro, ganin Innarmu ta tsaya sororo alamar tad'anji kunya sai Munubiya ta mik'e, inda take taje ta amsa Abdurraheem d'in. “la'ilahailllahu..”. Innaro tafad'a cikin mik'ewa a zabure alamar mamaki, tace, “A lallai duniya tazo k'arshe, ke kinmafi uwar taku ashe? Dagani

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});