Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

farin ciki mai tsanani dajin k'arin k'aunar Ahalin Galadima. ****** Saida shagalin bikin salla ya lafa nasamu zuwa gidanmu da zagaya dangi, kowa yayi farin cikin ganina, musamman ma Munubiya da Innarmu, su Aiyaan da sauran jama'ar gidanmu, jikin Innaro yayi tsanani, dan harma ana shirin kaita asibiti, ciwon k'afa ya takura mata ainun. Sati biyu dagama bikin salla tawagar masarautar su Momma sukazo daga Niger, a masarautar gagara badau suka sauka, kasancewar harda uban gayya Sarki. Wani k'warya-k'waryar biki zuwan nasu yazama a masarautar, tareda k'ulla alak'a mai matuk'ar k'arfi wadda ada babu ita, da safe Matan suka koma gidanmu akabar Sarki da jiga-jigansa anan. A wannan zuwane aka nemi auren Ayusher, saima Abbansu ya tak'aita musu wahala akan a d'aura auren kawai baki d'aya kowa ya huta. Kowa yayi murna da hakan k'wai da gaske..............โœ๐Ÿป *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*๐Ÿ˜ญ๐Ÿ™๐Ÿผ [8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing๐Ÿ“ฒ_* *_๐Ÿ’กHASKE WRITERS ASSO...._* *_โ™ฆRAINA KAMA...!!โ™ฆ_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce๐Ÿค™๐Ÿป_* ______________________ *_My Ayusher Muh'd kema ga naki, a koda yaushe kina cikin zuciyar bilyn Abdull, alkairin ALLAH yakai gareki har gadon barci tawan_*๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜๐Ÿ‘๐Ÿป *_Maman kadee kina ina, maza garzayo ki kar6i k'undumemiyar gaisuwa ga bilyn Abdull, ina yinki ever y'ar uwa rabin jiki, ked'in tadabance wlhy a gareni, ALLAH ya raya mana kadeen mu har lokacin aure mu kwaso shoki๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ‘๐Ÿป๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคธ๐Ÿปโ€โ™€._* _____________________ *_BOOK 3_* ๐Ÿ‘‰๐Ÿป3โƒฃ1โƒฃ .................Randa sukaje gidanmu ai munsha kallo da mamaki, yau ga babban Sarki har cikin gida, dan Sarki cewa yay saiya taka har d'akunan y'an uwansa, hakan yayma Innarmu dad'i, koba komai jama'ar gidanmu zasu kuma ganin martabarta. Aiko sun gani, dan ko rantsuwa nayi babu kaffara wasu saisunyi kukan fili bama na zuciya kawaiba. Ranar anguwarmu cika tayi mak'il da jama'a. A wannan zuwane Innarmu ta fara taka nawa d'akin itama, dan tana zuwa gaida ahalinta masarauta saboda anan aka saukesu, dan haka Galadima yake sakawa a d'akkota duk bayan kwana 2 susha hirar zuminci, duk da Sarkine dawasu manyan y'an rakiyarsa ne kawai a masarautar, sauran mata dasu Badeerah duk suna gidanmu, wasu kuma gidansu Ayusher. Kwanansu goma ciff aka d'aura auren Yarima Issifu da amaryarsa Ayusher, wannan aure yasaka kowa farin ciki da annashuwa, anyi biki na kwanaki biyu anan muka shilla Niger kaita, a can kuma aka d'auro auren Badeerah da Yaa Fadeel, kwanakinmu Biyar anashan shagali maiban mamaki da birgewa, muka d'akko amaryar Yaa Fadeel muka dawo gida. Koda muka dawo babu zama, dan kuwa hidimar bikin aunty salama muka shiga, Wanda yanemi had'ewa Dana Muftahu da Matawalle, zakusha mamaki idan nace Muku Samha Ce matar Muftahu๐Ÿ˜, wannan had'i ALLAH yayishine bisa umarnin Momma, kowa kuma ya kar6a da hannu biyu yay addu'a, koda Samha taso bijirewa bisa ga soyayyar Gopal nice naita tausarta da mata nasiha harta kwantar da hankalinta. Munsha shagali kam iya shagali, babu abinda zamucema ALLAH sai godiya dakuma bin amare da angwaye da addu'a. Aiko wad'annan bukukuwa sai suka tada tsumin Nuren shima, yace aure shima yakeso, kai tsaye kuma ya kawo Farhat d'iyar Minister a matsayin za6insa, su Papi basuk'iba, domin nagartar mahaifiyar yarinyar ya cancanci a aureta, hakan kuwa akayi, shima aka sanya bikinsa kusa, mukasha biki kuwa cikeda nishad'i da farin ciki. ************* Bayan kammala wad'annan bukukuwa mukajema Aunty Salamah gaisuwa, da tayata murna ta musamman ni da Munubiya, tarba tamana mai k'yau da mutuntawa, a hirar da muka gudanar nake mata tambaya gameda mitasani ga Galadima?, dan naga yaranta sun kasance yaransa na wajen aiki. Murmushi tayi tana sakama Meenal pampas, โ€œBabu wata alak'a tsakaninmu, Ameer k'aninane uwa d'aya uba d'aya, sanan mu y'ay'ane ga Baba Rabilu da zakiji yana fad'a, har akayi aurenki da Galadima bansan akwai alak'a tsakanin Mahaifina da shiba, duk da nasan kad'an daga cikin labarin mahaifina, sai a dalilin satar Muftahu da mukayi, ta wannan hanyarne kuma mahaifina baba Rabilu yasamu ganawa da Galadima ma, akuma wannan lokacinne duk muka San komai gameda abinda yafaru, ashema yanakan Sani ya saka Ameer aikin C.I.D, bisa tsatstsauran bincike daya dad'a yanayine ya gano Galadima yanama hukumar DSS aiki, shiyyasa yatura Ameer ga hukumar dan neman kusanci dashi, wannan shine kawai abinda na saniโ€. Daga ni har Munubiya munsha mamaki da girmama hukumar Ubangiji, dan shine ya sanya alak'a tsakaninmu da aunty salamah batareda sanin junaba ko wani dalili, ni dai ALLAH yariga ya k'addara nice dama matar Galadima, shiyyasa ya kulla bisaga hikimarsa wadda wasu wawaye suka kalla a matsayin nasararsu. Satinmu biyu da zuwa gidan aunty salamah mukaje India ni da Galadima, halattar bikin Akash da Doctor Erfan Fahad, abin mamaki da al'ajab saiga Radha a matsayin matar Akash, matan Dana ta6a had'uwa dasu a shagon kayan yara na Galadima, lokacim inada cikinsu Abdurrahman, masu yara Vishnu, Ashe ita k'anwar Maman Vishnu d'ince. Aiko muka rungume juna cikin tsantsar farin ciki da annashuwa, ashema munsan juna, vishnu ya k'ara girma abinsa, sai dai bai ganeniba ma๐Ÿ˜Š. Ana gama bikin Akash muka nufi Kashmir bikin Dr Erfan Fahad da tashi amaryar shima, nanma mun rakwashe mun kwalla kamar babu gobe. Daga nan muka dawo India muka baje kolin soyayya, duk da ni yanzuma banajin dad'in gidan babu su Momma, sainaita k'iyasta rayuwar damukayi aciki a baya, wani nayi kuka wani dariya, Ashe 6angaren Galadima ma hakance yafaru, rayuwa kenan tsarin ubangiji. Mune har k'auyen su Khumar, shima kuku munje nasu gida. Saida muka kwashe kusan watanni biyu a wannan zuwa sannan muka dawo bisa samun labarin rikicewar jikin innaro. A lokacin su Amaturrahman suna rarrafensu ko ina, harma sukan gwada mik'ewa tsaye, dan suna wata na 10 ne, danma tafiyar kamar tamusu nauyine. Isowar dare mukayi, dan haka washe gari tunda safe muka nufi asibitin da aka kwantar na innaro. Hankalina yatashi ganin yanda Innaro ta koma, dukta tsotse takuma tsufa. Na zauna bakin gadon ina kama hannunta da share hawaye, dukkan ahalin gidanmu mazata da mata na ma'auri suna asibitin. Innaro ta kalleni tana murmushi k'arfin hali, da ido taima Innarmu magana akan tazo kusa da ita. Innarmu ta share hawayen idonta ta k'araso gaban gadon ta durk'usa, hannuna innaro ta saki ta kama na Innarmu. Ahankali ta fara fad'in, โ€œAi'sha ki gafarceni, nasan na aikata miki kurakurai da zalunci iri-iri, na manta da duniya bakomai bace a wajen Bawa balle kayan cikinta, idan babu mutuwa akwai tsufa, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, duk yanda ka d'auki kanka hakan kake kasancewa, ko a auren yaranan da y'ay'an alhaji halluru na zalunceki, amma nayi nadama tun a auren su da mazajensu na yanzu, y'an biyu dan ALLAH Ku yafemin kuma, amatsayinku na jikokina ban muku adalciba, son zuciyane kawai da rashin hangen nesa, yafiyarku itace babban gatana, ina kuma rok'onku kumin Afuwa domin ALLAHโ€. Atare ni da Munubiya da Innarmu muka had'a baki wajen fad'in, duk mun yafe miki Innaro, ALLAH ya yafe mana baki d'aya, kin Isa damune ai, kuma Bawa baya zartama k'addararsa da bitar rubutaccen littafinsa tundaga cikin uwa. ALLAH ya baki lafiya dai. Innaro tayi murmushi mai ciwo tana hawaye, ta juya ga y'ay'anta su Abbanmu da gwaggo Safiyya suma tana Neman gafararsu. Suma duk d'urk'ushewa sukai a k'asa suna Neman tata gafarar, matan gidanmu duksai jikinsu yay sanyi, suma suka durk'usa suna Neman gafararta, ta rok'esu akan suma su canja Dan ALLAH. Cikin awannin dabasu gaza biyuba

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});