Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsakin yace, “inhar taci gaba damin zancen wani wawa lallai zan datse harshenta wataran”. 6oyayyan murmushi Muftahu yayi, a zuciyarsa yana jero hamdala wa ubangiji, dan babu abinda yake hange tattare da galadima sai tsantsar kishin matarsa, dukda baisan miya had'asuba yaji dad'in hakan, koba komai yanzu ya fita daga damuwa da fargabar rabuwar wannan auren. cikin son kuma fahimtar wani Abu yace, “to amma ranka ya dad'e yazamuyi idan lokacin rabuwarku yayi kenan? Kasanfa alk'awarin da mukai mata”. “Oho! Maka”. Galadima ya fad'a cikin tsananin fusata. Da k'yar Muftahu ya iya had'iye dariyarsa, bai sake cewa komaiba har suka isa gidan baffi, dan karya mazgeshi a banza. Muftahu ya fita domin nema masa ison shiga ciki, a lokacinne yasamu yay dariyarsa mai isarsa, lallai Galadima akwai kishi, tashin hankali, irin wannan ajiyar zuciya haka. *************************** Tunda na shiga Munubiya take bina da kallo, ta ce, “ina yaran?”. “Suna can”. ‘nafad'a ina shigewata ciki’. K'ala bata sake cewaba tafita abinta. Har dare ina fushi, nak'i kula kowa, innarmu yitai kamarma batasan inayiba, dukda batasan mike damunaba, Munubiya ma shareni tayi, sai laraba Ce ke tambayata kodai banajin dad'ine?, nace a'a. __________________________ Saida Muftahu ya raka Galadima har falon Baffi sannan yace zaije ya dawo kafin su gama. kansa kawai ya d'aga masa amma bai tankaba. Fitar Muftahu babu dad'ewa baffi ya fito shima, zama yay idonsa akan Galadima, dan ganinsa cikin damuwa, “d'an baffi miya farune haka?”. Galadima yafara k'ok'arin saita kansa cikin k'ak'aro murmushi yace, “Babu komai Baffi”. Duk da bai gamsu ba saiya k'yaleshi, dan maybe ba huruminsa baneba, yace “Alhaji Rabilu yakai maka bak'o ko?”. “Eh d'azunnan muka rabu dasu, abindama ya kawoni kenan, dan ina ganin insha ALLAH mun sami dukkan bakin zaren, zan fara aikina kawai”. Murmushi baffi yayi yana gyara zamansa, yace, “eh to ansami bakin zare kuma ba'a samuba, dan yanzu binciko Wanda Camera d'in take hannunsa shine babban aikin dake gabanmu, dan itace babbar hujjarmu bayan d'unbin hujjoji da muke dasu a k'asa”. Galadima ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina kai, “hakane Baffi, amma akwai dai wasu y'an bayanai danake dasu a hannu yanzu haka, sai dai banida tabbacin dai-dai ne? Kokuwa akasin haka, amma kama SD da mukayi shine zai fito da gaskiyar hasashen nawa”. “To shikenan, ALLAH yasa muji alkairi”. “Amin, saidai ni a bayanin Baba Rabilu akwai abinda har yanzu yakemin rawa a zuciya”. “tofa, minene kenan?”. “Maganar siyasa dayacemin ya shiga a wancan shekarun, bayan kuma lokacin mulkin sojane, kenan wace siyasa sukayi?”. Baffi yay murmushi, “wato abinda na fuskanta anan shine, yasako kalmar siyasa ne domin mu mufasa sauran bak'in da kanmu, amma tabbas a wancan lokacin babu wata jam'iyyar siyasa, wayema ya Isa d'aga murya akan mulkine? Saidai bincikena ya nuna Dalilin kafa Group nasu tanderu yanada nasaba da son kafa mulkin farar hula, wato sunason mulki yabar hannun sojoji kenan, saidai a 6oye sukeyin dukkan abinsu, har suka ringa jawo ra'ayin mutane mabanbanta a cikin tafiyar tasu, abinda na kasa fahimta nima shine, shin sunjawo Alhaji Rabilu ne dansu tabbatar Camera na hannunsa? Kokuwa shine yakai kansa garesu domin lek'en asiri? Dole cikin biyunnan a samu d'aya, kodan yunk'urin kasheshi da suka saka Darma yayi”. Galadima dayay shiru yana fassara zancen Baffi dak'i-daki ya shiga jinjina kansa alamar gamsuwa da bayaninsa, zuwa can yace, “Baffi ka bani kwanaki biyu zanyi bincike insha ALLAH, dan zan tattauna da SD da kuma Harun, sannan akwai yaron da aka saka yay aikin da aka buga a jaridarnan, shima inason yazo hannuna insha ALLAH ”. “ALLAH ya cigaba da dafa maka, Yakuma tsareka da dukkan sharri, lallai ka ringa kulawa, dan yanzu dukkan wata hanya da zasubi domin cuta maka sun tanadeta, karka d'auka suma basa bibiyar lamarinka kamar yanda kake bibiyar nasu, dan ranar naga Alhaji Abdul- Naseer da wani masanin Computer, saidai shi bai ganniba, nasha jinin jikina kwarai da gaske, amma nikam inamason tambayarka, minene alak'ar Surukinka da senator halluru ne?”. “kamar dai abokinsa ne baffi”. “Ok! Ok! To lallai ka sanar masa ya lura, dan Senator Halluru yaronsu tanderune, za'a iya bi ta hanyar surukinka a 6ata mana aiki, tunda sun san akwai alak'a tsakanin kai da shi”. “wannan gaskiyane Baffi”. Sun cigaba da tattaunawa akan matsalolin da ayanzu zasu fuskanta, baffi na kuma bama Galadima dabaru a shara'ance Wanda bazai aikata abinda shima zai rufta ba. Sai dare ya koma masarauta, yinin yau gaba d'aya a tsaye yayisa, shiyyasa duk jikinsa ciwo yake masa, yanayin zirga-zirga amma ba irin wannanba mai cikeda cajin kwakwalwa da rikitar tunani. Ga maganganun Munaya dake cin ransa, ya tabbata duk gaskiya ta fad'a, hakan datake yana kuma tabbatar masa da tasan darajar kanta, inda watace shiru zatayi sai yanda yaso yi da ita, duk kuma abinda zai mata koda Mara k'yaune zata shanye saboda kasancewarsa d'an wani, amma duk da kasantuwarta mace kuma wadda take k'ark'ashin mulkinsu ALLAH bai sakama zuciyarta tsoro ko kwad'ayi ba, itadai kullum burinta shine asan darajarta da kimar ahalinta, sa6anin y'an matan yanzu da duniyar Ce kawai burinsu da son ganinta a tafin hannunsu, auren mai kud'i ko mulki, mai k'yau ajin farko, na nunama k'awaye da yin alfahari a duniya, yasan darajarta kona iyayenta wannan ba matsalarta bace, yanada addini ko kula da addinin shiyya Sani, son gaskiya yake mata ko albarkatun jikinta yakeso batada matsala, ya zube a kujera yana sauke tagwayen numfashi. Sauban dake zaune yana kallo yakuma kallonsa, yayansu na bashi tausayi, saidai shi taurinkai da rashin yarda da kowansa ke had'ashi dashi, amma ta wani fannin yakan kalli hakan a matsayin gaskiyarsa, dan massarautar tasuce abar tsoro, ba kowane abin yardaba, yanda zaka tantance na kirkin shine mai wahalar kuma. ********************* Na kasa hak'uri da danne maganganun Galadima, hakanne ya sakani yanke shawarar tambayar Munubiya kota Sani, saida mukai shirin barci dukda sharenin da takeyi nadai danne nawa Fushin na zauna kusa da ita tana shayar da Meenat data tashi. Kan yarinyar na shafa sannan nace “Munubiya in tambayeki mana please?”. Kamar bazata kulaniba sai kuma ta kalleni. Tace, “Ina saurarenki”. Ajiyar zuciya nayi ina gyara zamana, nace, “dan ALLAH idan namiji yace gonarsa mi yake nufi?”. Jimm tayi alamar tunani, ta kwantar da meenat tana fad'in “Matarsa”. Da mamaki na kalleta, yayinda wani sanyi ya ratsa raina, amma na danne....... Ta katseni da fad'in “Munaya ki fito fili ki sanarmin abinda ke faruwa, kinsan banason kwana-kwana, sirrinki keda mijinkine kawai a rayuwa bazanso saniba, domin ALLAH ya haramta bud'e wannan, saikuma yankin sirrinsa na rayuwa Wanda yarda da matarsane kawai zaisa ya fad'a mata, shima wannan kirik'e masashi, amma Munaya na fuskanci har yanzu babu dai-daito tsakaninki da mijinki, duk da kin sanarmin da manufar aurenku nazata darajar zuri'ar data shigo tsakkiyarku zai kawo muku sasanci Ku manta da wani auren Contract, duk da na fahimci mijinki jinin mulki na yawo a jikinsa, danne Abu a rai da basar dashi tamkar jinin jikinsa yake, kekam nasan halinki mutumce maison a damu da ita, sannan a nuna mata komai a aikace da furucin baki, kema danaki jinkan Wanda bansan gidan uwarwa kika samoshiba, amma mike wakana a duniyar aurenki? Mikuma kuke shiryawa keda surukarki?”. Shiru nayi nakasa magana, dan banso fitar da wannan sirrinba har zuwa lokacin da

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});