Chapter 58
Chapter 58
mun Isa lafiya, Khumar da Samha, aunty Mimi sukazo tararmu, bama tamu sukeba ta yaran sukeyi, ganin haka Galadima yaja hannuna muka shige mota, saida suka gama murnarsu sannan suka shigo, aunty Mimi na fad'in, “Oh shine kuka shige mota?”. Galadima yabata amsa da cewa, “Tunda batamu akeba mizamu zaunayi”. Dariya ta sanya da fad'in “yau naga kishi, to kuma dai sannunku badan halinkuba”. Murmushi nayi ina gaisheta, Samha ta mak'alk'aleni. Haka dai muka k'arasa gida. Momma da jakadiya duk suna a harabar gidan da sauran hadimai mazan da mata. Kowa burinsa yaga yaran. Momma dai Nita rungume tanamin oyoyo. Kunya dukta kamani, ina k'aunar wannan baiwa har cikin raina wlhy. Galadima kam jingina yay da mota kawai yana kallonsu cikeda jin dad'in yanda kowa ke farin cikin dawowar iyalansa. Saida muka shiga ciki sannan Momma kecewa “Ina uban gayyar wai?”. Galadima dake shigowa a k'arshe yace, “gani a anan, naga batani akeba Momma shiyyasa naja gefe”. Duk dariya mukayi, yayinda bayin sukai k'asa da kai duk suna k'umshe tasu, dan babu damar yi. An shiga gaishe-gaishe damana sannu da zuwa, hadiman gidan duk suka fice aka barmu mu kad'ai. Momma duk tana rungume da jikokinta wad'anda suke rikid'ewa ruwa biyu, kamannin Galadima da Munaya, Khaleel ma yabi ya mamuk'e mata. Galadima ya mik'e ya haye sama, danya d'an watsa ruwa, gashima magrib tagabato anan. Momma harda hawayenta najin dad'i da farin ciki. Tofa lamari ya canja salo, a wannan karon dai maimakon Momma tace nabi mijina saitace na shiga d'akinta nayi wanka na huta, aunty Mimi kuma ta kwashi yaran da taimakon Samha zata musu wanka. Nikam hakan yamun dad'i, dan dama banason zama d'aki d'aya dashi. A d'akin Momma nai wanka na canja kayana, ina shirin kwanciya Samha ta shigo kirana wainazo naci abinci. Galadima yay ta zuba idon shigiwar Munaya amma saiyaji bulum. Da farko bai kawo komai a ransaba yashiga toilet danya watsa ruwa, jikinsa babu k'arfi har lokacin, dayake d'akin tsaf yake an gyara ko ina fes yanata k'amshi. Mamaki yakuma kamashi daya fito har sannan babu Munaya babu dalilinta, ko mai bai shafaba ya zura jallabiya ya sakko, Momma na zaune a falo, harya gama sakkowa idonta na kansa, duk sai ya rame mata a ido, ga hancinsa yay jajir alamar mura tamasa ligif, tissue d'in hannunsa ya ajiye sannan ya zauna. Momma tace, “Sannu Muh'd dukka rame, mura na wahalmin da kai wlhy”. Murmushi yad'anyi yana shafa sajensa. Yace, “My Sweet Momma to yaza'ayi, yanzu hakama kaina ciwo yake, ya muka sameku?”. “Lafiya lau, sai kewarku, ya kuka baro manasu da autana?”. “kowa lafiya, Autanki nacan nama inno ta6ara, bakiga yanda yay k'iba ba ma”. Momma tayi dariya tanacewa, “Ja'iri, da yanata zum6ure-zum6ure bazaijeba, bagashi haryaci wata kusan uku ba, kwana nawa zai gama”. “Dama ai shagwa6ace Momma”. Momma tayi murmuahi tana maida kallonta ga jakadiya dake maganar ga abinci. Sannu Tamata, ta kalli Galadima daya jingina da kujera ya lumshe ido. “Muh'd tashi ga abinci ko, kasamu ka kwanta ka huta”. Idonsa ya bud'e yana mik'ewa, saiga Samha da aunty Mimi sun fito suma. momma tace, Samha ta kira Munaya tazo taci abinci. Galadima yanaji amma baice uffanba, saima maida hankalinsa yayi ga abincin da Aunty Mimi ke zuba masa. Ya faracin abincin Samha da Munaya suka fito, kallo d'aya yamusu ya d'auke kansa zuciyarsa na mamakin miya kaita d'akin Momma?. Duk Momma na kula dashi. Itama Munayar kallonsa tad'anyi ta d'auke kai. Haka akaci abincin duk hirar dasu Momma sukeyi da Munaya Galadima baice uffanba, cin abincin sa kawai yakeyi, baima wani ci da yawaba ya matsa gefe alamar ya k'oshi. Aunty Mimi tace, “my K'ani Yaya dai?”. Yad'an yamutse fuska da fad'in “Alhmdllh ya isheni”. “Ai kai dama tsiyar murarka kenan wlhy Sameer, ta jigataka ta hanaka cin abinci, ALLAH ya kara sauk'i”. Cikin lumshe ido ya amsa da amin a saman la66a. Muma duk sannu mukai masa, ya d'aga mana kai kawai. Koda muka had'a ido saiya zubamin wata harar gargad'i, murmushi nayi na kauda kaina gefe tamkar ban ganiba.....................✍🏻 *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻 [8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_* *_💡HASKE WRITERS ASSO...._* *_♦RAINA KAMA...!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BOOK 3_* 👉🏻2⃣6⃣ .................Momma dai ta kasa ta tsare ta hanani hawa sama, idan abu Galadima ke buk'ata saitace Samha ta kai masa, tsakanina dashi saiya sakko gaidasu ko zaije massalaci, ya kumak'i nuna hakan ya damesa, sosai mamaki ya kamani, dan kwanakinmu hud'u kenan da dawowa, da farko na d'auka kawai shariyar tasa ta k'asaitace ta motsa, amma zuwa yau dayake shirin zuwa Kashmir sai abin yafara bani tsoro, dan ina zaune bakin gadon Momma ina shayar da Abdurraheem ya shigo, Momma ta fita kitchen. 'Dago ido nayi ina amsa masa sallamar da yayi, amma saiya d'auke kai tamkarma bai ganniba, ya k'araso kusa dani ya rissina ya d'auki Amaturrahman dake kwance tana motse-motse. Duk'owar dayay saitasa k'amshin turarensa bugomin a hanci sosai, na lumshe idanuna sannan na bud'e akansa, magana yake ma Amaturrahman ahankali cikeda k'asaitarnan tasa, saikace wata babba. Da kamar nima zan shareshi, saidai na daure nace, “Ina kwana”. “Lafiya”. Ya amsa batareda ya kalli inda nakeba. Hakan yamin ciwo a rai, na dangwarar da Abdurraheem d'in akan gado batareda ya k'oshiba, aiko saiya saka kuka, banbi takansaba na shige bathroom abuna. Da kallo Galadima ya bita cikeda takaici harta shige, ya cije lips nashi tamkar zai huda da hak'ori, idanunnan harsun kad'a da 6acin rai. Yana k'ok'arin tashi ya d'aukeshi Momma ta shigo d'auke da k'aramin Kofi ma Magani daza'a basu. K'arasowa tai dad'an hanzari tana fad'in “shikuma wannan mi akai masa?”. Ita bama ta lura da Galadima ba, amma taji k'amshin turarensa. Kwafar da yayi yasaka Momma juyowa ta kallesa bayan ta d'auki Abdurraheem d'in. “Wai dama kana d'akin amma yake kuka? Ina Munayar ne?”. Baice komaiba sai bayi ya nuna mata da hannu, hakan yasata fahimtar ransa a 6ace yake, ta zauna tana shafa bayan yaron, yayinda shikuma ya daina kukan. A kausashe Galadima yace, “Momma idan bazata iyaba na nemo masu kulamarmin da yara, dan bazan d'auki wannan wulak'ancinba, ta k'auracemin na k'yaleta tayi duk yanda ta gadama, shine yanzu kuma abin akan yarana zai dawo, nifa wlhy......” Dakatar dashi Momma tai ta hanyar d'aga masa hannu, “ya Isa haka Muh'd, Munaya dai matarkace, kuma lafiyar ALLAH kuka dawo k'asarnan, aganina tun washe garin dawowarku kaga batazo inda kakeba yakamata ka tambayeta miye dalili? Amma ka share tamkarma hakan bai damekaba, shin mulki haukane Muh'd? Indai kace zakaima mace izza da mulki wlhy kana tare da wahala, dan ba kowace mace bace zata d'auka, gaka da zuciyar tsiya saikace kuturu, ni nasan minene matsalarkune balle na sasantaku? Kuka Sani, inma zaku shekara a hakane kuyita zama babu ruwana wlhy”. Shiru Galadima yay yakasa magana, zuciyarsa sai zafi take masa. Momma kam ta d'auki Abdurraheem da maganinsu tayi ficewarta tabar musu d'akin, sumaci Kansu ita babu ruwanta. Kansa ya dafe cike da takaici, shi yarasa gane kan Munaya, da farko yabartane yaga iya gudun ruwanta, a tunaninsa ko kunyace, amma daga baya saiya fahimci ba haka bane, wani tsirin ne kawai take Neman k'irk'ira, kud'i ya ajiye mata shima ya fice d'auke da y'arsa a kafad'a. Munaya dake a bayi tana kuka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83