Chapter 3
Chapter 3
martaba dayake hutawa idan baya buk'atar ganin kowa har matarsa ya iskeshi, yayi mamaki kwarai, dan inhar mai martaba ya shiga falonnan kofa mama Fulani sai dai tayi hak'uri da ganinsa. Yana kishingid'e saman tattausar darduma da aka k'awata da kilisa ta asalin sarakuna masuji da tsantsar mulki, ga tumtum da sauran kayan k'awa, an saka na'urar dake d'umama d'aki kad'an saboda yanayin sanyin safiya musamman na wannan lokacin da bazara take kunno kai. Da hannu mai martaba yayma Galadima nuni da kusa dashi, Galadima yaje ya zauna yana tankwashe kafafu, cikin girmamawa ya risinar da kai yana fad'in “barka da asuba Abba”. Mai martaba ya jinjina kai yana lumshe ido da amsa cikin fad'in, “barka dai yarona, ina d'iya ta da abokaina da amarya?”. Murmushi Galadima yayi, kansa a k'asa yace, “duk suna lafiya Abba”. “Masha ALLAH, yaya jikin naka to?”. “Na warke ai Ranka ya dad'e”. “To Alhmdllh, haka akeso ai, Yaya maganar tafiyar ita mai d'akin naka? duk da dai abin yazo da tsoratarwa yakamata a ayi yanda kowa yakeyi Sameer, ALLAH shine mai tsarewa, kuma zai tsaresu, domin ransu a hannunsa yake, idan an hanata zuwa an tauye hak'inta, zakuma ta iya ganin hakan kamar ita danba wata baceba, nagama shirya komai yau za'amata rakkiya kamar yadda akema kowacce mace dake aure a masarautarnan”. Cikin had'iye yawu da wani Abu daya tokare mak'oahinsa yace, “to Abba, ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, nima zuwa yamma zan koma India, akwai abubuwan da zanyi na kwanaki biyu zuwa uku zan dawo”. Mai martaba yay murmushinsu irin na manya, cikin jinjina kai ya ajiye k'aramin mug d'in hannunsa mai k'yau yana fad'in “ALLAH ya taimaka, Maybe kana dawowa nima zanje insha ALLAH”. Galadima yace, “ALLAH ya kaimu”. Daga nan sund'an cigaba da ta6a hira, a haka jakadiya ta shigo nemawa matawalle iso, yabada izinin a shigo dashi. bayan shigowarsa da yin gaisuwa sai suka d'ora hirar su uku gwanin sha'awa da birgewa. da Wanbai yazo gaida Sarki jakadiya ta sanar masa ai Galadima da matawalle suna ciki, shi komawa yay wai yafasa gaisuwar, jakadiya ta ta6e baki tana 6azgar goro da fad'in “kaikuma kasani gwandararren banza, kai koma y'ar k'autarnan ta jinin girma ba iyawa kaiba, dakasha kanu da sirrika a wajena wlhy”. duk a hankali take maganar yanda kowa bazai jitaba🤣. Saida gari yay tangaran da haske sannan Galadima da matawalle suka fito, suka bar Sarki zaiyi shirin zuwa fada. Koda Galadima ya dawo sashensa wajensu Munaya ya nufa, saboda jiyo kukan yaransa. Ya iske Ashe wanka ake musu, Munaya kuma tana wankan itama, sai Samha da Sauban keta faman jijjigarsu a kafad'a, Abdurrahman kuma yana hannun laraba tana masa wanka. duk gaidashi suka shigayi, ya amsa musu cikin jinjina kai da lumshe ido, baki kam ko motsi bai yiba. Samha ta kawo masa Amaturrahman dake hannunta, bai d'auketa ba, ya dai shafa kumatun yarinyar yana murmushi, sai tayi shiru tana kallonsa kaikace tasan wanene. Murmushinsa ya fad'ad'a yana jan d'an hancinta. Samha tace, “Uncle Sam ALLAH Amaturrahman tafi su Abdurraheem wayo, shiyyasa nafi ji da ita”. Murmushi yakumayi, ya shafi muskar Samha itama tareda d'an bubbugawa, hakan ya sakata fahimtar yau babu y'an maganar a kusa. Saima ya juya yay ficewarsa abinsa daga d'akin. d'akinsa ya koma ya sake wanka da shirin fita cikin wani d'anyen boyal fari tas, anmasa surfani da golden color sai walk'iya yake da d'aukar idanu, takalmansa na ainahin masu sarauta half cover da lankwasarsu a gaba suma fari da kwalliyar Golden d'in, ya matsa gaban Mirror yana kallon kansa da d'aura a gogo, ganin komai dai-dai ya d'auki turarensa ya fesa kala-kala sannan ya zuba wayoyinsa a aljihu da d'aukar links d'in hannun rigar yafice yana k'ok'arin sakawa. Da Sauban sukaci karo, yabisa da kallon birgewa, kai manyan kaya na matuk'ar k'awata k'yawun dirin yayansa, kuma sai akayi sa'a yana masifar sonsu, Dan ko'a India yakan sakasu fiyeda k'ananum kaya ko suit. Zungurinsa galadima yayi yana fad'in “baka sanni bane?”. Ajiyar zuciya Sauban ya sauke, yana sosa k'eya, “Yaa Sam please one pic.. Mana”. Galadima ya hararesa zai cigaba da tafiya, da sauri Sauban yakuma had'e hannanyen sa alamar rok'o. Galadima yay guntun tsaki, “kaiwai shin mikake da hotone? kullum baka gajiya da tarasu”. ya k'are maganar yana d'an dafe goshi. Shidai Sauban ya marairaice, babu yanda Galadima ya iya dole ya yarda yamasa hoton, harda zuwa sukayi tare. Shidai Galadima ya girgiza kai kawai ya nufi sashen Munaya. Ya isketa taci gayunta cikin doguwar riga ta popul d'in material, tayi d'as da ita, bazaka ta6a kallonta kace itace da yara uku ba, tana zaune tana bama Abdurraheem nono, sauran kuma suna hannun Samha, laraba tafita.. Zama yay kusada Munaya ya kar6i sauran yaran a hannun Samha, ya d'an rankwafa kan Munaya yana kama hannun Abduraheem data cire a nono ta gyara rigarta, da sauri ta d'ago tana kallonsa da mamakin koya manta Samha na d'akin dazai wani shige mata, shima kallonta yayi yana d'age gira d'aya fuska babu walwala. Hakan kam saiya bama Samha damar yimusu hoto jiki na rawa, Dan ba k'aramin bada kala sukayiba😘. Hasken camera d'in ya saka su d'agowa duk suka kalleta, wani ta sake k'yastawa ta fita da gudu. Munaya ta saka hannu tana toshe bakinta saboda dariyar dake Neman kufce mata, shikam kwafa yay yana fad'in “zan kamaki ne Dan k'aniyarki, yara duk sunbi sun rainani”. Dariyar Munaya ta fito Dan takasa rik'eta, hararta yayi dukda dariyar tata tamasa k'yau, yad'an rankwasheta akai, “kece kika sakasu ko? dama ai Sauban shima titsiyeni yayi”. Daina dariyar tayi ta turo baki gaba tana tsafa inda ya rankwasheta, “yoni mizanyi da wani hotonka malam”. “waya Sani ko sokike ki mallakeni”. Baya Munaya tayi tana kallonsa, ya wani basar tamkar bashine yay maganarba, ya hauma yaransa wasa dukda basusan mima yakeyiba. Dan gwarar da Abdurraheem tayi gefensa tana mik'ewa, “Humm, ko inason mallaka bazan mallaki abinda bai minba”. Yi yay tamkar bai jita ba, yabama yaransa gaba d'aya hankalinsa. Munaya taji haushin k'in kulatan da yayi, yakai mintuna 30 a d'akin kafin yay kissing kumatunsu ya ajiyesu. inda Munaya take tsaye jikin mirror tana kallonsu ya nufa ta d'auke kanta tana maidawa gefe. Gabanta ya tsaya daf har tanajin hucin numfashinsa, hannunsa duka cikin aljihun rigar boyal d'insa 3Quarter, “Na dawo gareki, idan kin Isa maimaita abinda kika fad'a”. Tasan halinsa da makomar maimaicin, shiyyasa ta ta6e baki tana cewa, “aini ba'a sakani abinda ban niyaba”. Bakinsa ya ta6e yana murmushin gefen baki, “matsoraciya kawai”. yafad'a yana juyawa zai fita, saida yaje bakin k'ofa sannan ya kalli agogonsa, “kuzama a shiri, dana dawo....”. Bai k'arasa ba yay ficewarsa. Da mamaki Munaya tace “daka dawo? To daka dawo za'yi mi?”. Batada mai bata amsa dan haka ta share ta koma kusada yaran. Da hanzari Su sarkin Mota suka mik'e, aka bud'e masa mota ya shiga, sashen da aunty Mimi take suka fara zuwa, ya shiga Dan yasan tana nan tanajin haushinsa akan fitar jiya. Aiko a falo ya isketa zaune a dining tana breakfast, hadimanta nata kaikawon gyara 6angaren, dining d'in ya nufa yaja kujera ya zauna, idonsa a kanta, ta shareshi tamkar batasan dashiba, shima baice uffanba ya d'auki spoon ya saka a plate d'in da take cin Arish,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83