Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

aunty Mimi murmushi kawai take da wannan rigima tasu dabata k'arewa, dama can inhar Nuren da Galadima Na waje sai kayi dariya, Dan kafin su rabu sai anyi kusan fad'a goma. Galadima yace, “Ya jikin?”. “Aini kam Alhmdllh, yanzu kawai maganar gaskiya amin aure, inda Na mutufa shikenan, kukan kwana uku zakuyi a wuce wajen, amma in mat......” Hannu Galadima yakai zai bige bakinsa, yay saurin duk'ewa, Aunty Mimi ta sanya dariya, Galadima kuwa kwafa yay yana kallon Aunty Mimi, “oh ALLAH, maimakon kimasa fad'a dariyama kike masa? Wannan yaron wlhy fitsararrene, idan kunk'i masa aurenan zai iya zuwa yayi baku saniba ma”. Nuren ya gyara zama yana hararsa, “Yo angaya maka ni irinkane, soyyaya Na cin zuciyata k'asaita ta hanani fad'e, Malam mufa dama munsan komai, munzuba idone muga yanda wasan zai k'are”. Murmushin da Galadima bai niyyar yibane ya su6uce masa, ya mik'e da fad'in, “Duk iskancin da kamin ninaso, tunda nine nazo dubaka, idan nakuma zuwa d'akinnan kace ba sunanka Nureddin ba”. “Ahaf, yo dama sunana Sameer ne?”. Galadima bai kulashiba, ya kalli aunty Mimi daketa musu dariya, “Auntyna yakamata a sanarma gidansu ta farka, naga har yanzu babu Wanda ya iso”. Murmushi Aunty Mimi ta masa, ta ajiye plate d'in datake bama Nuren Abinci tana cewa, “babu damuwa, mu barsu har zuwa yammar, tunda kaga har yau basu bada damar a shigaba”. “Ok, hakan yayi”. Harzai fice aunty Mimi tai saurin cewa “Abincinfa?”. Kansa ya girgiza mata yay ficewarsa. Nuren dake murmushi ya kalli Aunty Mimi yana fad'in “Auntynmu soyayya nacin Guy d'inan yak'i fahimta”. Dariya tayi “Nuren kenan, ingaya maka sarai yasan yana sonta, shegen son girma da miskilancine kecinsa, amma ai naga alamar yanzu an wuce wajan”. “A haba? Aunty da gaske?”. “kwarai ma kuwa Nureddin”. Hannu yabata suka tafa, yanajin wani sanyi a ransa, da sakama Muftahu albarka a zuciyarsa, danya zama aboki kuma d'an uwa Na k'warai. Fitowar Galadima yaci karo dasu Yassar, ya fad'ad'a murmushinsa, shima yaran sun shiga ransa sosai, k'arasowa sukai gareshi, cikin girmamawa duk suka gaisheshi, ya amsa da kulawa. “ku bakwa gajiya da yawo?”. Soshe-soshen kunya suka farayi, Marcel yace, “ai daga gida muke, munzo muk'ara ganin jikin Aunty da Uncle ne”. Galadima yad'an murmusa yana tura hannayensa duka a aljihu, cikin d'an lumshe ido yace, “kushiga to kugansa”. “Uncle! Auntynfa? Ta farka itama?”. ‘Ahakam ne mai maganar’ Galadima ya jinjina kai. Yace, “ta farka Ahakam, amma tana barcine”. Gaba d'ayansu farin cikine ya bayyana a fuskokinsu, kai kace y'ar uwarsuce ta jini, da wannan farin cikin suka shiga d'akin da Nuren yake, shikuma yakoma inda Munaya take murmushi d'auke a fuskarsa. Dad'an hanzarinsa ya k'arasa gareta, ganin ta farka, zama yay a kujerar suna kallon juna, murya a sanyaye yace, “Kin tashi?”. Da idanu ta amsashi. Ya shafa kanta yana fad'in “Sannu, yanzu ina ke miki ciwo?”. Fuska ta d'an yatsine, ta nuna masa hannunta da kanta. Cikin tausayawa Yakuma mata sorry, sannan yace, “mizaki ci?”. Kanta ta girgiza masa alamar babu komai. Ya d'an 6ata fuska yana fad'in “Ban yarda ba, kinga kuwa yanda kika rame?”. Murmusawa tayi, itama ta masa alamar wai ya rame shima. Baki yad'an ta6e, amma baice komaiba ya d'auka wayarsa dake kusa da ita yay kiran Muftahu akan abinda za'a kawoma Munayar kozata d'anci. Itadai kallonsa kawai takeyi. Ya yanke wayar yana kallonta shima da d'age mata gira d'aya alamar kallonfa?. Dukda taji kunya saita yamutse fuska irin miye abin kallon anan. Galadima yay wani miskilin murmushi cikin murya k'asa-k'asa yace, “Really?”. Ta lumshe idonta alamun tabbabatarwa. “zaki maimaitamin idan kin warke yarinya”. Yay maganar da wata siga harda cije lips. Munaya ta kauda idonta tamkarma bata fahimci ina ya dosa ba. A ranardai haka kowa ya yini cikin farincikin farfad'owar Munaya, gashi anbarsun sunshi sun gagganta, saidai anata musu gargad'in banda hayaniya, tausayin ta duk ya kamasu. Innaro harda hawayenta, aka saka bakin Zane ana sharewa da jemasu Alhaji balala ALLAH ya isa, harda cewa sai an koma kotu an sake sabuwar shari'a an kar6oma jikarta hak'inta. Shi Galadima ma abin dariya ya bashi matuk'a, yadai had'iye yana duk'ar da kai baiyiba, wannan tsohuwa akwai abin dariya wlhy. Munubiya kam rungumeta tayi taita hawaye, itama Munayar nayin nata. ★★★★★★***★★★★★★ Bayan kwana hud'u da farfad'owar Munaya jikinta yayi k'yau Alhmdllh, Dan tana samun kulawa ta kowanne 6angare, ciwukan jikinta ne kawai basu gama warkewaba. Aunty Mimi da Laraba na a d'akin, Dan kowa ya tafi, suna zaune d'auke da su Abdurraheem da ake kawowa su yini yanzu, sai dare a koma dasu. Munaya tana zaune ne a gadon datake jiyya an saka mata filo ta jingina, abincin da aka zuba mata taketa faman jujjuya cokali a cikinsa, tasaba kullum Galadima ke bata abincin, gashi yau tun safe da'aka kirashi ya fita bai sake dawowa asibitinba har yanzu, dukta damu, da taji motsin tahowa za'a shigo d'akin saita zata shine, sai anshigo taga bashi bane sai haushi ya kamata, Munubiya data fahimceta tsaf taita gumtse dariya har suka tafi, su Aunty Mimi hankalinsu gaba d'aya yanaga yaran, basusan mitakeyiba. Turo k'ofar da akayi ya sakasu kallon k'ofar gaba d'aya, dan k'amshin turarensa yafara musu sallama kafin shigowarsa, wayace manne a kunnensa yana magana a hankali, hannunsa d'aya cikin wandon aljihun Ash color d'in shaddarsa daketa maik'o, Munaya daketa sauke k'ananun ajiyar zuciya tunda taji k'amshinsa tad'an saci kallonsa, shima idonsa a kanta, gira ya d'aga mata, tai saurin janye idonta tana tura baki kad'an. Murmushi yayi ya zauna a bakin gadon kusada k'afafunta yana cigaba da wayarsa, yayinda yakema Amaturrahman da aka kwantar kusada ita wasa, yaran sund'an fara wayo, Dan idanuwa k'yar suyita kalle-kalle, kwanakinnan da suka dawo shan nono sunyi y'an k'u6ul-ku6ul dasu abin sha'awa. Munaya dai tafara tura abincin da k'yar, sai wani faman had'e rai takeyi, shidai Galadima dariya na cinsa a rai amma baiyiba, saidai ya saci kallonta ya maida idonsa ga Amaturrahman data rik'e d'an yatsansa gam daya saka a d'an hannunta, kaikace tasan minene. Sudai Su aunty Mimi da laraba suna cigaba da hirarsu, Dan laraba na bata labarin halinda su Abdurrahman suka shiga a kwanakin da Munaya bata farfad'oba ne. Galadima ya ajiye wayar yana d'aukar Amaturrahman da fad'in, “O my lil princess I miss you”. Ya k'are maganar da sumbatar kumatunta, sannan ya juyo suka gaisa dasu aunty Mimi dake kallonsa shida babyn tashi abin sha'awa. Cikin tsokana aunty Mimi tace, “Ai dama shirin kiranka nake danna kula my k'anwa bazataci abincin nanba sai kana kusa”. Galadima ya juya yana kallon Munaya data waro ido tanajan mayafi ta rude fuska Dan kunya, dama aunty Mimi suna kula da ita kenan, itakam taga idi. Galadima yace, “A lallai Aunty Mimi da gaskiyarki fa, kamarma kuka tayi?”. “kad'an dai ya rage tayishi my k'ani, tun d'azun ina lura da ita, rabin hankalinta naga k'ofa”. Laraba da Galadima sukayi dariya, ya kuma kallon Munaya data kasa d'ago kai ta kallesu. Galadima ya had'iye dariyar dake Neman kufce masa, ya ajiye Amaturrahman d'in yana matsowa kusa da ita, Murya k'asa-k'asa yanda su Aunty Mimi bazasujiba yace, “Any problems my Princess?”. Munaya ta saci kallon su Aunty mimi, ganin basa ganinta saita tura masa baki kad'an tana matso k'ananun hawaye. “O my God”. ‘ya fad'a a hankali

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});