Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shima an gyarashi, maganar gaskiya ranka ya dad'e bazan 6oye makaba, tasamu buguwa akai, dan ALLAH ne ya tak'aita batasamu wata babbar Matsala a brain ba, saidai ahalin yanzu dukkan wani motsi mai k'arar sauti bama buk'atarsa kusa da ita, insha ALLAH inhar za'a kiyaye cikin kwanaki kad'an komai zai iya dai-daita, takuma dawo normal kamarma komai bai faruba, zamu bata dukkan kulawar daya dace da izinin Ubangiji. daganan har kwanaki uku zuwa hud'u zata kasance a halin barci, dan hakanne kawai zai girmama nutsuwar da muke buk'atar ta samu d'in, kai kad'aine kuma zaka ringa shiga d'akin”. Galadima ya lumshe idonsa tausayin Munaya da yaransu Na kuma mamaye jinin jikinsa da kowanne ga6a, da k'yar ya iya bud'e baki yace, “Doctor! Kana ganin zaku bata dukkan kulawa?. Sannan tanada yara jinjirai, yaya kenan za'ayi?”. Insha ALLAH ALLAH ranka ya dad'e, dan munada kayan aiki a asibitin mu, dakuma kwararrun likitocin da zasu iya aiki a kowacce k'asa, maganar yara inaga inhar akwai mai kulawa dasu acigaba da basu madara har ALLAH yasa ta farfad'o, saboda mu yanzu matsalarmu kawai shine motsin dazai iya farkar da ita ko wanda zaiyi tasiri cikin brain nata”. Gyad'a kai kawai Galadima yayi, yabama doctor hannu sukayi musabaha, daganan ya fito. Kuma ficewa yayi daga cikin asibitin, Sarkin mota yay saurin biyo bayansa, da hannu yamasa alamar yashiga mota suje. Dukda sarkin mota baisan inda suka nufaba haka ya amsa cikin girmamawa. Saida suka fara tafiya ya sanar masa inda zasuje. yana nufi gidansu Munaya dan yaga halin da yaransa suke ciki. Munubiya da kanta ta fito masa dasu itada Ayusher, tausayin su ya kamashi matuk'a, musamman ma Munubiya, dan tayi wujiga-wujiga. Cikin k'arfin hali yace, “kiyi hak'uri Sister, muyi musu addu'a ita kad'ai suke buk'ata a wajenmu, yanzu yaza'ayi dasu Amaturrahman? Dan nakula kamarma yunwa sukeji?”. ‘yay maganar yana kallon yaran da sukayi barcin wahala bayan sun gama shan kuka’. Share hawaye Munubiya tayi. tace, “Yakamata a nemo musu madara, idan kuma Na shayar dasu to shikenan”. Galadima ya jinjina kansa yana fad'in “Bamusan hikimar da ALLAH ya 6oyeba a gaba, karmuyi ganganci, bara kawai a nemo madarar, dan dolene su kwana anan, ita ba'ason mata hayaniya yanzun, maybe ma harnan da wasu kwanaki, saboda ta bugu a kanta, kuskuren kwakwkwaran motsi zai iya shafar brain nata”. Munubiya takuma fashewa da kukan tausayin y'ar uwarta, hakama Ayusher, shi kansa Galadima dauriya kawai yakeyi, danma ya 6oye idanunsa cikin eyeglasses shiyyasa basa ganin nasa tsantsar damuwar. Muftahu ya kira ya sanar masa a samoma su Abdurraheem Madarar da zasu ringa sha. Daga nan gidan yabaro akan cewar Muftahu zai kawo, yakuma rok'esu akan Abdurraheem, dan ba'ason yacika yawan kuka. A gurguje please😏😜 ___________________________ *BAYAN KWANAKI UKU* A kwanaki ukunnan fad'ar tashin hankalin da bayin ALLAH suke ciki 6ata lokacine, musamman ma Galadima da har wata uwar rama yayi lokaci d'aya, hakama Munubiya da innarsu, Nuren dai ya farka tun washe garin faruwar lamarin, kuma jikinsa Alhmdllh yanata murmurewa, saidai tausayin d'an uwansa daya addabi ransa. Ko abinci Galadima bayasonci, sai Aunty Mimi ta turkesa tana bashi abaki, shima baifi yay lauma biyarba yace ya k'oshi. tayi-tayi kuma ya kafe, garama idan tea ne, shima sai an had'a da lallashi, babu abinda ke addabar ransa irin damuwar Munaya da yaransa, sukansu duksun rame, danma suna samun tsantsar kulawane ta kowanne fanni. Papi yazo ya dubasu, hakama su mom da iyayen su Nuren d'in da y'an uwansa, mai martaba ma da daddare yazo cikin 6adda kama ya dubasu. Mama Fulani ma kullum saitazo, a matan Sarki gimbiya Zulfah Ce kawai batazoba, Dan kunyama ta hanata walwala gaba d'aya a masarautar, Mai martaba kuwa ya hanata hanyar ganinsa gaba d'aya itada y'ay'anta, sai matawalle kawai daya nuna damuwa akan abinda kakansu da mahaifiyarsu suka bada gudunmawa wajen aikatawa wan mahaifinsa, sanan yay ALLAH wadai akan son zuciyarsu, koda yaushe yana tare da Galadima da Muftahu a asibitin, da wata buk'ata ta taso kafin Galadima yayi shi yayita. A koda yaushe Momma cikin kira take taji yaya jikinsu Munaya, koda wasa ba'a sanarma Abie komaiba, Dan ana ganin cigaba da haske game da jikinsa sosai, ba'a fatan wani abinda zai maido da hannun agogo baya game da ciwon nasa. Addu'oi kam sosai aka duk'ufa yinsu game da Munaya, wadda har yanzu Galadima ne kawai keda alhakin shiga ya dubata, shima sau d'aya a rana kawai, yau dai duk ake saka ran farkowarta, Dan an dakata damata dukkan wata allura dake sakata barci, saidai kuma har dare babu wani bayani. Zasu tayar da hankalinsu doctor yace suyi hak'uri, maybe zuwa dare ko safiyar gobe ta farka d'in, danba a sume takeba, barcine kawai da sune suka sakata ta hanyar mata allurar. Badan hankalin nasu ya kwantaba sukai shirun, har lokacin barinsu asibitin yayi babu wani bayani game da farkawar tata. *Washe gari*. Duk dai yanda akaso farkawar Munaya a ranar sai a washe garine ALLAH ya amince da hakan, Alhmdllh anci nasarar farkawar tata yanda ake buk'ata, saidai ciwukan jikinta a halin yanzu. Saida doctors suka gama dukkan kai kawonsu naganin komai ya ida daidaita sannan aka bama Galadima damar shiga. Tamkar mai sand'a haka ya shiga d'akin, tana kwance amma idonta biyu, sai dai a lumshe suke, an kuma cire mata bandejin da aka zagaye mata fuska, sai kad'an aka bari inda ciwon yake. Durk'usawa yay a gaban gadon, ya kamo hannunta Na haggu dakeda lafiya ya saka nashi ciki, a hankali ta bud'e idanunta saboda jin tattausan hannunsa cikin nata, ga k'amshin turarensa daya mamaye d'akin Wanda ya tabbatar mata da shid'inne, tana shak'a a hankali. Idonta ta saka cikin nasa, kowanne yakasa koda kwakwkwaran motsi tsawon mintuna 2, a hankali Galadima ya bud'e baki tamkar mai rad'a ko gudun wani ya jisu yace, “Munaayaa I love you, I really love you, I love you more and more my Heartbeat..” Lumshe idanu Munaya tayi, wasu hawaye suka gangaro daga cikin idanu zuwa gefen kunnuwanta, zuciyarta sai wani irin bugawa take da sauri-sauri, ta kuma damk'e hannunsa cikin nata tana maijin tsigar jikinta Na tashi, jininta sai yamutsawa yake a kowanne 6angare. Kuma bud'e idon tayi a kansa, suka sakarma juna lallausan murmushi ga hawaye Na zuba a idonta har yanzu, shima kwalla sun tarar masa a cikin ido sun saka idon wani k'yalli Na musamman daya kuma sakama munaya wata kasala da tsantsar k'aunarsa, ya lumshe idanunsa alamar tabbatar da abinda ya fad'a mata har cikin ransane ba iya fatar bakiba. Itama hawayen ta kuma matsowa, ta bud'e baki da k'yar tana cigaba da kwararo hawaye. Tace, “i love you too yalla6ai, I love you so much...”. ‘takai k'arshen maganar wani kukan Na kwace mata. Hannunta dake rik'e cikin nasa ya sumbata yanamai jin farin ciki, yace, “ki kasance dani Munaya, ki kasance dani har k'arshen rayuwata, ke Katanga tace, haskena ce, farinciki nace, duniyata ce, duk duniya kece mace ta farko bayan mahaifiyata da y'ar uwata danakema so Na musamman, please karki barni uwar y'ay'ana, karki gujeni komai rintsi, nima namiki alk'awarin kasantuwar mu tare har k'arshen numfashi, ki rayu dani, ki mutu dani bugun zuciyata, kamar yanda nima burina kenan a gareki tsawon lokaci”. Lallai yau daba'a halin ciwo takeba har rawa sai tayi, Wanda

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});