Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Chapter 57

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya juyo ya kalleni da alamar tuhuma. Uffan bance da shiba, na mik'e da nufin fita na bud'e musu saiya dakatar dani ta hanyar d'agamin hannu. Komawa nayi na zauna, shikuma ya mik'e rik'e da mug d'in ya fita. Ajiyar zuciya nad'an sauke ina binsa da kallo. Saida ya zauna cikin kujera sannan yabama su Muftahu izinin ahigowa. Duk suka zauna suna masa sannu, ya amsa musu cikin d'aga kai da basu hannu sukayi musabaha. Magunguna Dr jalal ya bashi na mura. Sannan ya buk'aci yimasa allura, amma saiya nuna bayaso. Cikin dafe kai yace, “bar Allurarnan Jalal, bara nasha maganin kawai”. Murmushi Dr jalal yayi, Dan yasan dama Galadima bayason allura. Basu wani dad'eba sukai masa sallama suka fita. Fitarsu dana gani yasani fitowa falon, kallonsa nayi ina zama, shima idonsa a kaina, da hannu ya nunamin ledojin da Muftahu ya ajiye. Bance komaiba na bud'e, d'aukar d'aya nayi na fita, na kaima laraba dakema su Abdurraheem shirin barci. Cikin tsokana tacemin “kodai murufe d'akinmu kawai”. Dariya nayi na fita ina fad'in “kai iya yanzufa zan dawo”. Inajiyo dariyarta daga falo. Nidai nashiga kitchen na d'auki plate da spoon na koma wajensa. Farfesun kifi na zuba masa, dan zaifi masa sauk'in ci, da farko ma cayay bazaiciba, saida naita rok'onsa harda kwalla sannan ya amince nabashi da kaina, yad'anci babu laifi, nabashi drugs d'in da Dr jalal yabashi”. Koda yagama sha saiya jingina jikinsa da kujerar yay shiru, yad'anji dad'in jikinsa kam ba laifi, falon saiya d'auki shiru, muna a hakane kiran Momma ya shigo wayarsa. Yabud'e idanu yana d'aukar wayar, yay picking, gaisawa sukayi, bansan mitace da shiba daga can najidai ya amsa da “Insha ALLAH goben muna hanya”. A hankali yake maganar saboda kansa, bama su dad'eba ya yanke wayar ya mik'e, hannu ya mik'omin alamar na kama. Banyi musuba na saka hannuna cikin nashi ya mik'ar dani, bedroom d'in muka koma, ya zaunar dani bakin gadon sannan ya cire kayan jikinsa, ya hau gadon ya kwanta. Nidai k'in kallonsa nayi, saida ya kwanta sannan ya kirayi sunana a hankali can k'asan mak'oshi, kallonsa nayi. Yace, “Please mammatsamin jikina kozai rage ciwon da yakemin”. Tausayi yabani, dan haka banyi musuba na hau gadon sosai nafara masa tausa a nutse, idonsa ya lumshe yanamai jin dad'in tausar, ahankali drugs d'in dayasha yafara cin k'arfinsa, barci mai nauyi yay a won gaba dashi, saida na tabbatar barcin yayi nisa sannan naja bargon na kuma lullu6a masa har saman kafad'a, nai masa addu'a na mik'e Na lalla6a na fita a d'akin bayan na kashe masa fitila. Koda na koma d'aki laraba har tayi barci, nima shirin kwanciyar nayi kawai na kwanta, cikeda kewar y'an uwana da jiya iyanzu duk muna a tare😔. ******************** Iyayen Su Munaya maza sunyi farin ciki da labarin da Abba yabasu akan dangin inna, dan suna tausayinsu sosai, innaro ta tarasu duka tasa aka kira mata inna, harda hawayenta tana Neman gafararta bisa ga abinda tamata tsawon shekaru. “Kiyafemin Ai'sha, dan lallai son zuciya ya rufe idona ruf, banason ara6i y'ay'ana koni saboda abin duniya, nata k'ask'antar dake agaban wad'anda duk kin rigasu zuwa gidan, wlhy wani lokacin su mero ne suke zugani, dan ALLAH kiyi hak'uri, nasan dai da wuya ki yafemin ma.....”. Da Sauri inna tace, “Wlhy na yafe miki nikam, dama ban ta6a rik'eki a raina ba, dan matsayin uwa mahaifiya nake kallonki, inhar bazan iya musawa mahaifiyata magana ba ko jin zafinta to lallai kema baki cancanci na musa mikiba, ni dukanku ma na yafe muku wlhy, ALLAH ya kare gaba, yakuma yafe mana baki d'aya”. Su Abba duk suna amsa da amin, kowanne yanajin dad'i har cikin ransa, lallai idan kaga halin girma to daga tsatson d'an masu girma ya fito, duk cin kashin da innro tama innarsu Munaya hakan baisa ta gagara yafe mataba, ya rabbi kabamu k'yak'yk'yawar zuciya gaba d'aya. Masu samun fawar cin zarafin inna a wajen innaro duk sai suka nutsu suma, dan yanzu kam babu dama. Haka su inna sukaita rabon tsaraba akaita rabo, har gidajen iyayen su Maman safara'u duk saida aka kai, kafin kacemi labarin tushen inna yabaje anguwa, mutane sai mamaki da al'ajabin hikimar ubangiji sukeyi, lallai Maman biyu tazamema matan gidansu RAINA KAMA, su sunata hura hanci y'ay'an wasune, da mata gorin rashin dangi Ashe gaba da gabanta, aifa matan anguwa suka dinga shigowa mata murna da sannu da zuwa. Matan gidansu Munaya bak'inciki tamkar zai karsu, saidai babu damar koda yin tari, saidai kukan zuci da bak'incikin hassada mai cinye farin cikin Bawa. ****************** Washe gari Galadima yatashi dad'an dama-dama, dan babu zazza6in sai ciwon kai, shima bamai tsananiba irin na jiyaba. Da safen yake sanarmin nayi shiri wai zamu koma, mamaki ya kamani, wannan wace irin tafiyace haka babu shiri, bayanma naji yanata kukan rashin kud'i a tsakaninnan, saidai banida damar Musawa, dan inason zuwa naga jikin Abie nima. Da yake tafiyar saida yamma, tashin hantsi muka shiga cikin gida gaida mutane, fada Ce kawai bamujeba, sai yaran aka kai can, kowa yana yaba k'yawu da girman da yaran suka k'ara, gimbiya zulfa dai bata yarda mun gantaba, wai batada lafiya tana kwance. Bamuce komaiba muka fito, mun iske Galadima yana fada, dan haka muka cigaba da shirye-shiye, sai a waya na kikkira mutane mukayi bankwana, naso had'uwa da Aunty Salamah dan inason ta warwaremin wasu tambayoyi, to amma hakan bata samuba, ko gidansu baba mai k'anwa ban lek'aba, kuma wlhy naso hakan matuk'a, to amma ga ayanda tafiyar tazo babu shiri. K'arfe 2:00 mukabar masarautar gagara badau zuwa masarautar su papi, tarba akai mana ta mutunci, ina mamakin yanda suke matuk'ar k'aunar Galadima, Sauban tamkar zaiyi rawa dan dad'i, ammafa yayi 6ul-6ul dashi alamar yanashan gata, dukda lokacinmu k'urarrene munsha fira, inno tsohuwar mutunci, yanda take jana ajiki abin ba'a magana. Galadima ma tunda suka gaisa da papi da mutane saiya shige cikin d'akin inno ya kwanta, dan bayason yawan hayaniya, saida akayi magrib muka baro masarautar cikeda d'unbin alkairin wad'annan bayin ALLAH, alkairi sosai Galadima yay ma laraba, harda hawayenta nima haka, dan munyi sabo sosai, bansan miyasa Galadima baice mutafi har itaba, kokuwa matsalar kud'ice oho, lallai na yarda sabo Turken wawa, shi akema kuka ba mutuwaba. Nuren ya d'auke mu. Mun biya gidan Mom, itama dai haka tasha hidima damu, saidai akwai yarinyarta ta biyu nakula tun a wancan zuwan bata yina, dan ko gaisheni bama yi takeba, tata yatsine-yatsine kenan, a wancan zuwan abin yad'an dameni, amma yau ko a jikina, dan abinda na lura dashi son Galadima takeyi, dan haka na watsar da lamarinta ko kallo bata isheniba, babu mai takani na zauna, babu ruwana da arzik'inka ko ahalinka, ka mutuntani nima na mutuntaka saimu zauna lafiya. Wanda takeyi donshi d'inma ko kallo bata isheshiba, dan baya sakar musu fuska, duk shakkarsa sukeyi har babban wan nasu gaba d'aya, dan ko sauban ya girmeshi balle Galadima. Bamu bar gidanba saida time d'in tashin jirginmu ya matso, dan tacan zamu wuce, dukansu gidan sukai mana rakkiya har airport, har saida sukaga tashin jirginmu. ************** Abin ya had'emin da yawa kam, ga yara ga babansu daba lafiya, sauk'inama basuda yawan rigima, Abdurraheem ne dai idan yaji ya takura babu zaman lafiya, Alhmdllh ALLAH dai ya taimakemu

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});