Chapter 20
Chapter 20
mata, amma son gaskiya nakeson mijina yamin, bana k'yalek'yalen duniyaba, ko tsufa ya kamani bazai bar sonaba, ko nakasa ta kamani bazai bar sonaba, ko babu dukiya tattare dashi bazan gujesa ba, idan ciwo ya kamani koya kamashi zamu tattali juna saoda tausayi da rahamar dake cikin Auren da soyyar gaskiya da mukema juna, ko kishiya yatashimin nasan son gaskiya yakemin bazan ta6a saka kaina a matsananciyar damuwa ba tunda inada yak'ini akan son gaskiya yakemin, bazai ta6a tozartaniba, sannan ban Isa hanashi yaso matarsa ba Dan ni yana sona, nafison amin komai tsakani da ALLAH bada yaudaraba kema kinsani, Dan haka muyitayi inhar bai gajiba nima bazan gazaba”. “Duk mace haka yakamata tasan darajar kanta, takumayi abinda mijinta zai sota son gaskiya Munaya, wannan k'arancin soyayyar ta gaskiya da Muke fuskanta ayanzu shineke yawan ruguje rayuwar aure, mafi yawan mazan sukanso macene domin wata halitta ta jikinta, dasun sami nutsuwa dake kuma shikenan haskenki ya dusashe a idanunsu, wasu kuma Matan mai dukiya ne hangensu ko k'yau, da zarar mijin yazo babu saikiga wuta ta tashi, kokuma bashi dashi dama duk k'aryane, dakinje bakiga abinda kika aureshi danshiba babu sauran zaman lafiya kuma, gaskiya muna cikin matsala yanda taron biki yake a wannan zamanin kawai ya Isa ruguza dukkan albarkar aure, amma ni dazakiji ta tawa tunda shima yana sonki kubar wannan 6oyewar mana”. “Munu, idanfa bai canjaba nima bazan canjaba, bakinsa daya furta shi nakeso ya gyara da kansa”. “lallai to sai kiyita 6oyewar, idan ya nemi kasheku duk zaku fiddoshine kowama yaji, ai nama godema ALLAH da Muftahu dan ta silarsa ALLAH yamuku dabaibayi da yarannan, Ubangiji sarkin hikima kenan, naga Wanda zai iya barma wani ai”. Banza namata nayi kwanciyata, harma barci 6arawo ya saceni. Munubiya ta d'auki wayar munaya tana murmushi, tayi abinda zatayi ta ajiye mata abarta itama ta kwanta. ★★★★ Galadima daketa juye-juye a gado abin duniya dukya ishesa saijan tagwayen tsaki yakeyi ya kalli wayarsa datayi alamar shigowar sak'o, harzai share dai saiya kasa, dan numbers d'in cikin wayar duk masu muhimmancine. Jawo wayar yayi ya danna ta kawo haske, hoton y'an uku ya bayyana a screen d'in, saida yad'an ja wasu Seconds yana kallon yaransa sannan ya bud'e massage d'in, ganin wadda ta turo sak'on sai mamaki ya kamashi, Munayar da inhar bashine ya kirataba bata ta6a d'aukar waya ta kirashiba ita, amma yau itace harda message? Dukda baiyi tunamin samun mai dad'iba haka yabud'e dai, yasan bai wuce maganar data damu mutane da itaba... _Ina fatan ka koma gida cikin aminci da farinciki? Yaranka namaka fatan alkairi da addu'ar samun k'yak'yk'yawar Nutsuwa mai tarin hak'uri._ ya dad'e idonsa akan wayar yana kuma bitar sak'on, baisan murmushi ya su6uce masaba, watoma yaransa ba itaba?, kai jan ajin yarinyarnan yayi yawa, da ace agidan sarauta ta fito lallai bayi da hadimai sunga takansu, ya ajiye wayar yana gyara kwanciya, jiyay zuciyarsa tayi sakayau, dandanan barci ya d'aukesa, dama video call yayi dasu Momma, dan tun bayan daya sauka bai kuma kiransu ba saboda yau ya yini busy, ga tunani sunma kansa yawa, Munaya tagama saitashi yad'an samu nutsuwa amma shine takuma hargitsoshi da abinda zuciyarsa bazata iya d'aukaba. .............. *_Washe gari_* Munaya dai batasan minene ya faruba, dan Munubiya goge sak'on tayi bayan ta tura, da safe kuma ko alamar tayi wani Abu bata nunama Munaya ba. Wajen tashin hantsi saiga Aunty Salamah tazo, cikin farin ciki duk muka mak'alk'ale mata, ta rik'e baki tana fad'in “oh ni, ALLAH yabani y'ay'an da basu San sun girmaba”. Innarmu tace, “wlhy kuwa salama, baki moreba kam”. Laraba dai tanata musu dariya. Kayan gyaran jiki Na musamman Aunty salamah ta kawo musu, takuma bisu da gargad'in wlhy kowa tazage tayi, harda rok'on laraba ta saka musu idanu Dan ALLAH. Gaba d'aya yau a gidan tama yini, hakanne ya d'aukema Munaya damuwar data tashi da ita. ★★★★★★*★★★★★★ Tunda yadawo salla ya koma barci, saboda jiya bai wani samu yin isasheba, wajen 10 ya farka, brush kawai yayi yazo ya zauna yana hada wasu takardu, sosai aikin ya d'auke hankalinsa saboda muhimmancinsa, sauban datun d'azun yay shirin tafiya yagaji da jiran fitowar Galadima Dan haka yazo yaymasa knocking, Dan yanason biyawa wajen Munaya kafin ya wuce. Galadima dake zaune bakin gado ya baje takardu yana kuma rubutu a jikin wasu ya d'aga kai ya kalli Computer d'in dake hasko masa dukkan CCTV camera's d'in sashen nasa, ganin Sauban ne sai ya d'auke idonsa yace ya shigo. Zama sauban yayi saman stool d'in mirror ya gaida Galadima, hankalinsa nakan aikin dayake ya amsa. yace, “Dama katashi?”. “Wlhy Yaya tun d'azun Na tashi, naga baka fito baneba gashi inason kafin Na wuce nabiya Na gaida Aunty gimbiya naga my Triplet's kuma”. Galadima baice komaiba, sai had'e takardun gabansa daya shigayi, Sauban yamatso bakin gadon yana tayashi, saida suka gama tsaf, ya shiryasu cikin wani k'aramar briefcase sannan ya kalli Sauban dake zaune, “Mik'omin System d'incan”. Sauban yad'an marairaice fuska cikin tausayawa. Yace, “haba yaa Sam kad'an huta mana”. Da mamaki Galadima yace, “to idan Na huta kaine zakamin aiki?”. Girgiza kai Sauban yay alamar a'a. Ya tashi ya d'ako masa. Kar6a Galadima yay yana girgiza kansa saboda ganin yanda Sauban keta 6ata fusaka, a zuciyarsa yace bazaka fahimtaba yaro. Batare da sake kallonsa ba yace, “yanzu mikake buk'ata kenan?”. “yaa Sam kud'in wajenafa basuda yawa”. “Humm” Galadima ya fad'a hankalinsa akan aikinsa. yace, “Aikai dama baku iya tausayin kud'iba kai da Samha, mutum yarasa uwar mi kuke saya? Kaje zan turo maka, Dan yanzu kama nima buk'atar kud'in nakeyi, gashi sunyi cak, nasan kuma daga inno har papi idan suna dashi baka zasuyi”. “shikenan yaya, amma Dan ALLAH ko kad'anne”. “ka duba cikin kayan dana cire, maybe ka samu”. “yauwa Yaa Sam d'inmu. ALLAH ya k'ara girma”. Galadima Dai baice komaiba, ya kwaso kud'in duka yana fad'in “na kwashe duka?”. Kai kawai Galadima ya d'aga masa. Sauban yazo ya rungume Galadima ta baya yana godiya, sannan ya sakesa. Murmushi Galadima yayi yana fad'in “ALLAH ya gyaraka Sauban”. “Amin yayana”. Sauban ya fad'a cikin dariya. Sunyi sallama ya tafi akan cewa shima saiya zo, yakuma gaida su papi. ***************** Munaya taji dad'in ganin Sauban, sund'an ta6a hira sannan yamata sallama ya tafi tana shaida masa ya gaida mata su inno da k'yau, har k'ofar gida ta rakoshi, dukda dai bata fitoba iyakarta jikin gate, saida yashiga mota sannan ta koma ciki, tanamai jin k'aunar ahalin Galadima har cikin ranta. ************/********** Galadima na shirin fita kira ya shigo wayarsa, saida yagama d'aura belt d'in da yakeyi sannan ya matsa gaban gadon ya d'auki wayar, a dai-dai lokacin kiran ya kuma shigowa, ganin Sir Isa saiya d'aga. Ko gaisuwa basuyiba yace, “yalla6ai kaga kuwa aika-aikar da ake neman mana?”. “Aika-aika kuma? Tami?”. “Tabbas ansaka wani yamaka kutse cikin Computer, Nazatama kagani?”. Gaban Galadima ne ya fad'i babu shiri ya yanke wayar, system d'insa ya jawo ya zauna bakin gadon, “innalillahi...” Yashiga ambata zufa Na tsatstsafo masa saboda abinda yagani Na shirin faruwa, ya manta daya gama aiki bai saka security a matakin farkoba, saurin sakawa yayi, dukda yasan babu tabbacin zai iya dakatarwa ahakan kawai da yayi, ya ajiye lap-top d'in yana mik'ewa da hanzari, sauri d'aukar rigarsa yayi ya saka, yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83