Chapter 37
Chapter 37
bisa sanadin matata, data dinga zak'ulomin wasu masu alak'a da mahaifinta kuma Na jikinsu tanderu, irinsu Mamman k'afur, Alhaji Halluru, saikuma daga baya ga SD, wato Alhaji shehu Darma, Wanda shine aka saka yake bibiyar Alhaji Auwal Fharuk yana masa barazana, satar yarana da akayi a ranar sunansu ta kawo bayyanar aminina d'an uwana cikin case d'in mahaifina daban ta6a tunanin kasantuwarsa a cikiba, wato Harun d'an gidan waziri, shine wazirin mahaifina shine kuma wazirin Sarki Na yanzu, ina cikin rud'anin Hakan saikuma ga Alhaji Rabilu ya bayyana a gareni shida Badi d'a ga mai dokuna a masarautarmu, Wanda tun ina k'arami Na sanshi, amma daga baya ya 6ata 6at. Bayanan wad'annan bayin ALLAH da bincikena Na had'a suka tabbatar min da zargina akan wad'annan mutanen, nasan abune mai wahalar gaske samunsu cikin sauk'i da fahimtata da duniya zatayi akan zargin danake musu, shiyyasa naza6i yin Garkuwa da yaransu bisa tursasasu tilas sufad'i abinda ke ransu da Wanda suka aikata. Dukkan Wanda ya shigo cikin labarin nan nawa akwaishi a wajennan, mijin yayatane kawai bayada rai sai mahaifan Badi, dakuma wasu daga cikinsu da sukabar duniya, Dan haka ina rok'on wannan kotu data nemo dukkan Wanda Na ambata domin jin ta bakinsa”. Alk'ali ai yama kasa magana, sai kad'a kai kawai yake mamaki da al'ajabi Na cinsa, yayinda kotu tayi tsit kowa yana k'ullawa da kwancewa da tausayin Galadima, irinsu Alhaji Halluru kam ai cikine ya d'uri ruwa, sunsan dai tasu tagama k'arewa kam, Dan yau ranar bankad'a Ce da walle-walle. Alk'ali yad'anyi rubuce-rubucensa sannan ya buk'aci ganin Badi da Alhaji Rabilu, Galadima kuma yaje ya zauna. Alhaji Rabilu da Badi sun bayyana a gaban kotu, hakan ya kuma hargitsa hanjin cikin Waziri, yana mamakin dama Badi bai mutuba? Amma su hak'ilu sukazo sukace ya mutu a wancan lokacin, dan agabansu mai besfa ya kad'eshi, innalillahi ya shiga ambata a zuciyarsa, sai zufa ke jik'eshi, sauk'insa ma akwai malun-malun da rawani a jikinsa, Abba Hayatudden kallonsa kawai yake da tsantsar tsana da mamakinsa. Duk yanda Badi da Alhaji Rabilu sukaima Galadima bayani haka suka maimaita a gaban kotu, wasu harda hawayen tausayinsu suke matsewa, Alk'ali yace, a kawo Alhaji Auwal Fharuk Dan Badi yaga idan shine yabama camera. An kawo Abba, Wanda Alhmdllh jikinsa yayi sauk'i sosai, saidai abinda ba'a rasaba Na k'arfi, kallo d'aya Badi yayma Abba ya ganeshi Dan bai canja masaba sai canjin girma irinnan shekaru, hakama Abba ya gane Badi sarai Dan shima d'in bai canja masanba, aiko suka rungume juna kowa yana hawaye, Abba yana fad'in “Bawan ALLAH Dama baka mutuba a waccan ranar?”. Shima Badi cikin kuka yace, “ban mutuba, sai daga baya ne Na farfad'o a wajen”. Alk'ali ya ankarar dasu cewa a kotu suke, kotu kuma Na buk'ar jin bayani daga bakin Abba, ta Yaya Camera ta dawo hannunsa?. Abba ya dai-daita tsayuwarsa sannan ya gabatar da kansa ga kotu, ya d'ora da fad'in “shekaru 22 kenan da suka shud'e wannan camera take a hannuna ranka ya dad'e, nakuma sametane ta hanyar kad'e wannan bawan ALLAH danayi da abin hawana a wancan lokacin, saboda ya shigo hanya yana matsanancin gudun dabansan mafariba sai yanzu danaji a ya fad'a a gaban kotu. bayan na bigeshi numfashinsa Na Nuna alamar bankwana da gangar jikinsa ya d'auki wannan camera yabani acikin akwati da sunan amana, yakuma ambatamin sunan wad'anda zanba kamar yanda yafad'a, daganan numfashinsa ya tsaya cak da aiki, ina cikin k'ok'arin taimakonsa saiga wasu mutane da gudu da makamai sun dosoni, tsoro naji, Dan inada tabbacin shima sune suka biyoshi, saboda son isar da amanar daya bani inaji ina gani badan nasoba Na tsallakesa Na gudu, Dan nasandai zasu iya kwatar abinda yabani d'in. tunda camera d'in nan ta dawo hannuna ban sake barci mai dad'iba, kullum burina da tunanina tayaya zan Isar da amanarta Na huta, tsawon shekaru ban ta6a fuskantar wani k'alubale akanta ba, Dan ko iyalina babu Wanda yasan da zamanta a hannuna, matata tasha tambayata idan taganni cikin damuwa amma banta6a fad'a mataba, kwatsam cikin laluben Wanda zan bamawa sai Marigayi Alhaji Abdul-hakeem Uba tsohon Governor d'inmu ya fad'omin, Dan ganin yana auren d'iyar tsohon Sarki wadda tana d'aya daga cikin wad'anda akace nabamawa, to lallai anan Alhaji shehu SD yasan Camera Na hannuna, Dan tabbas yaji zancen da mukayi da Alhaji Abdul-hakeem d'in ta hanyar la6ewa, aranar da mukayi zan bama Alhaji Abdul-hakeem camera ya damk'ata ga matarsa sai aka samu akasi wani aiki ya tasomin Na manta ban fito da camera ba, amma mun had'u da shi marigayi Alhaji Abdul-hakeem Na bashi hak'uri da sanar masa uzirina, shikuma SD a tunaninsu nabama Alhaji Abdul-Hakeem wannan camera, shine suka hari rayuwarsa da nufin kar6a kafin ya kaima matarsa, inaga daga baya da suka fahimci babu Camera d'in a hannunsa shine suka juyo kaina. Sunta matsama rayuwata da barazana iri-iri, kiran waya da sauransu, duk number da suka kirani da ita gobe bada ita zasu kirani ba, hakkane ya sakani ware sim card guda kawai dansu, babu Wanda ya sanni dashi, sai matata Dana saka number cikin wayarta batare da itama tasan hakanba, nayi hakanne saboda watarana koda ALLAH yabasu nasarar kasheni d'in. A lokacin da akaima yarana 6atanci da Galadima lallai hankalina ya tashi matuk'a, amma daga baya danayi nazari saina gano maybe su SD ne suka aikata hakan domin 6atamin suna, hukuncin ALLAH kuma saigashi mai martaba Sarki jalaludden da mai martaba Sarki Abdul-fatah sunzo nemawa d'ansu Galadima auren yarinyata da abin yafaru akanta, dukda a 6adda kama sukazomin ni sarai Na ganesu, amma ko y'an uwana ban sanarmawaba, abinda yabani k'arfin gwiwar aurar musu da yarinyata shine Isar da amanar hannuna cikin sauk'i, saikuma aminin mahaifina Baba mai kanwa yace nabasu, Dan shine kawai yasan da zaman Camera a hannuna, shima bani Na sanar masaba, bankuma San a ina yajiba. A randa za'akai y'ata gidan mijinta a ranar Na saka wannan camera da takarda cikin wani kwali Na sakashi a kayanta batare da tasaniba, bansaniba kota gani? Dan cikin gifts d'inta data samu a hannun abokan mijinta ranar dinner d'in auranta Na sakashi, nabama d'an uwantane Abdul-Hameed babban d'ana yabata batare da shima ya san minene a ciki ba. Hikimata anan idan tagani tabama mijinta batare da kace Na ceba. SD bashikad'ai ke bibiyar rayuwata ba, Dan akwai masu sakashi yazomin da farashin kud'i masu tsoka akan camera d'in amma nayi kunnen uwar shegu dasu, hakanne yasakasu k'ok'arin salwantar da rayuwata wai tunda Na hanasu camera, nasan sunajin tsorone saboda Na kusantu da Galadima a lokacin, zan kuma iya bashi camera d'in, saidai abinda basu ma saniba tuni Camera d'in tabar hannuna. Alhaji Halluru abokinane Dan school mate d'inane, ada babu wata alak'a mai k'arfin tsakanina dashi, amma daga baya sai yayta Jana a jikinsa, ban fahimci manufarsaba dagashi har Alhaji Mamman, Dan da zuciya d'aya ni nake zaune dasu. Sai wannan karon da suka tabbatarmin da zulwa jahainin fuskarsu, sannan suka tursasa y'ay'ana biyu Dana d'auka nabama y'ay'ana Alhaji Halluru aure saboda yarda wai su d'akko musu camera a d'akina kosu kashesu dani dakuma iyayensu mata, sun razanasu da cewar sun dasa bomb a gidana, agabana duk suka sanar musu a waya. Abinda yasa ban damuba nasan k'arya suke, sannan Camera d'inma bata gidan, duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83