Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jarida zasu samu labari gobe dasunci kasuwa sosai.....” Hankad'a Muftahu Galadima yayi baya, yay taga-taga zai fad'i, bai kuma kallon ko wanne a cikinsuba ya nuna Harun da d'an yatsa, “Mara kwakwalwa kawai, kafin ni ka kasheni ninan zan kasheka daga kai har munafikin ubanka, dak'ik'i kawai”. yana gama fad'ar haka yabar wajen zuwa cikin gida, taku yake kamar wani bajimi ya fito za6en sarauniyar k'yau. Daga Nuren har Muftahu da kallon mamaki suka bisa, shi kansa Harun maganar Galadima tasakashi girgiza, kardai guy d'innan yana sane da wanene ni tun tuni amma ya k'yaleni? da k'arfi ya fisge shima daga jikin Nuren yana kaima Muftahu duka, “Munafiki dakai zan fara”. Saurin kare kansa Muftahu yayi, Nuren yakuma yunk'urin rik'e Harun, danshifa abin yafara d'aure kansa, kowa yasan Harun aminin Galadima ne Na kusa, yau kuma miya had'osu haka? harda zancen kisa? Galadima yanada matuk'ar zuciya, idan ransa ya 6aci babu ubanda ke gane kansa.... Fad'a dai Neman komawa yay ga Muftahu, saida su Ameer sukazo suka rirrik'e Harun, cak suka d'aukesa yana fisge-fisge da fad'ama Muftahu magana suka shiga dashi ciki. Nuren ya kalli Muftahu dake murmushi yana gyaran kwalar rigarsa. “Amma mike faruwa kuma haka? Yau Sameer ne ke fad'a da Harun?”. Muftahu ya dafa kafad'ar Nuren, “'Dan uwa akwai abinda baka Sani bane, amma Na tabbatar yanzu zama sanshi”. Yana gama fad'ar haka yayi gaba abinsa, shima da kallon Nuren ya bisa, kenan shima yasan dalilin fad'an nasu ashe? jiki a sanyaye ya nufi wajen motar ya kashe sannan ya nufi gidan shima, a yanzu kam lamarin wanan case yafara rud'ar dashi, dan yanda Sameer keta abubuwa a tsakaninnan basuyi kama da nasa zarginba shi. Galadima Na kwance cikin kujera doguwa, tunda ya shigo anan yazufe, duk yanda zuciyarsa taso 6aci sai kalaman Munaya su danne su (mata kunga amfanin hikimar zance ga mazajenmu ko), zantuttukanta suka shiga dawo masa a rai daki-daki, tabbas a yanzu ba fushinsa bane abin buk'ata, jarumtar hak'uri ce, kamar yanda ta fad'a idan kwallo ta 6ata ba daina wasa akeyiba, wata kwallon ake d'auka ayi da ita, cikin lumshe ido ya ciji lips nashi yana wani miskilin murmushi. Daga Muftahu har Nuren dai ido suka zuba masa, ga Harun da aka saka a wani d'aki aka kulle sai bugun k'ofa yake yana fad'ar magana masu zafi akan Galadima. Mik'ewa Galadima yayi yana gyara rigarsa, ya kalli su Muftahu yana cire safar hannunsa, “bara naje gida”. Abinda kawai ya fad'a kenan yay ficewarsa. Tamkar sokaye haka suka bishi da kallo, yana fitowa ya iske sarkin mota a waje yana jiransa (Ashe dama ya biyo bayansu) da hanzari ya bud'e masa motar ya shiga, Galadima ya zauna yana sauke ajiyar zuciya a cikin kujera. Har suka Isa masarauta babu Wanda ya iya tankawa. Sarkin mota nayin parking baima jira an bud'e masaba ya bud'e da kansa ya fice, hadimai masu tsaron sashen Na masa barka da zuwa amma ko kallo basu isheshiba. Kai tsaye sashen Munaya ya nufa, babuko sallama balle Neman iso ya danna kai cikin d'akin. Laraba da samba da yara duk sunyi barci, Munaya kam takasa hakan, sai safa da marwa takeyi tun d'azun, taje d'akin Galadima yafi sau 7 amma bai dawoba, hankalinta a tashe yake da tunanin ina yaje a darennan? shida idon mak'iya kullum a kansa yake, dama kad'an suke nema ta cuta masa?..... Cak tunaninta ya tsaya lokacin da taji anyi sama da ita, zata fasa ihu yace, “yima mutane shiru”. A hankali yayi maganar, Dan haka ta had'iye ihunta cikin sauri da mamakin abinda yayi, yana fitowa falonta ya ajiyeta yaja hannunta zuwa sashensa. Babu abinda zuciyarta takeyi sai dukan 50-50, miye yashiga kansa haka wai?. Basu tsaya a falo ba sai bedroom d'insa, dama tun a hanya ya fara cire jacket d'insa, suna shigowa yana ida cirewar, yay wurgi da ita a tsakar d'akin yakuma d'aukar Munaya suka fad'a saman gado. Tsoronsa yakuma shigarta lokacin dataji ya sakata jikinsa ya matseta, kaikace zai maidata a cikine. Cikin matse baki da sakin k'aramar k'ara tace, “wai minene haka yalla6ai?”. “shiiii!!”. Yafad'a yana d'ora yatsansa d'aya akan bakinta, batada za6in daya wuce tayi shirun, sai zuciyarsa dake wani irin bugu da k'arfi, hannunta ta saka a saitin zuciyar tana karanto addu'a. Duk abinda takeyi yana jinta, hawaye masu zafi suna kwarara masa a ido, saidai tacan gefene shiyyasa Munaya bata saniba, tsawon lokaci muna a haka, har zuciyarsa tafara dai-daita bugawa, takoma normal, sai ajiyar zuciya da k'ok'arin dai-daitar numfashi kawai yakeyi, a haka barci ya kwasheshi, saida nabari barcin yayi nisa sannan nazare jikinna cikin dabara da k'yar nabarshi, Dan Dana motsa saiya k'ara k'ank'ameni, da k'yar dai Na kwaci kaina Na maye masa gurbina da filo, cikeda tausayawa nake kallonsa ina hawaye, a haka Na cire masa takalman k'afarsa, naja bargo Na lullu6a masa, addu'ar barci nayi Na tofa masa, gudun karna ta6ashi ya farka na tofa d'in, Na kashe wutar d'akin nabar da barci kawai na fice ina share sauran kwalla. 'Dakin da Sauban yake kwance na kwankwasa, yataso cikin mayen barci ya bud'e, ganina yasashi watstsakewa babu shiri, “Aunty gimbiya lafiya kuwa?”. “lafiya lau Yaa Sauban, cazan dama kaje d'akin Abban su Amaturrahman ka kwanta tare dashi, naga kamar bayajin dad'i, ba'asan mi dare zaiyiba”. Kansa ya jinjina yace, “to aunty”. Tunda na koma d'aki sai damuwa ta katantaneni, na dad'e ban barciba, daga k'arshema saida na saka karatun Qur'an da k'ara kad'an sannan barci ya saceni batare da na shiryaba. *_Washe gari_* Tunda asuba kasa hak'uri nayi na nufi d'akinsa. Mamaki da kunya suka kamani, Dan ganinsa ragal ya fito wanka, gashi d'aure yake da towel, Sauban yafita saishi kad'ai. Da sauri na juya da nufin komawa amma sai naji an rik'o hannuna, kasa juyawa nayi, yamatso dani ya saka a jikinsa, laimar ruwan da k'amshin sabulun sai suka sakani lumshe ido, ya d'ora hannunsa d'aya bisa cikina ya rik'e hannuna da d'aya, kansa a dokin wuyana yace, “Thanks matar Contract”. Kamar bazanyi magana ba sai dai nayi, Dan karna barta ta kasheni, nace, “Tausayinsu Abie ya sakani, kaji mijin Contract”. Murmushi yayi mai sauti yana shinshinar dokin wuyana, hannu na saka na ture kansa ina fad'in “ka dinga kula fa”. Ya kuma maida hancinsa a wajen, cikin tura hannunsa a rigata yace, “Nida sadakina gwaggo tsiwa”. Ban tanka masaba na fisge jikina, shima saiya barni yana wani bina da ido cikin k'ank'ancesu da miskilin murmushi. Saida naje bakin k'ofa na tsinkayi muryarsa yana fad'in “Kinzo kawai kin karyamin alwala”. Babu shiri na juya Na kallesa, amma saiya basar tamkar bashine yayi maganarba, yama juya ya nufi hanyar bathroom. Kwafa nayi na ida ficewa. Bayan Galadima yakuma d'auro alwala ya fito saiya iske tea a mug da da cake a k'aramin bowl, ya d'anyi luuu da ido tamkar zai lumshe saikuma ya bud'e yana murmushi da shafar kansa. jallabiya ya saka yay salla a d'aki, bayan ya idar yazauna yasha tea d'in, dama jiya baici komaiba ya fita, yunwa yakeji, koda ya kammala saiya fice abinsa. Sashen mai martaba ya nufa hadimai nata zubewa suna kwasar gaisuwa, sukan samu amsa iya kan la66a da d'aga hannu, da haka harya Isa. Saida jakadiya tamasa iso sannan ya shiga, a k'aramin falon mai

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});