Chapter 4
Chapter 4
harararsa tayi, shima ya rama yana ta6e baki da basarwa ya cigaba da cin Arish d'in hankali kwance. Kallonsa ta tsaya yi kawai da mamaki, takai hannu ta daki damtsen hannunsa, shafa wajen yayi yana bud'e baki, saikuma ya kwa6e fuska alamar shagwa6a. Dariya Aunty Mimi tayi tana sake dukansa da fad'in “kadai girma rigimamme”. Yay Murmushi tareda kwantar da kansa gefen kafad'arta, a hankali yace, “kin daina fushin dani to? kinsanfa babbar ya uwa”. Murmushi tayi itama, ta shafa kansa tana fad'in “bazan iya fushi da kaiba ai my k'ani”. Yace, “Nagode Auntyna”. yafad'a yana tashi zaune sosai. Mug d'in tea d'in hannun ta ta mik'a masa, ya girgiza kansa. Tace, “miyasa?”. Iska yad'an furzo daga bakinsa, yace, “K'anwarki tamin d'ura tunda asuba Dan mugunta”. Aunty Mimi tayi dariya, “'Dan rainin wayo, inama laifin daka samu mai maka d'urar, kama tunamin, Yaya maganar tafiyarta gida?”. Saida ya rage fara'a sannan yace, “mungama magana da mai martaba” ya kalli agogonsa da cigaba da fad'in “yanzu zand'anje wani waje, insha ALLAH zuwa 2 to 3 zan dawo, basai yamma bane?”. “To Alhmdllh, naji dad'i da mai martaba yasa baki, dan da wannan taurin kan naka bazaisa ka saurari kowaba”. Mik'ewa yay yana ta6e baki, tareda cewa nayi nan, saina dawo, kudai zama cikin shiri jirgin 7:30pm zamubi”. “ALLAH ya tsare ya bada sa'a”. “Amin” ya amsa yana ficewa. Aunty Mimi tayi murmushi da binsa da kallo, tana tausayin k'aninta da gwagwarmayar rayuwa ta zauna jiransa tunkan yazo duniya, ALLAH dai ya kawo iyakar komai dan shima yasamu kwanciyar hankali. Nace, “amin aunty Mimi mu😘👍🏻”. ******************* Koda Galadima ta fita waya ya kira, Wanda suke wayar ya tabbatar masa k'arfe 11:00 dai-dai Alhaji Shehu Darma zaibar gidansa. Galadima yay murmushi, sannan ya kalli sarkin mota. “Baseer!” Sarkin mota ya amsa da “na'am Ranka ya dad'e”. Kwantar da kansa yay jikin seat d'in yana cewa “Zamu banbanta tafiya dasu, dan haka a plaza zamu kar6i mota hannun Saleem, da ita zamu samu Shehu, itace irin motar dazai shiga”. Cikin mamaki Sarkin mota yace, “Amma ranka ya dad'e ta Yaya? Kasanfa yanada bodyguards kuma masu had'ari”. Murmushi Galadima yay yana d'agowa, yace, “Duk had'arinsu Muhammad Sameer Saifudden yafisu, kaidai yi abinda nace”. Da to kawai sarkin mota ya amsa cikeda girmamawa................✍🏻 😨🙆🏽Galadima ma yazama kidnapper, readers saiku kiyaye⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀🤣. _Masu nemo picture's d'in mutane suna cewa wane da wane canta matse muku, nidai banyi cover d'in RAINA KAMA ba, sannan ban fad'i kamannin mutum ko guda d'aya a buk d'inaba balle mutum yace na siffanta da Wanda kuke yawo dashi, naga wasu suna fad'ar duk maganar datazo bakinsu akan hoton babu taunawa, Ku kama kanku bansan rainin hankalinnan, yafara isata hakanan kuma, bazai yuwu kulum ina asarar data da lokacina ba sannan kuzauna kuna yankama mutane magana batare da kun duba cancantar fitarta ba, please ya Isa haka, ya isa Wanda bazai iyaba babu lali babu tilas, idan kungama wannan kunga batakai mukuba saikuma Ku tsokalo wannan, shin wane irin rayuwane hakan dan girman ALLAH🤦🏻♀, salon cikin Luke d'auka ko k'alk'yalin duniya?, bazaku ta6a magana akan Abu mai muhimmanci da amfaniba sai Mara amfani._ *_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏼 [7/22, 6:22 PM] Aysha Galadima: *_typing📲_* 💡 *_HASKE WRITERS ASSO....._* *_♦RAINA KAMA.....!!♦_* _(Kaga gayya)_ *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* ~BOOK 3~ 👉🏻3⃣ & 4⃣ ................Suna Isa plaza Saleem ya fito, dan yana ganinsu ne ta CCTV, Galadima yay k'asa da glass 6angaren da yake, idonsa akan Saleem dake fitowa, ya k'araso yana rissinawa da gaisheshi, hannu kawai ya d'aga masa, Saleem ya mik'a masa key d'in motar yana fad'in “gashi ranka ya dad'e”. Kansa ya girgiza masa, sannan ya bud'e baki yana fad'in “ai Kaine da kanka zakaja motar, mu zamu bika a bayane”. Da “to” Saleem ya amsa, ya juya ga motar ya shiga. Haka suka tafi su Galadima a gaba Saleem nabin bayansu, suna tafiya Galadima nayin waya har suka isa inda aikai musu kwatance, wajen wata ma'aikatane, motocine birjik a wajen, alamun sunada yawa a ciki, daga d'an nesa suka tsaya, kusan mintuna biyar saiga wani dattijo ya fito tsakanin motocin jikinsa na rawa, harya k'araso wajen motar su Galadima idonsa akansa yake, ta window ya lek'o, amma sai Galadima yay masa nuni daya zagaya ya shigo. Ya zauna a d'arare yana gaishe da Galadima, cikin y'ar sakin fuska Galadima ya gyara zama yana kallonsa, “Baba Rabilu ka kwantar da hankalin, insha ALLAH zaka ku6ta kuma zaka samu y'ancinka, ni namaka wannan alk'awarin, bazaka ta6a taimakona nabari ka wulak'anta ba insha ALLAH, a hankali iyalanka da duk wani dake tare dakai zai fahimci baka mutuba, yanzu mi sukeyi cikin nan d'in?”. Baba Rabilu ya had'iye yawu, muryarsa na rawa yace, “Ranka ya dad'e ban saniba wlhy, amma abinda na fahimta shine lallai sunfara farga dakai, dan naji jiya mai wani a cikinsu yana waya wai kaima lokaci yayi dazasu maka irinna mahaifinka, dan kana neman zamewa rayuwarsu barazana”. Murmushi Galadima yayi, yana cije lips, “karka damu baba Rabilu, wannan ai a hannun Ubangiji yake, yanzu dai ga mota nan ankawo, saika kar6a, zakayi gaba, mukuma zamu bika a baya da y'ar tazara, inason kafinma su d'auki hanya komai zai wakana, su Ameer a shirye suke suma”. “shikenan ranka ya dad'e, ALLAH dai yabamu nasara, kaikuma yabaka kwarin gwiwa da k'arfin zuciyar abinda ka faro, ka ruguza rundunar wad'annan azzaluman da kullum cikin zaluntar bayin ALLAH suke ba a saniba, wasu kuma sunsani tsoronsune ya hanasu magana ko d'aga murya.....”. ya k'are maganar cikin sharar hawaye’. Shiru kawai Galadima yayi yana kallonsa, shima zuciyarsa sai suya da k'una takeyi, saidai yanata ambatar sunan ALLAH kodan neman sassaunci, ajiyar zuciya ya sauke da furzar da huci, yace “shikenan muje ko, dan zamu iya rasa damarmu”. Jin jina kai Baba Rabilu Yayi, ya fita yana rufo k'ofar, hawayen da suka cikama Galadima idone ya sakashi d'aukar glasses d'insa ya saka yana had'iye abinda ya toshe mak'oshinsa, yagaji hakanan, buk'atarsa yanzu kawai k'arshen al'amarinnan yazo kowa ya huta, shima ya gina rayuwarsa data y'ay'ansa cikin salama. Sun isa k'ofar gidan Alhaji Shehu Darma, amma baba Rabilu ya tsayane nesa da gidan, sai motar su Galadima Ce ta k'arasa har gate. Mai gadi yasan Galadima, dukda bawani zuwa gidan yakeba sosai, dan haka babu wani bincik'e-bincike ya barsa ya shiga. Gidane babba na alfarma, Wanda kallo d'aya zaka masa kasan lallai an kashe dukiya ta musamman. Galadima yana zaune a mota bai fitoba, sarkin mota ya fita domin nema masa iso, mintuna dabasu wuce 3 ba saiga P.A d'in Alhaji Darma tare da Sarkin mota, shine ya bud'e ma Galadima mota ya fito yana mai masa barka da zuwa. Yay masa iso har cikin gida falon Alhaji Darma na saukar bak'i masu muhimmanci. Zamansa babu jimawa aka cika masa gaba da kayan ciye-ciye, kai kace jiranshi suke, motsi Galadima bai yiba balle ya nuna alamar zaici, saima latsa wayarsa kawai yakeyi hankalinsa kwance, ga iskar AC na ratsa ga66ansa, kamar daga sama yaji ance “laaah Kaine a gidanmu yau?”. Da farko sharewa yay yak'i koda motsawa, mikuma ya tuna saiya d'ago a nutse ya zuba k'yawawan idonsa a kanta, gabansa yad'an fad'i, wannan ai yarinyar da suka ta6a had'uwane a jirgi, sannan itace suka kuma had'uwa a airport har yayma Munaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83