Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 73

Chapter 73

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bisaga farincikin kasantuwar bayin ALLAH wannan rana da ko yaro k'arami ke d'okantuwa da zuwanta, bare su Galadima da jama'ar masarautar gagara badau da farin cikin ya had'e musu biyu. Bayan idar da salla akaja addu'a mai tsayin gaske ga Abie, sannan aka bashi microphone daga zaune yay bayani mai gamsarwa da ratsa jini da jijiyoyi Wanda yasaka mafi yawan jama'ar dake massalacin hawaye. Hatta da Galadima k'asa kawai yayi dakai yana murmushi da share hawayensa da handkerchief. Yau dai kam ai saida aka kai kusan 11:30 a massalaci kafin a sallami jama'a. Yayinda manya kuma suka samu yin gaisuwa ga Abie da masa murna da addu'a. A can kuwa jama'ar gari kowa ya gumtsi labari yatafi fesarwa, hakama y'an jarida masu zuwa kallon zahiri, kafin kace mi labari ya cigaba da shiga lungu da sak'o, hakama hotunan Abie da nasu Galadima. Bisa ga wannan labarine su Ahmad tahowa Masarauta dukda basuda tabbacin ganin Galadima d'in. K'arfe 12 aka shirya liyafar cin abincin a masautar, wadda har governor zai halarta, itace madadin hawa da akeyi zuwa gaida Governor. Duk yanda Galadima yaso komawa ga iyalansa hakan ta gagara, yawan jama'a ya hanashi matsawa konan da can, kowa soyake ya nuna masa kansa a jerin masu tayasa murnar dawowar mahaifinsa cikin k'oshin lafiya. ********** Alhmdllh munsami kammala komai, Na barma su Umimi sauran aikin suka k'arasa, niko nanufi tsaftace jikina kafin mijina ya shigo, dukkan abincin da za'a fita dashi kuwa nabama su Umimi umarnin kaisa duk sashen daya dace. Galadima daya tuna da batun abincin da Munaya keyi yad'an fita daga cikin mutane yana kiran sarkin Mota, Umarni yabashi akan zuwa birnin gayu ya kar6o drinks wajen manager, yanason kiran Munaya amma babu dama, Dan dawuyama idan ta maida layinta Na 9ja bisa waya, gashi bashida damar tsallakewa ya taho gareta. ********** Sosai Momma take samun tattali ga mama Fulani, ita abinma mamaki yabata, saida aka sakko idi sannan aka kaita sashe Na musamman da akayi aikin gyarawa da safiyar, zasu d'an zauna anan itada Abie kafin asan abinyi gameda sarautarsa dake kan d'an uwansa. A tsorace mama Fulani take, dukda kaffa-kaffa da take dasu Momma, ko kad'an batason mulkinan yabar hannun d'anta, har yanzu burinta jikokinta su gaji masarautar gagara badau. Amma dai taita danne zuciyarta Dan karta nuna hali. ****************** Bayan mai martaba da Abie sun huta aka fara gudanar da liyafar cin abincin a babban d'akin taro Na masarautar. Wanda yasamu halartar manyan mutane dake cikin binin, duk wani mai fad'a aji ya garzayo masarautar Dan kar ayi babushi, kokuma ya shiga black list. Matawalle ya kalli Galadima dayak'i cin komai sai drink yake sha. “Lafiya kuwa Sameer?”. Galadima ya kallesa da alamar tambaya, amma baice komaiba. Da hannu Matawalle ya nuna masa abincin gabansa. Murmushi Galadima yayi yana shafa kumatunsa, cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Bazaka gane bane d'an uwa, my mata tayi abincin salla, idan naci wannan cikina ya cika naje can kuma babu space ai sai a hanani.......”. Sai yay shiru bai k'arasaba. Mi Matawalle da Muftahu zasuyi inba dariyaba, har mutanen dake d'an gefensu suka juyo suna kallonsu. Galadima kam murmushi kawai yayi ya maida eyeglasses d'insa a ido yana kallon inda su Abie ke zaune. Anci ansha kowa yay mak'il cike da godiyar Ubangiji, daganan aka fara gudanar da jawabai Na godiya ga ALLAH bisaga ni'imar dawowar Abie. Mai martaba shine ya fara, sannan Abba hayatudden. Maganarsu ta ratsa zukatan mutane da dama, domin sun nuna k'auna mai yawa da farincikin dawowar d'an uwansu, hakan ya k'ara musu kima, dan sunture zancen nan Na mutane a zuciyarsu, wato y'an ubanci dayafi komai ruruta wutar k'iyayya a masarautunmu Na Hausa Fulani. An buk'aci ganin Galadima shima. Ya mik'e cikeda takun izza da zagayawar jinin Mulki a dukkan sassan jikinsa, k'asaita da kwarjinin yarinta Na d'awainiya dashi. Yanda akaita zubama su mai martaba hototuna shima hakanne. Da yawan mutane dake wajen ya burgesu, koda haushinsa kakeji kwarjininsa ya Isa jin ka k'aunacesa lokaci d'aya. Ya gyara tsayuwarsa yana wani k'asaitaccen murmushi mai tsada da nuna halin dattako, cikakkiyar sallama ya musu suka amsa, sannan yacigaba da magana yana zare eyeglasses d'insa. Hawaye cike da idonsa yace, “A watannin da bazasu cika shekara ba Na tsaya a gabanku kamar haka ina kuka da kausasan kalamai ga dukkan mai hannu a ciwon mahaifina, a ranar d'aurin aurena hakan ta faru, nasan kuma dayawanku dake nan suna a wancan zaman, sai dai bisa ga hukuncin Ubangiji yau nine tsaye a gabanku ina kukan farinciki da tausasa harshena Na Neman afuwa, na godema Ubangiji da yaymin dukkan sutura ta rayuwa, ina fatan samun ta gaba inda yafi gidan duniya, badan nafi kowaba yaymin wad'anan ni'imomin, sai Dan hak'uri da juriya da kar6ar k'addara aduk yanda tazoma bawa, bara nabaku wani labari kad'an, Wanda yana d'aya daga cikin babbar riba dabazan manta da itaba har k'arshen numfashina. Doctor Arjun shine likita na farko daya fara duba Abie, shine kuma yacigaba da kulawa dashi har nakai wayo, shi mabiyin addinin Hindu ne, sanann daga wannan k'abila ya fito, shekarar dazan shiga jami'a sai ALLAH ya jarabcesa da ciwo rana tsaka, yanama cikin aiki a asibiti ya yanke jiki ya fad'i, y'an uwansa doctors sun bashi dukkan taimakon gaggawa harya farfad'o, a daren ranar saiya buk'aci d'aya daga cikin doctors d'in daya kira masa ni. Ina tare da Momma da Jakadiya kiran ya iso gareni, munyi mamaki kwarai da gaske, dan bamu dad'e da duboshiba, lokacin salla dayayine yasakamu baro d'akin dayake ma. Haka Na tashi natafi amsa kiransa. Awajen doctor Arjun Na iya yarensu na Hindu, tunda Na shigo saiya shiga muk'omin hannu alamar nazo garesa, nabi umarninsa Na zama kusa dashi tareda rik'e hannayensa cikin nawa, muryarsa cike da rauni yace___”. _“Sameer Kasan miyasa nace a kiraka kuwa?”._ “Kaina na girgiza masa alamar a'a. yayi murmushi idonsa Na cigaba da tsiyayar da hawaye, yakuma damk'e hannuna a cikin nasa yana cigaba da fad'in___”. _“Sameer kune Muslims na farko dana ta6a mu'amulla mai tsayo dasu, daga gareku na fahimci wasu k'yawawan halaye da kullum duniya kefad'in baku dasu, lallai duk mai ambatar wannan addini da addinin y'an ta'adda ya jahilci fahimta da sanin halayyar d'an adam, kun kasance masu hak'uri wajen samu da rashi, kar6ar rayuwa a dukkan halin data zo muku, kun kasance masu yawan k'yautata zato, mutane da yawa sunsha zuwa duba mahaifinka, amma duk d'unsu ban yarda dasuba amma Ku sainaga babu wani kokwanto a Kansu, da zuciya d'aya kuke k'ar6arsu da mu'amulantarsu, dukda zukatanku sunada yak'inin dolene a samu mugaye a cikinsu, a duk daren duniya idan nashiga duba mahaifinka nakan iske mamanka tana salla ko karatun littafinku, ahankali sai wad'annan abubuwan suka fara kwad'aitamin wani abu daban, tun ina kokawar turewa harya fara zama babban 6angaren tunanina dayay tasiri mai girma a dukkan kuzarina, da farko tsoro nakeji, Dan kaf ahalinmu babu wani mabiyin addinin musulunci ko kiristanci. Amma kasan duk miye matsayar wannan labarin danake baka a yau?”._ “kaina Na girgiza masa jikina a sanyaye, yayd'an murmushi da cigaba da fad'in__”. _“Inason biyan ko nawane domin Shiga addininku, a yau bana tsoron kowa yasani koya ganni a ciki, inason ribantuwa da k'yawawan halayenku”._ “A lokacin kunsan miya faru?”. Jama'a suka amsa da a'a. Galadima yay

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});