Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Raina Kama Book 3 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

matsayin karatunsa da abinda suke karanta, dukda ba magana yakeba murmushinsa Na sakasu farin ciki..... .............★ A can kuwa waje, police nata k'ullawa da kwancewa da jiran isowar IG, Dan yace su jirayi zuwansa. Dukda Galadima yana hira da yaran hankalinsa nakan saurarensu ta abinda ke kunnensa. Babu dad'ewa saiga IG ya iso, kar6ar wayar yayi da kansa bayan sungama salute nashi ya zauna, ya kuma kiran Galadima da kansa. Galadima yay picking amma sai yak'i magana yanzunma, hakanne yasaka IG yin magana cikin takaici da fusata, “Kai bamason rainin hankali, kafad'i abinda kawai kakeso duka amaka kabasu yaransu”. K'ala Galadima bai ceba ya yanke wayar. Mamaki ya kama IG, C.P yace, “Sir dadai anyi hak'uri an musu magana kawai suma aji mizasu ce”. Cikin matuk'ar takaici IG ya dangwarar da wayar yana huci da cire hular kansa, da hannu yayma C.P umarnin a kirasun. Da Sauri Aka danna kiran wayar d'aya daga cikin su, dama duksun tattarune a waje d'aya, Dan haka ya saka Hans free duk sunaji. C.P da kansa ya sanar musu buk'atar Galadima, kallon kallo aka dungayi, kowa ya kasa magana, Shidai C.P ya yanke wayar yana fad'in “nanda mintuna 10 zasu kira”. Suna ganin C.P ya yanke wayar suka hau cecekuce da fad'in yaronan yagama raina musu hankali, kaza-kaza dai, wasu suna bada goyon bayan abadashi sai abi tawata hanyar a kar6i camera d'in saboda suna matuk'ar k'aunar yaransu, wasu kuma sunce kar'a sakeshi, Dan haka tamkar tonon sililine agaresu. Sundai kasa samun matsaya har 10minute's ta cika C.P ya sake kira. Ba'a samu Wanda ya iya d'agawaba harta yanke....... (**************************) Zuwa yanzu gidan su Munaya sunsan halin da'ake ciki game da Galadima dakuma maganar fitowar Abba, Dan y'an jarida nata yad'a komai live a gidajen redio da TV, ga masu d'auka a waya y'an gani da ido dasukazo suka kafa suka kuma tsare. Kuka dai Munaya Na shansa, tayi wujigi-wujigi, miji da Uba duk suna cikin matsala, da k'yar inna ta bata tea tasha da kanta, yaranma sai an mata dole take shayar dasu, ta lafe jikin innarsu tanata hawaye daga ita har Munubiya, yaran sai innaro dasu mama rabi'a da sukazo gidan Tun farar safiya ke kula dasu. A can gefe kuma Zarah da Siyama NATA zagayen d'akin Abba Dan son samun damar shigewa su d'auki camera🤦🏻‍♀. ************************** Alhaji Hallurune yabasu shawarar su d'auka kawai suce su k'arya ake musu Alhaji Auwal baya hannunsu. Wannan shawarar sukabi, da Kansu suka kira C.P suka shaida masa. Sharri Galadima ke musu. Galadima dakejin komai yayi murmushi kawai yana cizar lips. Laptop d'insa ya janyo yafara danne-danne. Daga can C.P ya yanke wayar yana Neman izinin IG domin kiran Galadima shima. IG ya bada izini zuciyarsa Na sakejin zafin Galadima da rainin wayonsa. Saida ta kusa tsinkewa sannan Galadima yay picking, C.P ya sanar dashi amsar da suka bada. Cikin murmushi mai sauti da har su C.P sukeji Galadima yace, “ga za6i biyunan, kodai su fad'i inda yake, kokuma su sakoshi, kokuma shi yasaki video d'in yanda suka saceshi”. Jikin C.P fa kansa yafara sanyi, Dan yafara hango k'amshin gaskiyar Galadima. Bindiga Galadima ya nuna Alhaji Darma da ita, yamasa alamar ya matso gabansa, jikin Alhaji Darma Na rawa ya matso, waya ya mik'a masa, sannan ya danna kiran su C.P yana fad'in a had'ashi dasu yanzunan. Kallon IG C.P yayi, alamar neman izini, IG ya bada damar hakan. Dan danan aka had'a Galadima da su, bindigar hannunsa ya d'ora saman kan Ahmad, maimakon Alhaji Darma, jikin Ahmad yafara rawa, tuni yafara kuka saboda tsoro, tsawa Suka dakama Galadima daga can. Ahmad daketa mazari ya sanya kuka yana fad'in “Dady please and please kubashi abinda yakeso Dan ALLAH, wlhy zai kasheni, wayyo daddy I love you so much”. Tuni Alhaji Bana ya rikice jin muryar d'ansa, Galadima ya cire bindigar daga kan Ahmad ya harbata gefe, k'arar ta tsorata su Ahamad suka rikice da ihu. Rud'ewa su Alhaji Bana sukayi, Dan azatonsu Galadima ya kashe Ahmad ne, su kansa su IG dake waje duk sun tsorata da tunanin ko Galadima ya harbi wanine a cikinsu. Galadima yace, “idan Baku shirya sakinshiba zan kashe Na gaba kuma”. A tare suka hau ihu kowa yana rige-rigen fad'in zasu saki Abba. Galadima ya ta6e baki yana gimtse kiran. Alhaji Bana dai ya suma tuni, saboda tunanin an kashe masa d'a. Saidai suka zuba masa ruwa ya farfad'o, kuka rurus yashiga musu yana kiran sunan Ahmad d'insa, Yakuma rikicewa lokacinda Hajiya Fannah Maman Ahmad ta kirashi. Kasa d'agawa yayi....... **** Galadima yay kiran su IG yana fad'in “inhar suka nakasa Abba ko kawoshi da wani mummunan raune abakin ran d'aya daga cikin y'ay'ansu, Dan haka a matsayinsu Na police su gargad'esu. ********* Antura Police inda suka kwatanta aje a d'akko Abbansu Munaya. A inda aka d'aukeshi suka iskeshi ajiye cikin mota a sume, haka suka d'akkoshi suka taho, kai tsaye asibiti aka wuce dashi domin duba lafiyarsa, dukda babu wani ciwo a jikinsa Na alamar duka sai fashewar baki da kumburin da fuskarta tayi shima bada wani yawa can sosaiba. Galadima sunga komai a TV saboda nunawar da akeyi, hawayen da suka taho masa ya had'iye da k'yar yana sunkuyar dakai danma kar wani cikin yaran kosu Muftahu su fahimci wani Abu, saidai tuni Nuren and Muftahu da Harun sun fahimceshi, Dan sunsa halayyarsa duka, yana da tausayi ainun. Ran Harun A 6ace yake akan bada Abba dasu Alhaji Mansur sukayi, zuciyarsa sai tafarfasa takeyi, gashi kuma a d'aure. Galadima ya mik'e yana bada izinin kowa yaje yay alwala time d'in salla yayi. Idan kuma anyi salla su Farhat su shiga kitchen nema musu abinci. Wannan adalci Na Galadima yanata tasiri a zukatan yaran, harsu gebiral. Duk yanda Galadima yace haka sukayi, har Harun dake d'aure saida aka kwanceshi bisa tsayawar Ameer kansa da bindiga yay alwala. Koda su IG suka nemi yin magana da Galadima saiya jefa musu takardar yana sanar musu time d'in salla yayi, bazai sake saurarensuba sai yayi salla.. Dole sukabi yanda yakeso, suma kuma ya tunatar dasu abinda suka manta. .............................★ Bayan idar da salla da gama girkin su Farhat aka kawo abincin kowa ya d'ebi iya buk'atarsa, yanzuma Galadima bai Ciba, kwanciyarsama yayi cikin kujera ya lumshe ido. Harun dai anji wahala anci yanzu🤣😜. .............................★ Tuni mazan gidan su Munaya suka d'unguma zuwa asibitin Dan duba halin da Abba yake ciki, matan dai da yaran an barsu a gida, sai innaro kawai data Dage sai taje aka tafi da ita. .............................★ Buk'ata ta biyu da Galadima ya kawo bayan idar da salla itace a tura jami'an tsaro suje subama iyalan Abba tsaro a gidansa, hakama a asibiti. Babu musu IG yasaka C.P, shikuma CP yabama D.P.O Umarni, dandanan aka sanar da station d'in yankin su Munaya, aka kuma k'ara dawasu police d'in harda mata da zasu shiga cikin gida. Munaya taji dad'in hakan da Galadima yayi, Dan a tsorace tale dama. Dole kuma Zarah da Siyama suka nutsu, Dan Munaya k'ofar Abba taja zugar y'an uwanta suka shimfid'a tabarma sukayi zaman jugum-jugum d'in a can.🤨👍🏻. ************************ A masarautar gagara badau kam babu abinda kakeji Na tashi sai k'ananun magana. Bayi da kuyangi, dogarai da y'an gidan, manya da yara, kowane hadimi burinsa yafara kaima

Table of Contents

Chapters

83 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});